Connect with us

CIWON 'YA MACE

Muhimmancin Koya Wa ‘Yarki Rayuwar aure

Published

on

Masu karatu barkanmu da sake haduwa a filinmu na ciwon ‘ya mace, wanda masu hikimar magana ke amsawa da cewa ‘na ‘ya mace ne’.

A wannan makon za mnu tattauna ne a kan wani abu mai muhimmancin gaske da uwargida za ta mayar da hankali a kai da zarar ‘ya’yanta mata sun taso, suna fuskantar yin aure. Yana daga cikin abin da ya dace iyaye su rinka gayawa yara mata da zaran sun fara tasowa wato rayuwar aure.

Yara da yawa a yanzu kan fassara rayuwar aure a matsayin rayuwar jin dadi ko yadda suke tsara abin cikin zukatansu,bayan abin ba haka ba ne. Idan tun farko uwa zata sanarwa yarinyar ta cewar rayuwar aure ibada ce,idan jin dadi yado a godewa Allah akasin hakan ma a gode masa da an rage kaso mafi yawa na cikin matsalolin aure. A duk lokacin da uwa ta dora yarinya a rayuwar jin dadi kawai cikin gidan aure sabanin dorata akan ibada ce,to daga nan an samu babbar matsala. Wasu da yawa tunanin su dabam ne akan rayuwar aure kafin aure, a lokacin da aka yi aure idan aka ga sabanin haka sai matsala ce zata biyo baya. Bayan koyar da girke girke, ladabi da biyyaya, tsaya, kula da maigida, yana da kyau a koyar da yarinya hakuri da yanayin da zata tsinci kanta bayan tayi aure. Idan tasan Wadannan tun kafin ta shiga gidan miji tabbas zata san yadda zata tafiyar da rayuwar ta bayan tayi auren. Wasu iyaye kan yi kuskure ko sakaci wurin dora yaransu mata akan sanin rayuwar aure gabadaya har sai anyi auren ayi ta samun matsala. Kuma koda bayan aure iyaye bazasu gajiya ba wurin jaddada musu meye auren dama rayuwar da ke cikin gidan aure. Abu ne da za a yi ta yinsa har lokacin da aka ga yarinya ta fahimta, wannan zai taimaka matuka wurin rage yawan matsalolin gidan aure, dama yawan mace macen aure dake faruwa a yanzu. Saboda mafi aksarin matsalolin nada nasaba da haka. Ba daidai bane yadda iyaye zasu kyale yarinya da rayuwar gaban talabijin kuma suyi tsammanin ba za a samu matsala ba bayan an aurad da Ita. Allah ya sa mu gyara ya bamu Ikon aikatawa,amin.

 

 

Zainab Ahmed Shamsuna: Fitacciyar ‘Yar Arewa Da Ta Shahara A Fannin Sha’anin Kudi

Ko-kun-san? Zainab Ahmed Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasar Nijeriya tana da cikakken kwarewa a fannin mu’amala da kudi na tsawon shekaru 28, a bisa duba dacewarta ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada ta minista har sau biyu, domin kuwa a zangon Buhari na farko ta kasance Ministar Kudi a shekarar 2018, kana ya sake mata sabon nadi a matsayin Minista a zangonsa na biyu. Zainab tana daga cikin mata bakwai da lifafarsu ya cilla na shiga jerin Ministocin Buhari a rukunin neslabul. Wace Ce Zainab Ahmed? An haifi Zainab Ahmed ne a jihar Kaduna a ranar 16 ga watan Yuli na shekarar 1960. Bayan da ta kammala Firamare ta halarci kwalejin Kueen Amina College da ke Kaduna a shekarar 1977 domin samun shaidar kammala sakandari, ta kuma yi IJMB a shekarar 1979 a SBS/ ABU Zariya ta samu digirinta na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1981 wacce ta karanci Akanta, sannan ta samu shaidar digirinta na biyu a jami’ar jihar Ogun, Ago Iwoye a watan Agustan 2004 wacce ta karanciGudanar da Harkar Kasuwanci. Biyo bayan murabus din tsohowar Ministan kudi, Kemi Adeosun a ranar 14 ga watan Satumbar 2018, Buhari ya nada Zainab ta zama Ministan kudi a watan Satumban 2018. Tana da kwarewa sosai a fannin gudanar da harkokin kudi da tafiyar da kasuwancin jama’a sosai. Gabanin ta zama gogaggiya sai da ta yi aiyuka a wurare daban-daban. A shekarar 1982 bayan da ta kammala karatu, ta samu aiki a matsayin Akanta mai mataki II a ma’aikatar kudi ta jihar Kaduna, daga bisani aka kara mata girma a watan Maris na shekarar 1984 ta zama Akanta I, sai dai kuma ta yi murabus daga wannan aikin a shekarar 1985 gami da fara aiki da Kamfanin NITEL. Tun gabanin nan ma dai, ta yi bautar kasa (NYSC) a jihar Kaduna a tsakanin 1981- 1982 wacce aka cillata aikin hidima wa kasa a Messrs. Egunjobi Suleiman & Co. Chartered Accountants, wacce ta yi aiki a matsyain mai ba da horo. Ta dawo ta ci gaba da gwagwarmayar aiki a wurare daban-daban wacce ta taka matakai mabanbanta, daga cikin kujerun da ta rike sun hada da Manajan gudanarwa na kamfanin zuba jari ta jihar Kaduna, sannan ta rike babban jami’ar kudi a ma’aikatar Nigeria mobile telecommunications company, Sannan kuma tarihin rayuwarta ya nuna cewar ta yi aiki da NEITI da Global EITI. Zainab Ahmed ta kasance tsohowar mamba ce a kwamitin gwamnoni kan asusun lamuni ta duniya (IMF) a shekarar 2018, sannan ita tsohowar mamba ce a kwamitin gwamnoni kan bunkasa banki musulunci (IDB) a shekarar 2018. Shigarta Majalisar Zastarwar Nijeriya A Zangon Neslabul: Dangane da yunkurinta na kyautata tattalin arzikin Nijeriya, Minsitan kudin ta shaida cewar ma’aikatar nata zai tsara ababen da suka dace dukkanin rassan da ke bayar da tallafi na kasa da kasa sun bi tsari da matakan da kasar nan ke bukata domin tabbatar da bunkasa tattalin arziki. Ta ce, nan gaba kadan za ta kira ganawa da dukkanin rassan kasashen waje masu bayar da tallafi domin zayyana musu ababen da Nijeriya ke bukata. Ta ce daga yanzu dukkanin masu bayar da tallafi dole ne su bi tsarin da Nijeriya ta fitar. Ta sha alwashin cewar za ta tabbatar da ta share wa shugaban kasa Muhammad Buhari hawaye ta fuskacin yin aiki tukuru domin ci gaban Nijeriya, nan da nan ta gana da manyan jami’an ma’aikatar nata domin zayyana musu irin shirin da ta zo da su. Sannan ta ma umurci kwamitin duba kasafin kudi da cewar su fara shiryeshirye da tsare-tsaren kasafin 2020 har ma ta ce kasafin zai zama a kimtse daga nan zuwa watan Satumba. Sannan ta kuma bayyana aniyarta na tabbatar da kara samar wa Nijeriya kudaden haraji domin tabbatar da kudaden shiga sun karu. Ta ce akwai bukatar kasafin kudi ya karu daga kashi 55 cikin dari a shekarar 2018 zuwa kashi 85 cikin dari. Ta kuma kara da cewa samar da asusun shigar da kudi na bai-daya ya taimaka sosai wajen toshe aniyar masu cin hanci da rashawa da babakere kan dukiyar kasa. Ta ce, akwai tsare-tsaren masu kyau da ta zo da su da take son tabbatar da ta bisu domin kasar nan ta samu habakuwa ta fuskacin tattalin arziki, kudi, haraji da kuma tabbatar da tsara kasafin kudi mai nagarta.

Zaman Aure: Kiyaye Hakkin Juna Shi Ne Gishirin Zama Da Mace Fiye Da Daya

Masu karatu barkanmu da sake saduwa a wannan makon a filin naku mai farin jini na Hantsi Leka Gidan Kowa. Kamar yadda muka saba a ko wane mako, a yau ma mun yo muku gagarumar tsaraba game da abin da ya shafi gyaran zamantakewar aure. A wannan zamanin, duk da cewa akwai wasu mata da suka fara fahimtar alfanun kyale miji ya kara aure, har yanzu akwai sauran rina a kaba, saboda wasu sun kasa gane hakan, wani lokaci kuma masu irin wannan tunani ba su da laifi su kadai, abin yakan hada har da laifin miji mai kara aure, saboda gazawarsa wurin yin abin da ya dace a tsakanin uwargida da amarya. Wasu na ganin auren mace fiye da daya a matsayin shi ne silar rashin samun zaman lafiya, amma abun ba haka yake ba. Wasu sukan ji dadin zama da matarsu ta farko. Ana jin dadin zaman auren mata da yawa ne a lokacin da miji da mata suka kiyaye hakkin juna. Yana yawan samun rigingimu da matsalolin mabambanta da suke tattare da auren mace fiye da daya ko kuma zaman kishiya da kishiya. Ina kyautata zaton daya daga cikin ma’auratan ko kuma dukkan su ba su bin koyarwar alkur’ani da sunna. Musamman mijin. Musulunci ya koyar da yadda za a yi auren mace fiye da daya wanda ya nuna mana koyi da manzon Allah yadda ya yi da matarsa. Wannan shi ne babban gunshiki ko turba da kowani musulmi ya kamata ya bi wajen koyi da yadda aure yake domin samun nasara. Auren mace fiye da daya ana ganinsa ne a matsayin cewa, yana amfanar da miji ne fiye da matan, amma a gaskiyan zance yana da matukar wahala ga miji. Musamman wajen daukar dawainiyarsu ta fuskar tufatarwa da ciyarwa da sauran bukatu da kula da yaran. Ga wasu kadan daga cikin abubuwan da ya sa mata ba su san zama da kishiya. -Raba soyayya: Babban matsalar da mata suke fuskanta wajen zama da kishiya shi ne, wajen nuna soyayya wanda wannan shi yake kawo rashin jituwa. Soyayya kuwa wani abu ne da ake nunawa a tsakanin jama’a. Ita mace a duk lokacin da mijinta ya karo aure, sai ta dauka ya daina sonta ne wanda wannan ba dai-dai ba ne. A dauki misali da lokacin da uwa ta haifi wani yaro bayan tana da wani za ta nuna soyayyarta ga dukkanin yaran da take da su, tamkar haka abun yake ga namiji, a lokacin da ya karo aure. Maza nagari suna kara aure ne ba wai don ba sa son matayensu na farko ba, domin kuwa idan ba sa son su za su sake su ne su sake wani auren. -Raba lokaci: Abun da za a raba a zaman kishi shi ne loakcin mijinki. Ko da yana daukan lokaci kadan ne da mijinki, abu ne mai kyau ko mara kyau ya danganta da yanayinki da yadda kike kyautata masa ne. -Zama da kishiya: Ka da ki yarda ki dauki kishiyarki a matsayin abokiyar adawar ki. Ki yi kokarin tabbatar da cewa kina da kyakkywar alaka da mijinki. Shawara mai amfani daga bakin dan’uwa cewa, rashin tabbas da macen farko shi ne ta tabbatar da cewa mace ta biyu za ta maye gurbinta, a saboda haka ki yi kokarin tabbatar da cewa kin kyautata alaka da mijinki. Yadda Mata Za Su Magance Kishi Babban hanyar da za a magance kishi shi ne, ta duba abun da ka dosa. Kishi ne ka sami wani a wurin da kake ganin kai kadai ya kamata a ce ka mallake shi. Idan a alakar ku akwai kishi, ki mayar da hankali wajen kulla alaka mai kyau da mijinki. Ki tabbatar kin jawo hankalinsa a kanki a maimakon ki rika husuma da mijinki. Ki tuna fa Nana Aisha ta yi kishi a kan Manzon Allah wanda har ta taba fasa tangaran saboda da kishi. Idan kun sami sabani da kishiya, a zauna a tattuana ka da a yi aika-aika domin kaucewa bacin rai. Aure na baci ne a lokacin wani ya saba wa wani aka kasa yin hakuri da juna, wanda daga karshe saki ya shiga tsakani duk da yake sakin halal ne. A duk lokacin da aka yi auren mace fiye da daya kamar yadda musulunci ya koyar, ba za a taba samun wata matsala ba.

 

Rigakafin Cututtuka A Saukake

Wani sirri daga Manzon Allah shi ne, tsare yara don kada aljanu su kama su idan yamma ta yi, domin aljanu da zarar magariba ta yi suke bazamo wa, saboda akwai mashaya jini da yawa a cikinsu. To duk abinda yake mai shan jini ne baya iya fitowa in akawai rana, sai rana ta tafi ta fadi sannan ya bazamo neman abincinsa, kamar yadda kaima daga rana ta fito kake bazama neman naka abincin. Da zarar rana ta taho faduwa za ka ji jikinka ya yi lakwas kana tunanin ka koma gida ko ka yi bacci, saboda haka Manzo SAW ya koya mana da magariba ta yi mu kame yaranmu, mu shigar da su cikin gida, haka ya koya mana, saboda haka sai a bari in an kira sallar magriba wannan ba laifi kwa iya fita don yin Sallah tare da su wadannan yaran. Kuma idan lallai akwai bukatar za a je kamar asibiti ne tare da su a iya, amma lallai a bari a jinkirta sai an yi kiran Sallah. Ka ga wannan likitanci da babu wanda ya isa duk duniya ya koya maka shi, ko a Turawa ko a Larabawa in Ma’aikin Allah ba, a ko wacce kabila yake. Da dama wasu suna haduwa da matsalar aljanu, wanda mu muna ganin su kuma muna maganinsu, sau da yawa za a zo mana masu irin wannan cutar ta aljanun, ka ga yaro an kawo shi ace yaron ba shi da kokari a Makaranta, baya cin jarrabawa ya baci da shaye-shaye, yana sace-sace, don Allah Mallam a taimaka. To in muka zo muna yin aikin Allah ya kan bayyanar mana, wani lokcin ta bakin su kansu aljanun a jikin yaron, sai ka ji suna cewa lallai dai-dai magriba ne suka gan shi ya fito kofar gida, ko kuma wani abu makamancin haka. Yana daga cikin ribar mu da za mu nuna wa duniya muna da wayo shi ne, mu dauki koyarwar Manzon Allah SAW. Sannan Manzon Allah ya nuna mana lallai mu rika rufe tukwanenmu, kofunanmu, kwanika, abin tara ruwa kamar duro, da duk wani abu da muka san muna amfani da shi idan dare yayi. Wani Hadisi yana nuna cewa Annoba da kuke gani, sakamakon wasu aljanu ne da ake samu suna shigowa cikin duniya, ya danganta da yadda yadda tsautsayin ya fada a kan mutum ko wani gari, sai su watso wani abu, to shi ne wannan abin sai ya biyo iska ya bazo cikinku. In ya fado din zai shiga cikin tukwanen da suke bude ne. To idan ya fada cikin kwano ko bokiti ko tukunya, sai wannan cuta ta zauna, ku kuma kun tashi da safe sai ku girgije abin ku fara amfani da shi, ita kuma matsalar Annobar ta fi karfi a girgije, wani ba girgijewa zai yi ba kawai sai ya dauka ya tara a famfo ko ya jawo a rijiya ya yi wanka, da yayi wankan nan shike nan ya zuba Annoba a jikinsa. Sai ka ji ana cewa Annoba ta bulla a gari kaza ana ta kurajen biri, kurajen mage, duk wadannan za ka samu abubuwa ne da suke da alaka da wannan Annoba kamar yadda Manzon Allah SAW ya bayyana. Sannan Manzon Allah SAW ya hana mu shiga garin da ake Annoba, don gudun in ka shiga ka dauka, kuma kana ciki ake yi to kada ka fita, saboda gudun kada ka kaita wani garin. Sannan Manzon Allah ya yi umurni da mutum ya zauna rabin jikinsa a rana rabi a inuwa, ko dai ka shiga ranar gaba daya, ko kuma ka zauna a inuwar gaba daya, saboda in ka zauna a wancan yanayin, to cuta za ta iya kama ka, irin wadda za a rasa kanta. Har ila yau Manzon rahma ya sake koyar da wani rigakafin shi ne, kada mu zauna ba aure, lallai idan mutum yana hali ya yi aure, domin ya fada wa sahabbansa cewa wanda duk ya samu a cikinku ya yi aure. Hadisi ne ingantacce da yake cikin Bukhari da Muslim, domin auren nan zai samar masa kariya, wanda bai samu damar yin auren ba aka ce ya yi azumi don ya rage masa karfin sha’awa, saboda maniyyi yana da matsala idan yana tarar wa mutum, gashi kuma an haramta maka yin zina, kuma kuma kai ma ka san illolin da yake cikinta, kuma kai istimna’i nan ma ka jawo wa kanka, wato shi ne mutum ya yi ta wasa da gabansa har ya biya bukatarsa. Wannan yana kankantar da gaba, kuma yana sa raunin zuciya, mai yin wasa da gabansa ba ya samun karfin zuciya. Saboda haka mafita kawai ita ce aure, duk wanda zai zo ya rika yi maka wata huduba cewa ai kai matashi ne ka bari sai ka yi Digiri ko wani abu, wannan mai baka shawarar mahaukaci ne yana so ne ya raba ka da koyarwar Manzon Allah, kuma wannan din da ya hana ka aure shi zai zo ya ce ku je ku yi zina, a she makaryaci ne ya kai ka ya baro. Ka je ka bincika ka ga shugabannin duniyan da kake ji Yahudawan da Nasara a shekara nawa suke aure? In ban manta ba George Bush na farko yana da shekaru ishirin ya yi aure. Amma kuma suna ta yada jita-jitar kada a yi aure da wuri, za ka samu irin su Obama ga su nan da ‘ya’ya manya-manya saboda sun yi aure da wuri. Don haka yin aure da wuri lafiya ce ga jikin mutum, yana sanya jikin mutum ya samu cikakkiyar lafiya, kuma rigakafi ne ga talauci. Da yawa wadanda suka yi kudi idan ka duba za ka ga sai da suka yi aure suka samu dukiya ko rufin asiri. Sannan kuma wani rigakafin ga mata su ma Manzon Allah ya ce su rika rufe jikinsa, don gudun kada a yi musu fyade, rigakafi ne ga jikinsu da yake hana aljanu shiga jikinsu. Idan muka duba za mu ga kasar da tafi karancin yi wa mata fyade a duk duniya Saudiya ce, sai irin makwaftansu Oman da sauransu, sirrin shi ne matansu gaba daya a rufe suke. Ba a ce ba sa yin wani abu mara kyau ba, amma a boye ake yi. Saboda mutum ya ci abinci ya koshi, dole sha’awa ta zo masa, amma kuma abin da zai motsa sha’wara an boye shi, saboda kafin ya gani sai ya sha wahala. To amma mace ta bude jikinta ta bayyanar da wasi abubuwa nata, da mutum ya gani sai abin ya motsa masa sha’awa, in tsautsayin bai fada kanta ba zai iya fada wa kan wata.

Da ya samu dama a kanta koda yarinya ce karama sai ya afka mata, ga laifuffuka nan na fyade ana ta samu, ga shi nan ana ta fada a labarai, dan shekara kaza ya yi wa yarinya karama fyade. Msali a ce dan shekara saba’in ya yi wa ‘yar shekara shida fyade, kaga ai ba ita ya kalla ba, amma wadda ta yi shigar ita ya kalla sha’awarsa ta motsa. Amma saboda ba zai iya samunta ba ko don rashin kudi ga tsufa, kuma ga matan nan manya-manya sun ki su yi aure, wasu suna son yin auren amma iyaye sun ki yi musu an ce sai sun yi karatu. Kuma suna cudanya da maza baligai a makarantu, suna bayyana jikinsu iyakar bayyana wa da shiga ta badala da iskanci. Ga lamarin yana faruwa an rasa maganinsa, kullum ka ji an ce an kai mutum kaza kotu an yanke masu hukuncin shekara kaza, a gidan yari. To in za a yanke wa mutum shekara dubu in ya fito sai ya sake in dai mata ba su daina shigar banza ba. Sannan Manzon Allah SWA ya hana mu cin abinci da hannun hagu domin rigakafin kamuwa da cuta, domin hannun hagu shi ake sawa a kazanta, don haka duk abin da mutum zai ci ya tabbata ya ci da hannun dama. Sannan ya koya mana nisantar kamuwa da annobar ciwo, cewa idan mutum yana da dama ya lashi zuma sau uku a jere da sassafe kafin mutum ya ci komai, idan aka ce sabon wata ya kama tun daga farkon watan Musulunci kafin ya kai 15 ake son ka yi, kwana uku a jere, sannan ka lasa wa yaranka suma sau uku kwana uku a jere. In Allah ya so ka yi musu haka, to annobar da za ta zo a wannan shekara Allah za tsare su. Sannan yana daga cikin koyarwar da Malamai suka yi mana na rigakafi, mutum ya rubuta Fatiha kafa bakwai da kursiyyu bakwai da lakad ja’akum kafa bakwai, Falaki bakwai Nasi bakwai, a rubuta da tawada mai kyau a allo mai kyau a wanke da ruwa mai kyau. Ruwan da za a wanke in an samu Zamzam an fi son haka, in ba’a samu ba an fi son ruwan Sama, in ba’a samu ba a sa ruwan rijiya. In babu kuma to sai a nemi kowa ne ruwa, sai a wanke a sha shi ma ya wadatar, domin shi Allah niyya yake kallo. Sannan ana rubuta Ayatusshifa’a din nan guda shida da suke cikin Alkur’ani su ma a rubuta duk wata a sha a gida, wannan ma ana fatan samun kariya daga annoba, wannan fa ba wai an ce idan cuta ta kama ka za ka warke ba ne, a’a rigakafi za ka yi yadda cutar ma ba za ta kama ka ba. Sannan Manzon Allah SAW ya hana mutum ya yi kaki ya tofar a Masallaci, Malamai likitocin Musulunci suka ce ai saboda Masallaci wurin taruwar jama’a ne, idan ka yi tana iya yiwuwa kana da wata cuta da ta kama ka a huhunka idan ka tofar, iska za ta iya dauka ta sanya wa mutane. Sannan Manzon Allah ya ce, ku ji tsoron la’ana guda biyu, kamar yadda ya zo a ruwayar Muslim, ya ce la’ana ta farko ita ce, mutum ya yi ba-haya a kan hanyar da mutane suke wucewa, ko a inuwar bishiya. Hikimar hanawar ita ce, iska za ta iya daukar cutar da ke cikin wannan najasa taka ta kai wa mutane. Bincike ya nuna cutar kwalara bayan garin da ake yi ne iska take daukar sa ta kawo cikin mutane sai a shaka, ko ta zuba acikin ruwa sai a yi abinci da shi ko a sha, sai a yi ta amai ana gudawa. Kamar a kauyuka yadda za ka ga ana haduwa ana wanka a wuri daya, kuma ruwan nan wani fa ba ya gudu, a ciki za a yi fitsari ko a wanke bayan gari. Manzon Allah SAW ya hana mu fitsari a cikin ruwa, sai kare lafiyarmu, to suna da yawa a yanzu dai mun fadi kusan guda ishirin da biyu a iya dan bayanin nan da muka yi. Allah ta’alah ya yi wa abin da muka ji albarka, kuma insha Allah a shirin da za mu yi nan gaba za mu shiga wani bayanin ne sai a yi hakuri da dan wannan da muka ji.

Assalamu alaikum warahmatullahi Ta’alah wabarkatuhu.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: