Connect with us

SIYASA

Shugaban Majalisar Bauchi Ya Nemi Abokan Aikinsa Su Jingine Banbancin Jam’iyya A Gefe.

Published

on

 

An bukaci mambobin majalisar dokokin jihar Bauchi, da su jingine banbance-banbanen jam’iyya da ta siyasa su hada karfi da karfe wuri guda domin sauke nauyin da ke kawukansu na tabbatar da ci gaban jihar Bauchi.

Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Abubabar Y. Sulaiman shine yayi wannan kiran, yana mai shaida cewar akwai gayar bukatar ‘yan majalisun su tabbatar da yin dukkanin mai iyuwa domin sauke nauyin da al’umman mazabunsu suka daura musu wanda hakan ne ma ya sanya suka zabesu tun a farko.

A wata kwafin sanarwar manema labaru da mai magana da yawun Kakakin majalisar, Kwamared Abdul Bura ya fitar, kakakin ya yi bukatar ne a lokacin da yake bude wani taron kara wa juna sani da aka shirya wa ‘yan majalisun na kwanaki biyu wanda gwamnatin jihar Bauchi da hadin guiwar National Institute for Legislative and Democracy Studies (NILDS) suka shirya a Kano.

Abubakar ya kaddamar da bude taron da cewar hakan zai taimaka sosai wa ‘yan majalisun dangane da gudanar da harkokin majalisar jihar yadda ya kamata. A cewar shi, “Ya dace mu san cewar al’ummar mazabunmu sun bamu dama ne don mu yi musu wakilci na gani a majalisar jihar, wannan ba karamin dama ba ce a garemu, ya dace ne mu sanya bukatar jama’an mazabunmu fiye da kowani abu,” A fadin Kakakin.

Abubakar Sulaiman ya nemi ‘yan majalisun da su tabbatar da gudanar da aikin da ke gabansu cikin hankali da mutunta juna domin samun nasarar bunkasa ci gaban jihar ta kowace fanni. Ya kuma taya ‘yan majalisun murnar shawo kan barakar da ya barke a cikin majalisar a kwanakin baya, yana mai tabbatar musu da cewar a shirye yake ya hada kai da dukkaninsu domin gudanar da wakilci na kwarai.

Taron kara wa juna sanin wanda aka masa take da: ‘Good Gobernance Through Effectibe Legislative Engagement’ an kai ga kammala shine a ranar Alhamis 29 ga watan Agustan wanda rukunin farko na ‘yan majalisar su 17 suka halarta. Kamar yadda sanarwar ta shaida ‘yan majalisun za su kuma koma majalisar domin ci gaba da gudanar da aiyukan da ke gabansu a mako mai zuwa, yana mai shaida cewar zasu dawo majalisar ne domin fara tantance kwamishinonin da gwamnan jihar Bala Muhammad ya aike wa majalisar kamar yadda ake tsammani.

Idan za ku iya tunawa majalisar jihar dai ta barke da rikicin shugabanci ne tun bayan kaddamar da majalisar a watan Yuni, inda aka samu shugabanin biyu kowa ke ikirarin shine Kakakin majalisar jihar. To sai dai kuma daga baya sauran ‘yan majalisun da suke karkashin Kawuwa Shehu Damina sun amince da jewa kwaryar majalisar domin a tantance su lamarin da ake ganin takmar matsalar ta kawo karshe ne.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!