Connect with us

MAKALAR YAU

Waiwaye Kan Sana’ar Masu Keke Napep (A Daidaita Sahu) A Nijeriya

Published

on

Babu shakka za a ga cewa, Babur maikafa-uku da a yanzu haka cikin wannan Kasa ya sami cikakkiyar karbuwa kusan a duka bangaren Kudunci da Arewacin wannan Kasa, a matsayin guda cikin manya-manyan hanyoyin sifurinmu na yau da kullum, an kira shi da sunaye iri-iri tun daga lokacin bayyanar tasa a Kasar.

Bayyanar Babur Mai-kafa-uku, (Keke Napep / A Daidaita Sahu) A Nijeriya A zamanin mulkin Soja, na marigayi Sani Abacha, wajen karshen Shekarar 1990, gwamnan Lagos, Col. Buba Marwa, ne ya fara shigo da irin wadancan Babura masu kafa uku cikin jihar ta Lagos.

An fara lakabawa wadancan babura sunan Keke ne, a farkon lokacin da suka bayyana cikin wannan Kasa. Bayan Buba Marwa, sai kuma aka koma kiran su da Keke Marwa.

A lokacin shugaba Obasanjo, farkofarkon wannan Jamhuriyya ta hadu (4) da muke ciki, yayinda hukumar “National Agency for Poberty Eradication Program”, NAPEP, ta shigo da irin wadancan Babura masu tarin yawa cikin Kasa, karkashin tsarin rage radadin talauci musamman ga Matasa, daga lokacin ne aka canza kiran Baburan, daga Keke Marwa zuwa Keke Napep, lokacin da Dr Magnus Kpakol ke jagorantar hukumar

Duk da irin matsalolin da ba a rasawa tattare da Keke Napep, sai ya samu cikakkiyar karbuwa daga jama’ar Kasa bayan bayyanar tasa. Nan da nan ne ya shiga rukunin ababen da al’uma suka laru a kansu, a harkokinsu na zirga-zirgar yau da kullum. Mutanen Kasa a lokacin, na ganin, yin ta’ammuli da Baburan na Keke Napep, ba su fi karfin tattalin arzikinsu ba. Sannan kuma ga biyan-bukata da baburan ke da, wajen kai mutum inda yake so cikin kankanin lokaci. Duka sakuna da lunguna, Baburan na iya kutsawa ciki, sabanin motocin tasi-tasi da bas-bas.

Daga Ababen Sufuri Gabanin Keke Napep

Bas-bas da Tasi-tasi hada da baburan acaba ko Okada, kusan da sune aka faye amfani cikin garuruwan Kudunci da Arewacin wannan Kasa a matsayin ababen sufurin da akasarin al’uma ke amfani da su, a harkokinsu na yau da kullum.

Daga cikin dalilan da suka taimakawa baburin Keke Napep ya karbu cikin sasannin wannan Kasa a lokaci guda na da tarin yawa, daga cikinsu, ta tabbata da daman mutanen Kasa sun fara dawowa ne daga rakiyar Baburan acaba ko a ce Baburan Okada. Ta kai ta kawo, cikin wasu jihohi na wannan Kasa ma har an fara haramta yin amfani da baburin na Okada.

Haramta Sana’ar acaba A Jihar Delta

A cikin Watan Nuwanba na Shekarar 2012 (Nobember 2012) ne, jihar Delta ta haramta aiwatar da sana’ar acaba ko Okada a cikin manyan birane da garuruwa na jihar. Sai dai bayan wannan haramci, ra’ayin jama’a ya kasu gida biyu ne. Wasu da dama, sun marawa gwamnati baya ne. Sannan, mutanen dake zaune cikin wuraren da aka haramta yin ta’amuli da Baburan, sun nuna rashin jin-dadinsu ga haramtawar.

A fili yake cewa, gwamna Dr Emanuel Ewetan Uduaghan na jihar ta Delta, akasarin al’umar jihar, sun yi matukar na’am da haramta zirgazirgar Baburan na acaba da sunan haya. Tukin ganganci, afkar da hadura babu kakkautawa tare da amfani da ake yi da baburan, wajen aikata laifukan fashi da makami, na daga hujjojin da masu lale-marhabin da wannan hukunci na gwamnatin jihar suka rika a matsayin kwararan hujjojin da za su wajabta yin watsi da munanan ayyukan da “yan Okadan ke aikatawa dare da rana cikin jihar.

Masu yin tofin-ala-tsine da hukuncin gwamnan kuwa, na cewa, danyen hukuncin na gwamna Emmanuel, na nunawa karara a fili, gwamnatin jihar ko kadan ba ta damu da wahalhalun rayuwa da al’umar jihar ke ciki ba. Sun kara da fadin, hayar da Matasan jihar ke yi da irin wadancan Babura, na matukar taimaka musu, wajen bunkasa tattalin arzikinsu. Uwa-uwa, kange Matasan ga barin waccan sana’a ta achaba, ba komai hakan zai haifar ba, sai karuwar rashin ayyukan-yi da yaduwar ayyukan ta’addanci a jihar da kuma sace-sace.

Sai dai duk wancan korafi na wadanda ba sa goyon bayan wancan umarni na gwamna, ta tabbata cewa, adadin wadanda ake rungumowa ko kwasa a kai su Asibiti, a matsayin wadanda irin wadancan Babura na acaba suka jazawa jin-ciwo, ya matukar raguwa. Asarar rayuka da dukiyoyi sun ja-baya ainun, bayan fatattakar “yan achabar daga kan kwalta da gwamnan ya yi.

Kyamatar miyagun ayyukan masu baburan acaba ya cigaba ne a tsakanin jihohin wannan Kasa ta Nijeriya a wancan lokaci, domin kuwa, ba ya ga jihar Delta, za a ga ma wasu jihohi sun bi sawun jihar Delta, wajen haramta hayar baburan na okada. Jihar Lagos ma, na daga cikin jihohin da suka haramta waccan sana’a ta haya da babura masu kafa-biyu.

Yin watsi da harkar baburan masu kafa da gwamnoni suka fara yi, ya yi sanadiyyar rage shigo da baburan daga Kasashen Duniya zuwa Nijeriya. Ta tabbata cewa, cikin Shekarar 2015 da 2016, kasuwar shigo da baburan acaba zuwa nan Nijeriya ta fadi warwas!. Cikin Shekarun 2017 da 2018 kuwa, kasuwar shigo da baburan Keke Napep daga Kasashen ketare zuwa Nijeriya ta kankama matuka, hakan na da alaka da rushe sufurin baburan acaba da da yawan gwamnoni a Kasar suka yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: