Connect with us

FILIN FATAWA

Ya Halatta A Sanya Bakin Kaya Saboda Nuna Alhini?

Published

on

Tambaya:

Assalamu alaikum, inada tambaya, akwai wata abokiyar karatunmu Kirista da ta mutu, shi ne aka nemi kowa a makaranta ya sa bakaken kaya, shin ya halatta a musulunci mu musulman Makarantar mu sa?

Amsa:

Wa’alaikumus salam, Bai halatta ku sanya ba, saboda musulunci ya hana kamanceceniya da Kafirai. Sanya bakin kaya lokacin musiba, ba al’ada ce ta musulmai ba. Allah ne mafi sani. Hukuncin Yin Kiran Sallah Ba Tare Da Tsarki Ba

Tambaya:

Assalamu Alaikum, malam ko ya halatta mutumin da yake da janaba ya kira sallah?

Amsa:

To dan’uwa wasu daga cikin malamai suna cewa tsarki ba sharadi ba ne yayin kiran sallah, saboda babu wani nassi ingantacce wanda ya nuna hakan, don haka ya halatta ga mai janaba, da mai karamin kari su yi kiran sallah, saidai abin da ya fi shi ne yin cikakken tsarki kafin kiran sallah, saboda fadin Annabi (SAW) “Ina kin na ambaci Allah alhali ba ni da tsarki”, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 16, kuma Albani ya inganta shi a Sahihu-sunani Abidawud 1\16. Don neman Karin bayani duba: Fathul-bary 3\113 da Majmu’u fataawaa wa makaalatin mutanawwi’a 10\338.

Taurin Bashin Mawadaci Zalunci Ne!

Tambaya:

Assalamu alaikum, akramakallahu tambaya ta akan bashi ne, akramakallah ya muslunci ya tsara akan wadannan ka ke bi bashi amma sun hanaka kuma suna da kudin. Wace azaba Allah ya tanadarwa wadan da basa biyan bashi. Na gode.

Amsa:

Wa’alaikum assalam To dan’uwa taurin bashi mawadaci zalunci ne yana halatta mutuncinsa da yi masa ukuba kamar yadda hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito a Musnad a lamba ta: 17945, kuma Ibnu Hajar ya kyautata ya tabbabtar da hakan. Duk wanda ya karbi bashin mutum da niyyar zai mayar masa, Allah zai taimaka masa wajan mayarwa. Ya halatta ka kai wanda kake bi bashi kotu, don ta amsar maka hakkinka, mutukar ka tabbatar yana da shi amma ya hana ka, saboda hadisin da ya gabata. In har aka tabbatar da cewa rashin kudi ne ya hana shi biya, ya wajaba a jira har ya samu, kamar yadda aya ta: 280 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan. Biyan bashi akan lokaci yana da mutukar muhimmanci, saboda wanke tukunya don gobe yana saukake girki. Allah ne mafi sani.

Hukuncin Sayar Da Kaya A Wurin Da Aka Saya

Tambaya:

Mutum ne zai kawo mota wacce tayi hatsari sai wani ya siya misali dubu 600’000 ,to shi wanda ya siyar yana wajan zai ga an siyar da ita kamar million daya.
Amsa:

Game da tambayarka da ka yi, bai halatta mutum ya sayar da abin da ya saya ba, a wurin da ya yi sayayyar, Annabi s.a.w. ya haramta hakan, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 3499. Sharia ta haramta hakan ne, saboda zai iya bude hanyar hassada da kiyayya tsakanin masu cinikayya. Allah ne mafi sani.

Hukuncin Zakkar Noman Rani

Tambaya:

Assalamu alaikum, Malam Dangane da zakkar amfanin gona da ka noma ta hanyar noman rani da aka yi amfani da ban ruwa na inji kuma da aka yi lissafin abin da aka kashe, sai ya zama kayan da aka samu bai biya kuDin wahalarsa ba, yaya zakkarsa za ta kasance? Allah ya kara budi! Amsa: Wa alaikum assalam, duk da haka za’a bada zakkarsa mutukar ya kai Sa’i 300. Za’a fitar da daya bisa ashirin, 1/20 na abin da aka samu, wato in Sa’i dari uku ne sai a bayar da Sa’i sha biyar, in dari hudu ne sai a bada Sa’i ashirin، kamar yadda hadisin Buhari mai lamba ta: 1483 ya nuna hakan. In har bai kai wancan mikdarin ba to babu zakka a ciki. Shari’a ta rataya zakkar kayan amfanin gona ne da samun Sa’i dari uku, Hakan kuma ba Shi da alaka da faduwa ko samun riba a noman. Allah ne mafi sani.

Mene Ne Hukuncin Sanya Hakorin Makka A Ma’aunin Shari’a?

Tambaya:

Assalamu Alaikum Dr, dafatar ka tashi lafiya Alagafarta malam ina neman karin bayani game da Hauren makka da alhazzai suke sakawa akan cewa shima yana haddasa lum’a a lokacin da mutum ya zo kuskurar baki ruwa ba za su taba ainihin Hauren da Allah ya halicci mutum da shi ba?

Amsa:

Wa alaikum assalam, a zahiri sanya Haure bayan aikin hajji ba matsala ba ne ta fuskar Lam’a tun da kurkure baki sunna ne a wajan da yawa daga malamai, wannan yasa rashin shafar ruwan ga hakori daya tare da Dr. Jamilu Yusuf Zarewa 08135018032 ba zai yi tasiri ba. Amma zai iya zama matsala saboda yana iya janyo riya, tun da galibi wanda zai sanya yana yi ne saboda yaje hajji ko dan ace masa Alhaji, hakan ya sa barinsa shi ne ya fi. Idan ya kasance an yi hauren ne da zinare to haramun ne namiji ya sanya saboda Annabi (SAW) ya ce: (An haramta zinare ga mazajen Al’umata, amma an halatta ga matayansu) kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: (1720). Allah ne mafi sani.

Zan Iya Kara Gashi Saboda Mijina?

Tambaya:

Malam na yi rashin lafiya kaina ya kwakuye, mijina yana bakin ciki, in ya ga kaina, zan iya kara gashi don zaman auranmu ya kara dadi?

Amsa:

To ‘yar’uwa wata mace ta je wajan Annabi (SAW) ta ba shi labari cewa: ‘Yarta ta yi rashin lafiya gashinta ya fadi, kuma gashi mijinta ya umarceta da ta kara mata gashi, shin za ta iya karawa? sai Annabi (SAW) ya ce mata: A’a, saboda an la’anci masu kara gashi”. Bukhari ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4831. Hadisin da ya gabata, yana nuna cewa: bai halatta mace ta kara gashi ba, ko da kuwa mijinta ne ya umarceta, saboda hakan zai sa ta shiga tsinuwar Allah. Allah ne mafi sani.

Ta Haihu Kafin Ta Cika Wata Bakwai Da Aure, Yaya Hukuncinta?

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar da ita batayi wata bakwai ba 7 ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara (9) to malam meye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a musulunci?

Amsa:

Wa’alaikum salam, In har an San tanada ciki aka yi auran wannan hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai inganta ba a zance mafi inganci, amma in haihuwa ta yi bayan wata bakwai, kuma ba’a santa da ciki ba to dansa ne, saboda ayar suratu Lukman da tá suratul Ahkafi sun nuna cewa ana iya haife ciki a watanni shida. Auran dá aka yi dá cikin shege ba tare da an sani ba ya inganta, saidai ba za’a danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba shi ya yi ba. In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure bai halatta ya take ta ba har saí ta haihu, saboda fadin Annabi (SAW) “Duk wanda ya yi imani dá Allah da ranar Lahira to kar ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa” kamar yadda Abu-dawud ya rawaito. In ta haihu za su iya cigaba dá mu’amalarsu ta aure, musamman in bai sani ba saí dá aka daura. Allah ne mafi sani.

Hukuncin Yin Sallar Jam’i A Gida

Tambaya:

Assalamu alaikum. Malam mene hukuncin sallar namiji da ba ya son zuwa masallaci jam’i saidai ya tara iyalinsa a gida ayi sallah tare?

Amsa:

Wa alaikum assalam. To ‘yar’uwa Malamai sun yi sabani game da sallar jam’i a masallaci. 1. A wajan malaman Malikiyya zuwa sallar jam’i sunna ne saboda fadin Annabi S. A.W. “Sallar jama’a tafi sallar mutum daya da lada ashirin da bakwai” hadisin yana nuna ingancin sallar wanda ya yi sallah shi kadai, tun da an tabbatar masa da lada daya. 2. Ya wajaba yin sallah a masallatai a cikin jama’a saboda fadin Annabi (SAW) “Na yi niyyar na yi umarni a tsayar da sallar jam’i, ni kuma na je na kona gidajan wadanda ba Sa halarta sallah a masallaci” wannan ita ce maganar Malamai da yawa. Ibnu-Mas’ud yana cewa: “Babu wanda yake kin zuwa sallar jam’i sai munafiki, wanda aka san shi da munafunci, akan kawo mutum ranga-ranga ba shi da lafiya a tsayar da shi a tsakanin Sahu”. Wani Makaho ya zo wajan Annabi (SAW) ya nemi ya yi masa izni ya yi sallah a gida saboda ba shi da Jagora, ya ba shi izni, bayan ya tafi sai ya Kira shi ya ce masa kana jin kiran sallah? sai ya ce E, sai ya ce to ka amsa”. Allah yana cewa a Suratul Bakara aya ta (43): “Kuma ku yi sallah tare da masu yin sallah” A bisa dalilan da suka gabata za mu fahimci cewa: Yin sallar jam’i a masallaci shi ne abin da Shari’a ta zo da shi, kuma wajibi ne ga wanda yake da iko, tun da ga shi har Annabi (SAW) ya yi niyyar zai kona gidan wadanda ba sa halarta. Idan akwai nisa tsakaninsa da masallaci ko kuma yana da lalura ba za’a ce ya aikata haramun ba in ya yi sallah a gida tare da iyalansa saboda fatawar Malikiyya da ta gabata da kuma aya ta karshe a suratul Hajj wacce take nuna sauki da rashin kunci a addinin musulunci. Allah ne mafi sani.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: