Connect with us

LABARAI

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Nijeriya 1, 460 Cikin Wata Bakwai- Gwamnati

Published

on

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa mutum dubu 1, 460 suka rasa rayukansu a hare-hare 330 da ‘yan bindiga suka kaddamar a cikin watanni bakwai da suka gabata, musamman a yankunan Arewa maso yammacin kasar .

A cewar Dk. Amina Shamaki, jami’ar dake kula da ayyuka na musamman a Ofishin babban Sakataren gwamnatin Nijeriyar yayin wani taro kan al’amuran tsaro da ya gudana a jihar Kebbi, ta ce adadin na daga cikin alkaluman da bincikensu ya nuna.

Dk. Shamaki ta bayyana cewa kawo yanzu kalubalen tsaro shi ne babban abin dubawa musamman a yankunan arewa maso yammacin kasar da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Babbar jami’ar gwamnatin Nijeriyar ta bayyana cewa hare-haren sun faru ne daga watan Janairun bana zuwa Yuli, ko da dai ta ce an samu raguwar hare-haren ‘yan bindiga cikin watan Yuni da Yulin musamman a jihar Zamfara.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!