Connect with us

WASANNI

‘Yan Wasan Nijeriya Mata Sun Lashe Zinare A Maroko

Published

on

Tawagwar kwallon kafar Nijeriya ta mata ‘yan kasa da shekara 20 ta lashe kyautar Zinare a gasar wasannin motsa jiki ta nahiyar Afrika da ke gudana a kasar Maroko. Nijeriya ta samu nasarar ce bayan doke Kamaru da kwallaye 3-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Da fari dai ‘yan matan na Nijeriya da Kamaru sun kammala wasan a 1-1, bayan shafe mintuna 120 suna fafatawa, abin da ya kai ga bugun Fanareti.

Nijeriya ta taba lashe kyautar Zinare a fagen kwallon kafar mata yayin wasannin motsa jikin nahiyar Afrika a shekarun 2003 da 2007.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: