Connect with us

LABARAI

Aikin Hanyar Kano Zuwa Abuja Na Ci Gaba Da Sanadiyyar Mutuwar Mutane Masu Yawa

Published

on

  • Bai Wa Masu Garkuwa Cin Karensu Ba Babbaka
  • Haifar Da Cunkoson Ababen Hawa

Lokacin da ka fara aikin hanyar Kano zuwa Abuja, al’umma suka fara murna sakamakon saukin da za su samu wajen gudanar zirga-ziraga, musamman da yake ana kara fadin hanyar da ingantata, yadda matafiya za su samu walwalar tafiye-tafiyensu.
Amma sai ga shi abin da ke biyo baya, sakamakon wannan aiki babu dadin ji, domin kuwa kusan duk inda aka fara wannan aiki ana mayar da direbobi su bi hannu daya, maimakon hannu biyu inda mai zuwa da mai tafiya kowa zai bi hannaunsa daban.
Mayar da direbobin bin hannu daya ya haifar da abubuwa masu tarin yawa kama daga mutuwar dimbin mutane da asarar dukiyoyo masu tarin yawa da bai ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane damar cin karensu babu babbaka da kuma haifar da cunkoson ababen hawa.
Idan ka tawo daga Kano an fara aikin wannan hanya tun daga Kano har zuwa Kwanar-dangora kimanin kilomita 80 daga Kano wanda kuma kusan duk tsawon wannan tafiya an koma ana yinta a hannu daya maimakon hannu biyu saboda wannan aikin.
Wannan ta sa a wannan tsakanin ake samun munanan hadari wadanda ke sanadiyyar mutuwar jama’a da dama. Matafiya a wannan hanya sun tabbatar mana cewa, wuraren da aka fi yin hadari a wannan tsakanin akwai garin karfi da gab da shida garin Kura, wanda a wannan wuri ne ma tsohon shugaban gidan rediyon jihar Kano Umar Sa’idu Tudun wada ya yi hadari, kuma nan take kwanansa ya kare.
In ka bari Kura akwai Gadar ‘Yan kifi kusa da Dakatsalle nan ma wurin ya yi sanadiyyar mutuwar al’umma masu tarin yawa. San nan in ka baro garin Gwarmai, sai kuma gab da shiga Kwanar-dangora. Wadannan wurare ne da Allah kadai ya san adadin mutanen da suka mutu da yawan asarar dukiyar da aka yi.

Daga matafiya ba za su sake fuskantar tashin hankali ba sai sun zo Dumbin Rauga, bayan sun wuce Zariya kadan inda aikin hanyar ya zo. Daga nan har kusan shiga Kaduna.
Mukaddashin Kwamandan Shiyyar Zariya na Hukuma Kiyaye Hadura Alhaji Muktar Zaki, ya shaidawa wakilinmu cewa, kusan kullum sukan samu rahoton afkuwat hadari musamman daga Dumbin Dutse zuwa Dumbin Rauga.
Jami’in Hukumar ya ce, duk da cewa, akwai babbar matsala wajen yin amfani da hannu daya musamman inda aka saba da esfires, to amma rashin hakurin direbobi na daga cikin abubuwan da ke jawo hadura a kan wannan wannan.
Saboda haka ne ma ya yi kira da babbar murya ga direbobobin da su dinga yin hakuri sannan kuma su dinga kiyaye dokikin hanya. Ya ce wani lokacin za ka samu direba na wuce dan’uwansa har ta hannun sauka wanda kuma wannan ba daidaidai ba ne, saboda haka ya roki direbobin da su taimakawa rayuwar al’umma, su yi tuki cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Shi kuwa, Bello Direba wanda ya shafe shekaru kullum yana zuwa Abuja daga Zariya, cewa ya yi lallai aikin hanyar na daga cikin abin da ke kawo cinkoson ababen hawa da haifar da hadari a wannan hanya. Ya ce, tun daga Dumbin Dutse zuwa Dumbin Rauga zuwa Birnin Yero zuwa gadar Jaji har zuwa gab da shiga Kaduna wannan wurare sun yi sanadiyyar mutuwar mutane masu da jawo asarar dukiyoyi da haifar da cunkoso.
Ya ce, wani lokaci idan hanya ta kulle sai sai a yi zagaye Kawanar Farakwai a fito ta Rigachukum ga mai tafiya daga Zariya ke nan, ga mai tawowa daga Kaduna kuwa sai dai ya biyo ta Marabar Jos ya bulla ta Igabi sannan ya fito ta kwanar Farakwai in ba haka ba kuwa bai san lokacin fitarsa ba.
Haka kuma in kawuce wannan siradin ka nufi Abuja Bello ya ce da ka wuce Jere kadan, nan ma na fada fargabar hadari har sai ka kusa shiga gaba da Zuba.
Ya ce, baya ga wannan fargaba hadari sai kuwa wata babbar fargabar wadda ta sa mutane da yawa ke kauracewa hanyar wato annobar garkuwa da mutane wanda ko a ranar Talata masu garkuwan sun sace mutane masu yawa ciki har da daliban jami’ar Ahmadu Bello guda uku. Sannan ko a jiya Juma’a an samu rahoton sace wani dan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar Zariya.
A kwanan baya an ruwaito Ma’aikatar kula da Ayyuka ta jihar Kaduna ta sanar da cewa, kimanin mutum sama da hamsin suka rasu wasu kuma suka samu munanan raunuka a hadurran da suka auku a kan hanyar a tsakanin watan Janairu zuwa watan Yulin 2019.
Su ma al’ummar yankin sun sha kokawa kan yadda wasu direbobin suke musamman na manyan motoci da ke yin gudu, a kan hanyar, duk da aikin da ake kan gudanarwa a kan hanyar.
Shugaban kungiyar direbobin da ke tashar Kantin Kwari Kaduna Kwamared Abdullahi Z. Garba ya ce, “ Motocin da ke bin hanyar suna janyo cunkoso musamman manyan motocin Terela da direbobin su suke ajiye su a gefen hanyar, musamman daga Mararraba zuwa Rigachikun, tunda an ware masu gareji inda za su dinga ajiye su ya kamata su koma can suma direbobin na masu yin haya dana gida, su dinga zamowa masu hakuri a yayin da suke a kan hanyar .”
“Muna kira ga gwamnatin Kaduna su dauki mataki don su koma inda aka ware masu.” Kuma na lura, Kamfanin dake gudanar da aiki a kan hanyar yana kokari duk da cewa, wasu kamfanonin dake yin hanya ba sa yin aiki da damina amma kamfanin yana iya kokarinsa.
Shi ma Shugaban kungiyar direbobi na tsahar motar da ke a Kasauwar Bacci Kwamarade Lawal Abubakar ya ce, “Rashin hakurin wasu direbobin ne ke janyo cunkoson bama wai sai a hanyar Kaduna zuwa Zariya ba, gaskiya dari bisa dari wasu direbobin suna daga cikin wadanda ke janyowa wasu domin suna barin hannunsu su bi hannun wani direban don wai suna sauri, inda hakan ke janyo ba wai cunkoso ba, har da janyo hadurra a kan hanyar.”
Ya kara da cewa, “Jami’an tsaro dake sanya ido a kan hanyar suna yin nasu kokarin wajen rage cunkoson, sai dai wani lokacin suna kara haddasa cunkoson, idan sunga wani direban ya dauko kaya ko fasinjoji fiye da kima wajen su yi kokarin kama shi a kan hanyar, hakan yana kara janyo cunkoson na ababen hawa.”
A karshe, direbobi da matafi wadanda su ke dandana wannan wahala sun yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da in zai yiwu a dinga bayar da damar duk inda aka kammala aikin a bude hanyar a ci gaba da binta musamman da daddare.
Sannan kuma jami’an Hukumar Kiyaye hadura sun roki direbobi da su zama masu bin doka da oda domin tseratar da rayukan jama’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: