Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Fakewa Da Batun Hong Kong Yayin Tattaunawar Ciniki Ba Za Ta Yi Amfani Ba

Published

on

A jiya Juma’a ne wasu Amurkawa, suka sake bayyana cewa, tattaunawar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasarsu da kasar Sin tana da nasaba da batun Hong Kong, sai dai kasa da wata guda da ya gabata, wadannan mutane sun taba bayyana cewa, “Hong Kong wani bangare ne na kasar Sin, kuma kasar Sin da kanta za ta daidaita matsalar, ba tare da bukatar shawara ba.”
Wadannan mutane sun sauya matsayarsu kamar yadda suke so, abun da ke nuna cewa, da wuya a iya tabbatar da sahihancin kalamansu. Kana an lura cewa, idan aka gudanar da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka lami lafiya, wadannan Amurkawa kan ce, ba za su tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin ba, amma idan sassan biyu wato Sin da Amurka suka gamu da matsala yayin da suke gudanar da tattaunarwar, to za su hada batun Hong Kong da tattaunawar, lamarin da ya nuna cewa, wadannan Amurkawa ba su damu da yanayin da Hong Kong ke ciki ba, kawai fakewa suke yi da batun, ta yadda za su matsawa gwamnatin kasar Sin lamba.

Hakika batun Hong Kong harka ce ta cikin gidan kasar Sin, kuma gwamnatin kasar Sin tana gudanar da harkokin yankin bisa tsarin mulkin kasar da kuma dokar yankin Hong Kong. Don haka, bai dace kasashen ketare su tsoma baki ciki ba. Yanzu haka wadannan Amurkawa sun amince da Hong Kong a matsayin yanki daya dake cikin kasar Sin a fili, kuma ya dace gwamnatin kasar Sin ta daidaita matsalar da kanta, sai dai dole ne su cika alkawarin da suka dauka. Ko shakka babu, ba za su cimma manufarsu ta amfani da batun Hong Kong don matsawa kasar Sin lamba yayin da suke tattaunawar tattalin arziki da cinikayya ba.(Mai Fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: