Connect with us

WASANNI

Van Dijk Ya Fi Messi Da Ronaldo Kokari — Arjen Robben

Published

on

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Chelsea da Bayern Munchen, Arjen Robben, ya bayyana cewa dan wasa Virgil Van Dijk yafi Messi da Ronaldo kokari a kakar wasan data gabata.

Dan wasan Liverpool, Virgil Van Dirk shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na nahiyar Turai na bana bayan da ya taimakawa Liverpool ta doke Tottenham a wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai da aka kammala.

Van Dijk mai shekara 28 ya yi nasara ne a kan shahararrun ‘yan kwallon duniya guda biyu, Lionel Messi na Barcelona da tsohon dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo mai buga wasa a Juventus.

Dan wasan ya zama kashin bayan Liverpool tun lokacin da ya koma Anfield da buga wasa daga Southampton a Janairun shekara ta 2018 kan fam miliyan 75 a matsayin dan wasan baya mafi tsada a lokacin.

Van Dijk dan kwallon tawagar Netherlands ya taimakawa kasarsa ta kai wasan karshe a gasar cin kofin UEFA Nations League a bana, inda ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Portugal mai masaukin baki.

Haka kuma an bayyana ‘yar Ingila, Lucy Bronze a matsayin gwarzuwar macen da babu kamarta a fagen tamaula a Turai a bana sannan mai tsaron baya Bronze, ta yi nasara ne kan wadanda ta yi takara da su da ya hada da Ada Hegerberg da kuma Amandine Henry.

Bronze ita ce macen farko daga Ingila da ta lashe kyautar da masu horar da tamaula mata ke yi da wasu ‘yan jarida ke zaba kuma ana ganin zata iya lashe babbar kyautar da hukumar kwallon kafa ta duniya ke bayarwa a karshen shekarar nan.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: