Connect with us

WASANNI

Wanyama Zai Koma Club Brugge

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta amince zata sayar da dan wasanta na tsakiya, Bictor Wanyama, zuwa kungiyar kwallon kafa ta Club Brugge akan kudi fam miliyan 12 bayan an dauki kwanaki ana tattaunawa.

Dan wasan, mai shekara 28 a duniya, dan asalin kasar Kenya, wanda ya koma Tottenham daga kungiyar kwallon kafa ta Southampton ya buga wasanni 93 a kungiyar tun bayan komawarsa shekaru hudu da suka gabata.

A kakar wasan data gabata dai Wanyama wasanni 13 kawai ya iya bugawa kungiyar sakamakon ciwon cinya da yayi fama dashi kuma hakan yasa kociyan kungiyar yaga akwai bukatar ya rabu da dan wsaan.

Tun bayan da aka kammala kakar wasan data gabata dan wasan ya bayyana cewa yana fatan zai bar kungiyar domin komawa inda zai dinga buga wasa akai-akai kuma kungiyoyi da dama a gasar firimiya sun nemi Tottenham data sayar musu dashi.

Sai dai kamar yadda rahotanni daga kasar Ingila suka bayyana, kungiyoyin Tottenham da Club Brgugge ta kasar Belgium sun amince da cinikin dan wasan akan kudi fam miliyan 12 inda ake saran za’a kammala cinikin kafin ranar 2 ga watan Satumba.

Club Brugge, wadda ta lashe gasar rukuni rukuni ta kasar Belgium shekaru biyu da suka gabata ta fito acikin rukunin daya hada da Real Madrid da PSG da Galatasaray a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai na bana.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: