Connect with us

TATTAUNAWA

Published

on

A kwai Rufin Asiri A Harkar Farauta – Mai Dawa Sani Lawai

Malam Sani Lawai wani mafaruci ne da ya shahara a sabgar farauta a fadin Jihar Katsina, a gefe guda kuma ya kan bayar da taimako na wasu magunguna amma a ba’a fannin bokanci ko surkulle ba. Ya yi wa wakilin LEADERSHIP A Yau Lahadi RABIU ALI INDABAWA bayani kan sha’anin bayar da magani da farauta, in da ya ce akwai matukar rufin asisri mai yawa a sha’anin farauta. Don jin yadda ta kasance ku biyo mu a wannan hirar.

Da fari masu karatu za su so sanin cikakken sunaka

Ni sunana Sani Lawai Malam Sani mutumin wace Jihace kai?

Ni mutumin Jihar Katsina ne Kofar Guga

Mecece sana’arka?

Sana’ata a da ina aikin kwadago kamar aikin kankare haka ko kuma gini, daga baya kuma sai na samu aikin mota Tifa, tun muna zuwa mu tono yashi mu loda mata, har ta kai ga na fara aikin motar wato ina tukawa da kaina. To kuma sai aka samu tsaikon ayyuka, to kuma motocin nan na kwangila ne, sakamakon ajiye motocin da aka yi ba sa aikin komai sai aka mayar da su gida, a yanzu dai ina aiki ne a karkashin kamfanin Dahiru Mangal.

To na ganka da shigar kayan saki, shin kai dan daba ne ko mafarauci?

To asalina dai Bafulatani ne gaba da baya, wannan kayan saki dama mu muke da su, kuma dama gadonmu ne wannan, kuma nib a dan daba ba ne, amma abin da ya san a kan ci gaba da sa wadan nan kayan, Allah ya san a dan fahimci wani abu game da magunguna, iana bayar da magani haka taimako na kariyar jiki, a hankali a haka- a haka wanda ya gani yana tare da ni za mu yi magana da shi, ni ba na tare da barawo, bana sha’awar dan daba, mu tsakaninmu da dan daba sai dai in ya gagara a ce da mu mu je mu kamo shi.

To idan na fahimce ka kamar kana dan taba farauta ke nan.

Eh duk shekara ina zuwa farauta, amma shekara biyu ta wuce na bar zuwa farauta, domin an ce idan kana da iyali dole wasu abubuwan sai ajiye su, saboda karfi karewa yake yi ba karuwa yake ba, an dan manyanta bakin gwargwado.

To me ya sa irinku ba kwa so a kira ku da ‘yan daba?

Eh gaskiya dai mu ba ‘yan daba ba ne, abin da ake nufi da ‘yan daba, wanda ba ya jin tsoron kowa, baya tausayin ya karbe mata abin ka, bai dai san darajar kowa ba, shi ne ma’anar daba kuma bin da muka sani kenan.

To a irin al’amari na bayar da magunguna wane irin kalubale ka fuskanta kamar bayar da magani ya kiyin aiki ko ya cutar da wani?

Gaskiya ni ban taba fuskantar wani kalu bale akan harkar bayar da maganin da nake yi ba, domin taimakona ba tallansa nake yi ba, wanda ya fuskanci abin da nake yi shi ne yake yin min tambaya, idan na ga ina da abin nan na taimaka masa in kuma ba ni da shi to zan gaya masa gaskiya ba ni da wannan abu.

To yanzu a takaice mai ba da magani za a kira ka ko mafarauci?

Duka ana iya hadawa a fada, in ka ce mafarauci to, in kuma ka ce mai ba da magani duk daya ne. To mafarauta irinka ana kiransu da wani suna musamman na jeji bayan sunansu na gaskiya, kai da wane suna ake kiranka? Ni Mai dawa ake ce min, saboda ba a nan Abuja ba, a yankinmu na Katsina in an fita daji ni ne babba a gare su, kuma idan mkua fita ba ma fadace-fadace ko da mun hadu da wasu mafarautan ba fada sai dai a gaisa a shige, in ma da wanda yake da dan ruwa a goransa yana iya taimaka wa wani, kuma bakin gwargwado idan muka fita muna samo alheri, baa bin da muka bari mu in maciji muka samu lahiya lau ne, komenene in dai ana ci to za mu ci.

To mu dawo maganar sanar magani, shin ka kai kamar shekara nawa kana yi?

A gaskiya tun da na taso ina yaro na kakannina su suka dinga nuna min wasu magunguna da ban-da ban na taimakon da za a taimakawa jama’a, kuma sun yi kashedin cewa kada in mayar abin duk wanda zan ba wa taimako sai mun yi tsada da shi ya biya ni, a ah duk wanda yake bukatar taimako na taimaka masa abin da ya ga dama ya kawo ya bani alhamdulillahi, ni babu haraji tsakanina da masu neman taimako.

Ka kai kamar shekara nawa kana wannan sana’ar?

Gaskiya zan kai kamar shekara 27 zuwa 28 ina wannan sabgar

To da yake abu ne ba na kyama ba, kana da muradin kamar danka ya gaje ka?

Eh, in dai zai bi irin akidata ina bukatar ya gaje ni, in kuwa ba zai irin akidata ba, to nib a na bukatar ya gaje ni.

To wane irin ci gaba aka samu a wannan harkar?

Eh alhamdulillahi, tun da muna samu bakin gwargwado mu ci mu sha har ma mu taimaka wa wani ka ga ke nan akwai inganci a sana’ar kenan, kuma ba ma kyamarta tun da ita muka tashi muka ana yi iyaye kakannina dai ne kadai ban ga sun yi ba, amma na ta so na ga iyayena suna yi.

Yanzu kana da kamar ‘ya’ya nawa?

‘Ya’yana uku domin da fari Allah bai nufe ni da samun haihuwa da wuri ba, to amma yanzu alhamdulillahi tun da yanzu ina da ‘ya’ya uku mace daya namiji biyu.

A karshe wane kira z aka yi wa masu sana irin taka kamar mafaruta da masu bayar da magani?

Eh to kiran da zany i ga mafarauta shi ne, duk wanda zai yi wannan sabgar ya tsaya yayi ta tsakaninsa da Allah, abin da ya samu shi ne na sa, kada ya mayar da na wani nasa in yana so ya ci gaba kuma ya ga ingancin abin ke nan. In kuma ya ce ba zai kan na sa ba, to ba zai ci nasara ba, idan ma ya samu nasara a yau to ya sani gobe fa ba zai samu nasara ba, domin Allah yana kallonsa. Kuma ka je da gaskiyarka gaban Allah shi ne ya fi maka sauki, Allah y aba mu ikon kwatanta gaskiya, ya raba mu son zuciya amin.

To mun gode mai Dawa Sani

Ni ma na gode sosai.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!