Connect with us

TATTAUNAWA

Aikin Hanyar Abuja Zuwa Kano Yana Tafiyar Hawainiya – Abdulaziz Salisu Mai Maggi

Published

on

Baya ga abin da ya shafi barazanar tsaro, wani kalubalen da ke fuskantar matafiya a kan hanyar da ta tashi daga Abuja zuwa Kano a halin yanzun shi ne rashin kyawun hanyar. Wanda kuma al’umma suke farin ciki da yanda a halin yanzun ta tabbata gwamnati ta bayar da kwangilar aikin hanyar, domin a sarari yake yanda aikin ya kankama. Sai dai kuma wani abin da jama’a suke kokawa da shi, shi ne yanayin da aikin ke tafiyar Hawainiya, wanda a sakamakon hakan, tafiya a kan hanyar ta kara zama aba mai tsananin wahalar gaske. Baya ga jin jikin da su kansu mutane suke fama da shi a kan hanyoyin, hatta su ma ababen hawan suna matukar jin jiki. A cikin tattaunawar da LEADERSHIP A YAU ke yi da masu ruwa da tsaki a kan abin da ya shafi hanyar, mun zanta da daya daga cikin Shugabannin al’umma, kuma daya daga cikin masu ruwa da tsaki a kan abin da ya shafi harkan sufuri, wanda shi ne, Alhaji Abdulaziz Salisu Mai Maggi, Sarkin Arewan Anguwar Mu’azu, Kaduna. Abin da ke biye nazarinsa ne a kan aikin da kuma shawarwarinsa ga al’umma da kuma gwamnati. Wakilinmu Umar A Hunkuyi, ne ya zanta da shi a ofishinsa da ke Kaduna. A sha karatu lafiya:

Me za ka ce kan irin yanda mutane suke yin guje-guje hakanan musamman a kan hanyar Kaduna zuwa Kano, duk da halin da ake ciki na gudanar da wasu ayyukan gyare-gyare a kan hanyar?

Tuki abu ne da ya shafi rayuwar al’umma, tun daga kan direba da fasinjojin da suke a cikin motarsa, hatta mutanan da suke a gefen hanya kowa akwai alhakin da ya hau kansa. Sau da yawa wasu ba su damu da halin da za su jefa mutane a ciki ba, don haka sukan yi gudu ne iya son ransu, sannan su ma wadanda suke zama a gefen hanyar ba kasafai ba ne aka san ka’idojin hanyan sakamakon za a iya cewa jahilci da jama’a suke a ciki, a gefe guda kuma akwai laifin ita hukumar domin aikinta ne ta wayarwa da jama’a kai ta nuna masu abubuwan da ya kamata su yi da wanda ya kamata su guda, a lokacin da suke tuki ko a lokacin da suke a kan hanyoyi, duk wannan abu ne da ya kamata a ce lokaci bayan lokaci ana yi wa al’umma fadakarwa a kansa.

Amma a halin yanzun hanyar misali Abuja zuwa Kano ta kusan zama tarkon mutuwa, inda ya zama kusan a kullum sai ka ji labarin an yi hatsari ko kuma ma an rasa rai, sannan abin takaici, su hukumomin da ya kamata su kula da ana bin dokokin hanyar da kuma ita hukuma da ya kamata ta sanya alamomi sai ka samu duk ba abin da suke yi ba kenan. Sai ya zamana idan ka ga ‘yan Kastelia ko jami’an kiyaye lafiyar hanya na Road Safety a kan hanya, duk hanzarinsu shi ne su kama wanda takardun motarsa ba su cika ba ko ya aikata wani laifi na daban domin su ci taransa. Sannan a sakamakon gyaregyare da ake yi a kan hanyar za ka samu a wurare da yawa an mayar da hanyar falan daya an rufe daya bangaren, wanda kuma a sakamkon hakan sai ka ga mutane suna ta guje-guje, wanda akwai bukatar su al’umma su kiyaye sannan ita kuma hukuma ta yi abin da ya kamata.

Wasu suna ganin tun farko gwamnati ba ta baiwa ingantattun kamfanonin da za su yi aikin hanyar nan a kan lokaci aikin ne ba?

To lokacin da aka diba na kammala aikin ya yi yawa, hakan ne kuma ya sanya aikin yake tafiyar Hawainiya, domin aikin da za a iya yi a cikin shekara guda sai aka ce an ba su shekaru uku, to ai ka ga sai yanda suka ga dama su yi, ballantana ma a yanda dai aikin yake tafiya a halin yanzun aikin zai ma iya fin shekaru uku din tun da yanzun an kusan shekara guda da bayar da aikin amma a inda ake a kan aikin yanzun cikin kasha 100 bai fi kashi 10 kila zuwa 15 na aikin da aka yi ba. Don haka akwai bukatar gwamnati ta ji koken mutane a kuma yi tunanin hanyoyin da za a magance hakan din. Ba wannan ce hanyar da aka fara bayar da kwangilar aikinta ba, an bayar da ayyukan hanyoyi da yawa wadanda ba a cika samun irin matsalar da ake samu a kan ita wannan hanyar ba. akwai bukatar a zauna a duba a ga wadanne hanyoyi ne ya kamata a bi domin a kaucewa hakan din.

A baya mutanan arewa suna kokawa da Ministan da ke lura da aikin hanyoyin, suna ganin kasantuwarsa ba dan Arewa ne ba ya sanya kamar bai damu da yanayin da hanyoyinmu a nan arewa suke a ciki ba. A halin yanzun ga shi an nada sabbin Ministoci an kuma baiwa dan arewa Ministan kula da aikin hanyoyin, wane kira za ka yi a gare shi na ganin ya taimaka musamman an gyara hanyar da ta tashi daga Abuja zuwa Maiduguri?

Tun da yanzun namu ne, kiran da za mu yi a gare shi shi ne, sau tari ayyukan da wancan tsohon Ministan ya yi a kan abin da ya shafi yankinsu abin ya ma zama mana kamar abin gori, An ci yaki da mu an kuma bar mu a kuturun bawa a wancan lokacin. Kusan duk ayyukan da ya kamata a yi mana mu a nan sai ya zamana a wancan sashen ne ake yinsu. Don haka akwai bukatar a yanzun shi mai girma Minista ya dawo da hankalinsa a nan, domin akwai kalubale mai yawa da muke fuskanta musamman abin da ya shafi sufuri a harkoki na yau da kullum a nan Arewacin Nijeriya. Akwai bukatar ya jajirce sosai domin akwai jan aiki a gabansa, ya yi iyakar yinsa domin ganin ya fitar da mu kunya da yankin namu baki daya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: