Connect with us

LABARAI

Bamu Da Wani Dan Ta’adda Da Ya Sami ‘Yancin Zama A Kano, Inji Wakilin Dukiya

Published

on

Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin dukiya tsohon shugaban kungiyar kasuwar Wapa ta Kano ya ce, yaga wani abu a wata jarida na bacin da cin mutunci da wulakanci gari kamar Kano wanda duk kullin tsiya daka kullo kazo Allah zai baje shi a garin nan. Amma wani ya ce mata matattarar yan ta’adda, ba mu da yan ta’adda a jihar Kano imma kasan inda suke kaje kanunasu hukuma ta yi maganinsu ammau bamu da wani dan ta’adda wanda ya sami yancin zama a Kano” inji wakilin dukiya.

Ya ce, gari ne wanda ake kwana sallah da karatu da addu’a ana sadaka da kyauta amma dan asalin Kano ba zai kirata matattarar ‘yan ta’adda ba sai dai bako wanda bai san mutuncin kansa ba.

Alhaji Yusuf ya kara da cewa Kano Allah ya yi mata daraja da ilhama saboda tsarkin garin yasa duk wanda yazo da mugun aniyarsa Allah yake warware shi. Ita Kano garine na kasuwanci kuma mahada a Afirka,ita ce in abu nema baka iya ba zaka zo ka koya addini ma wasu anan suka zo suka koya, amma har wani shakiyyi ya ce matattara ce ta ‘yan ta’adda wanda yafadi wannan ya koma ya roki gafarar Allah ya yafe masa domin “bamu da wannan tsarin bamu san shi ba muna yi wa Allah godiya kan haka”

Wakilin dukiyar ya ce, Ba zaka taba mans jihar Kano mu yan’asalin Kano ace mana matattara ce ta ‘yan ta’adda mu kyale ba. Al’umma su kara dagewa da addu’ou da aikin alkhairi domin Allah ya ci gaba da kare Kano da bunkasa cigabanta.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: