Connect with us

LABARAI

Dan Majalisa Mai Wakilitar Malumfashi Da Kafur Ya Tallafa Wa Al’umarsa

Published

on

Hajiya Aisha Women leader ta Babangida Talau dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Malumfashi da Kafur dake jihar Katsina a zauren majalissar wakilai dake Abuja ta bayyana cewar su kam sai Allah sambarka domin kuwa suna cigaba da samun tallafin kayan alheri a wajen dan majalissarsu a kowane lokaci a duk fadin mazabun kananan hukumomin Malumfashi da Kafur baki daya.

Aisha women leader ta Babangida talau Malumfashi tayi wannan lafazi ne a garin Malumfashi alokacin da al’ummar kananan hukumomin Malumfashi da Kafur suke karbar tallafin da  dan  majalissarsu  ya kawo ma al’ummar yankin na yar besfa wadda akafi sani da suna yar kurkura da injinan casar masara da shinkafa da sauran makamantansu, women leader taci gaba da cewa dan majalissar ya saba da kawo musu irin wadannan tallafi na keke NAPEP da injinan casar shinkafa da masara da sauran kayayyakin da mata da maza manoma suke amfani dasu a wajen gudanar da harkokin rayuwarsu na neman abinci na yau da kullum.

Hajiya Aisha ta ci gaba da cewa wajibin sune al’ummar wadannan yankuna guda biyu na Malumfashi da Kafur su nuna farin cikinsu da jin dadi da sanya albarka da kuma fatan alheri ga wannan bawan Allah bisa ga wannan karamci da yake yi wa al’ummar mazabarsa na Malumfashi da Kafur sannan kuma ta umurci ‘yan siyasa maza da mata na kananan hukumomin Malumfashi da Kafur da su cigaba da bawa Babangida Talau hadin kai da goyon baya tare da fatan alheri bisa ga wannan jagoranci da yake yi acikin adalci a kananan hukumomin Malumfashi da Kafur a duk fadin mazabunsa.

Sannan kuma tai kira ga sauran ‘yan majalissun jihar Katsina da Nijeriya baki daya dasu ci gaba da koyi da halayen wannan bawan Allah Babangida Talaud dan majalisar kananan hukumomin Malumfashi da Kafur domin kara bunkasa al’ummar mazabunsu da Nijeriya baki daya, karshe ta ya bama Gwamnan jihar Karsina Alhaji Aminu Bello Masari a kokarinsa na kauda miyagun ayyukka a jihar Katsina da kawo kyawawan abubuwan da za su taimaki jihar Katsina da Nijeriya baki daya
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: