Connect with us

LABARAI

Matsalar Tsaro: Yankin Jibia Na Cikin Halin Kakani Ka yi, Inji Kungiyar Matasan Jibia

Published

on

Kungiyar Matasan karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina sun nuna alhini da damuwa game da matsalar tsaron da ta addabin yankin na Jibiya wanda hakan ya haifar da hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da jama’a da satar dabbobin al’umma

A wani taron maneman labarai da kungiyar ta kira a Katsina sun bayyana cewa ‘yan bindigar suna yi masu ta’addanci ne musamman wajen yin ta’annati da yin fyade ga ‘yan mata da matan aure gami da  kisan gilla tare da yin garkuwa da mutane.

Shugaban kungiyar Matasan na Jibia, Alhaji Gide Dahiru ya ce a makon da ya gabata a cikin kwanaki goma sun kai farmaki a kauyuka shida da suka hada da  Tsayau da Zandam da  Mallamawa da Karauki da Shimfida, tare da Tsugunni duk a cikin karamra hukumar Jibia.

Ya kuma bayyana cewa ‘yan ta’adar sun fara shiga kauyen tsayau ne da ke akan babban titin da ke zuwa jihar Zamfara, ranar Lahadi 18 ga watan Ogustan 2019 da misalin karfe 1:45 na maraice, suka yi masu hasarar rayukan mutane 4, kuma suka  tafi da mutane 2 tare da rasa rayukan dabbobi marassa adadi.

A cewar shugaban kungiyar a garin Zandam kuma sun shiga ne ranar laraba wacce tayi daidai da 21 ga watan takwas na shekara 2019 da misalin karfe 10:40 na dare, inda suka yi masu hasarar rayukan mutane 4 da raunata mutum 3 gami da kwashe dabbobi 85  d suka hada shanu, tumaki, zuwa awaki.

Alhaji Gidd’e Dahiru bai tsaya nan ba sai da ya cigaba da bayanin kamar haka “Sannan kuma sun shiga Mallamawa ranar alhamis 22 ga watan takwas na wannan shekarar da misalin karfe 10:15 na

dare,  inda suka yi fyade ga matan aure da ‘yan mata, kuma suka tafi da mutane kimanin 14, suka kone masu mashinan hawa guda 13 kuma suka tafi da mashin 14 gami da shanu 500, daga bisani kuma suka kira daya daga cikin ‘yan  garin ta wayar salula suka shaida masa cewa ba za su sakar masu iyalansu ba har sai sun bada kudin fansa Naira milyon 30”.

Haka kuma shigaban ya ce abin bai tsaya nan ba, inda ranar 23 ga wata kuma sun fafata a garin Kaura da kauyen karauki, sannan kuma a yammacin ranar lahadi 25 ga watan din suka je garin Shimfida da misalin karfe 6:00 na maraice, inda suka kashe mutum 4, suka kone motoci 5 gami da mashinan hawa 80, sannan suka raunata mutum 4 kuma suka yi garkuwa da kimanin mutane 29 Kuma suka ce masu Naira milyon 150 kudn fansar iyalansu.

Daga karshen ya rufe da cewa ko a ranar laraba 28 ga wata, tsakar dare suka je kauyen Tsugunni, inda suka yi masu barazana tare da kwashe masu dukkanin dabbobin garin da suka hada da shanu, tumaki, zuwa awaki. Wannan lamari dai na kai hare-haren wuce gona da irin na cigaba da afkuwa a wannan yanki duk da kokarin da gammayar jami’an tsaro suka ce suna yi ba dare ba rana, wanda haka tasa gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya shirya wani taron gaggawa domin ganin an shawo kan wannan matsala.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: