Connect with us

RAHOTANNI

Rikicin Tibi Da Jukun: Buhari Ya Yi Mamakin Yadda ‘Yan Uwa Ke Kashe Junansu

Published

on

Shugaba Nuhammadu Buhari ya ce, ya girgiza da halin dabbancin da wasu ke nunawa inda suke iya kasha ‘yan’uwansu.

Buhari yana yin wannan maganar ne a kan rikicin Tibi da Jukkunawa, inda ya nemi gwamnarocin Jihohin Benuwe da Taraba da kuma al’ummominsu da su sa hankali su kai zuciya nesa a sakamkon kisan da aka yi wa David Tanko, wani Limamin Kirista na Cocin Katolika da ke kauyan, Kpankufu,Wukari, Taraba.

Shugaban kasan ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Juma’a.

Wasu ‘yan bindiga ne ake zargin sun yi wa Malamin kwanton bauana suka kashe shi a lokacin da yake a kan hanyarsa ta zuwa tattaunawa a wani taron sulhu da sauran malamai.

Shugaban kasan ya nemi gwamnonin Jihohin da masu ruwa da tsaki da suka hada da Sarakunan Tor Tib, Aku Uka na Wukari, malaman addini da shugabannin al’ummomi da su yi wani taro a cikin hanzari domin kawo karshen rikicin na tsakanin al’ummun.

Ya ce gwamnatin tarayya ba za ta kame hannunta tana kallon ana shuka gaba a tsakanin al’ummar ta Tib da kuma Jukkunawa ba.

“A madadin gwamnatin tarayya da daukacin al’ummar kasar nan, ina mika ta’aziyyata ga ‘yan Cocin Katolika, gwamnati da al’ummar Jihar Taraba a kan wannan rahin da aka yi.

“Cigaba da kasha-kashe da lalata dukiyoyi da al’ummun da bas a ga maciji da junan suke yi  abin kunya ne, ya kuma sabawa dabi’ar zamantakewa ta kabilu da addinai na kasar nan.

“Ba za a samu ci gaba ba tare da yamutsi, matukar muka bari lalata dukiyoyi ya karfafa a cikin al’ummun mu.

A cewar shugaban kasan, rikicin na tsakanin Tiv da Jukun yana daya daga cikin dadadden rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa a Nijeriya, wanda kuma yake haifar da matsalar tsaro sosai. “Lokaci ya yi da ya kamata shugabannin kabilun su zauna tare domin su tsara yanda za a samar da zaman lafiya.

Shugaban kasan ya ce, taimako daga gwamnatin tarayya ya hada ne da shugabannin addinai, shugabannin al’umma da manyan jami’an tsaro a karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Ya ce, tawagar sa hannun za ta yi nazarin duk wasu rikicerikice da nufin neman hanyar karshe ta warware su.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: