Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din “Gidan Kudi”

Published

on

Suna: Gidan Kudi

Tsara labari: Abdullahi Amdaz

Kamfani: Sadiq Movies Tone

Shiryawa: Sunusi Sajjad

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Bada Umarni: Sunusi Oscar 442

Jarumai: Ali Nuhu, Ramadan Booth, Garzali Miko, Maryam CTB, Ibrahim Shehu, Natu Niger, Abdul Buba, Danjuma Salisu, Rukayya Sharada da sauransu.

Fim din“Gidan Kudi” fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani matashi mai suna Yaseer (Ramadan Booth), wanda ya kasance mara mutunci a cikin makaranta, saboda kudi da kuma alfarmar da mahaifinsa ko kawunsa ya ke da ita. A farkon fim dinan nuno Yaseer ya danno cikin makaranta a guje a cikin mota in da ya na tsayawa a ka ga ya fito a cikin motar ya zo kawai ya rufe wani dalibi da mari, ya na ta marun shi amma saboda tsoro ba a iya samun wani mutum daya a wajen da ya je domin hana shi ba.

Mugun halin Yaseer ya sa kowa tsoronsa ya ke a cikin makarantarsu. Kodayaushe ya na tafiya ne da ayarin abokansa wadanda su ke bin umarninsa a kodayaushe. Saboda rashin mutuncin Yaseer, har bindiga ya ke yawo da ita da niyar zai harbi duk wani da ya yi niyar shiga gonarsa.

Yaseer bai fara fuskantar matsala ba sai a lokacin da ‘yan sanda su ka zo su na tuhumarsa a kan kisan wata budurwarsa mai suna Baby. Sai dai a karshen binciken jami’an tsaro sun gano cewa Yaseer ba shi ne ya kashe baby dinba. Sai dai zargin ya koma kan kawunsa Alhaji wato (Ali Nuhu), amma shi ma har karshen fim dinba a nuna cewa tabbas shi ne ya kashe ta ba.

ABUBUWAN YABAWA

  1. An samu sauti mai kyau musamman daga tsakiyar fim dinzuwa karshensa.
  2. Hotuna sun dauku radau.
  3. Jaruman sun yi kokari a rawar da su ka taka a cikin fim din.

KURAKURAI

  1. Labarin fim din ya na da wahalar fahimta kwarai da gaske.
  2. Fim dinya yanke ba tare da bayyanawa mai kallo cikakken sakon da ya ke so mai kallon ya fahimta ba.
  3. An samu sabawar sautin furuci da kuma motsawar baki daga farko zuwa tsakiyar fim din.
  4. Ansamu maimaituwar fitowar da a ka nuno abokan Yaseer su na tattaunawa a kan dabi’unsa.
  5. Ya na da kyau a ce an bayyanawa mai kallo wa ce ce Baby, me ya sa a ka kashe ta, yaushe a ka kashe ta, wa ne ne ya kashe ta, amma a Acikin fim dingaba daya babu amsar wadannan tambayoyin.
  6. Me ne ne alakar Yaseer da Alhaji?
  7. An samu tafka da warwara a jerin wasu kalamai.

KARKAREWA

Fim din“Gidan Kudi” fim ne mai dauke da sarkakken sako. Domin sakon zai matukar wahalar da mai kallo. Fim dinsam bai bayyanawa mai kallo sakon da ya ke so ya fahimta ba. Ya kamata a bayyanawa masu kallo wa ne ne Yaseer, me ne ne abunda ya sa ya ke wulakanta mutane, sannan ya kamata a ce ya yi nadamar irin abubuwan da ya aikata. Kuma an nuna a na bincike a kan kisan baby, amma kuma ba a nuna mai karshen binciken ya samar ba. Sannan ba a bayyana makasudinkisan nata ba, da kuma wa ne ne ya kashe ta ba. A gaskiya kalubalen da fim din“Gidan Kudi” ya samu ya fi nasarorin da ya samu yawa a gurun masu kallo.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!