Connect with us

WASANNI

Smalling Ya Koma Roma                                                                    

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Chris Smalling, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Roma dake kasar Italiya a matsayin aro na tsawon shekara daya kamar yadda kociyan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer ya tabbatar.

Smalling dai ya rasa wajen buga wasa ne a Manchester United tun bayan komawar dan wasa Harry Maguire ya koma kungiyar a watan daya gabata wanda hakan yasa dan wasan ya yanke shawarar barin kungiyar domin komawa inda zai dinga buga wasa.

Tuni dai Manchester United ta tabbatar da barin dan wasan kungiyar ta bakin kociyan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer, wanda yace tuni Smalling ya sauka a kasar Italiya kuma an gama kulla duk wata yarjejeniya.

Roma dai ta dauki aron dan wasa Samlling ne domin maye gurbin dan wasa Kostal Manolas wanda yabar kungiyar ya koma kungiyar kwallon kafa ta Napoli wadda itama take buga gasar Siriya A ta kasar Italiya.

Kociyan na Manchester United ya ce akwai bukatar dan wasan yabar kungiyar domin bazai samu damar buga wasanni ba akai-akai a wannan kakar kuma dan wasan bayason cigaba da zaman benci a cewar Solkjaer

Smalling ya koma Manchester United ne daga kungiyar kwallon kafa ta Fulham dake kasar Ingila a shekara ta 2010 inda kuma ya lashe kofuna takwas ciki har da gasar firimiya guda biyu da gasar Europa da kuma gasar cin kofin kalubale guda daya Smalling yabi sahun manya manyan ‘yan wasan da suka bar Manchester United a wannan kakar da suka hada da Ander Herrera da Rumelu Lukaku da Alexis Sanchez sannan kuma ana ganin dan wasa Matteo Darmian shima zai bar kungiyar kafin gobe Litinin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: