Connect with us

MAKALAR YAU

Cikar Dr. Dauda Shekara 54: Darussa Daga Rayuwar Gamjin Gusau

Published

on

Yau babbar rana ce ga al’ummar Jihar Zamfara, rana ce da a ka haifi gwarzo, mutumin da ke samun jin dadi da natsuwa yayin da yake taimakon al’umma, wanda babban burinsa shi ne ya ga bunkasar jiharsa ta kowanne fanni.

A nawa hangen, babu wata burgewa a bukin murnar zagayowar ranar haihuwa, sai dai idan wanda za a yi wa bukin murnar ya yi wani abin kirki ga al’umma. Misali, ya zama mutum ne wanda ya ke ko ta ke yin hidima ga al’umma ba tare da tsammanin wani tukuici ba. Irin wadannan bukukuwan ranar haihuwa ne ya cancanta a yi murna da zuwansu, ko don wasu su yi koyi da kyawawan halayen masu wannan hali.
Irin wadannan halaye sun yi daidai da na Dakta Dauda Lawal Dare (Gamjin Gusau), wanda aka haife shi a ranar 2 ga watan Satumbar 1965. Dauda ya fito ne daga gidan mutanen kirki da dattako a Jihar Zamfara. Saboda dattakonsa da sanin darajar dan adam ya sa sunansa ya shahara a tsakanin mutanen Jihar. Masani ne, kuma kwararre a fannonin da suka shafi harkar banki, tattalin arziki da siyasa.

Dakta Dauda Lawal ya na da kwarewa ta sama da shekara 25 a fannin aikin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Ya samu wadataccen ilimi, domin kuwa ya samu shaidar kamala digirin farko a kan kimiyyar siyasa da kuma digirinsa na biyu a kan kimiyyar siyasa da mu’amalar kasashen duniya duk a mashahuriyar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Daga bisani ya bar Nijeriya inda ya yi kwasa-kwasai a manyan makarantun duniya irinsu; London School of Economics, Habard Business School da kuma Oxford University Business School da dai sauransu.

Dakta Dauda ya fara aiki a matsayin Jami’in kula da harkar siyasa a tsohuwar MAMSER, ya samu lambar yabon girmamawa ta (Dr.) daga Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato. Ya rike mukamin mataimakin manaja na kamfanin Wested Nigeria Ltd daga 1989 zuwa 1992. Ya fara aiki a matsayin jami’i na musamman a ofishin jakadancin Nijeriya da ke Washington daga shekarar 1994 zuwa 2003. Daga nan ne ya koma aiki da shahararren bankin ‘First Bank’, ya kuma ajiye aiki a shekarar 2017 a matsayin Babban Darakta na shiyyar mu’amala da jama’a.

Tabbas ya zuwa yanzu, al’ummar Jihar Zamfara sun iya fahimtar cewa Gamjin Gusau, Dakta Dauda Lawal Dare ba kawai dan siyasa ba ne, a’a jigo ne da ke kumshe da kishin jihar Zamfara a zuciyarsa. Wannan kuwa bisa la’akari da irin hidindimun da yake yi wa Jihar domin ganin ta bunkasa, ta daukaka, sannan kuma al’ummar cikinta sun amfana.

Ba kawai jihar Zamfara ba, gabadaya Nijeriya shaida ce kan wani gagarumin aiki da Gamjin Gusau, Dakta Dauda ya yi a Zamfara, wanda gwamnan Jihar Bello Matawalle ya kaddamar a ranar 15 ga watan Yunin shekarar nan ta 2019.

Ayyukan raya kasa ne wanda sai an tona cikin masu hali kafin a samu wanda zai iya yin irin wadannan ayyuka da Dauda yayi. Wasu suna da dukiya da wadatar da ta fi ta Dauda, amma ba su da zuciyar hidimtawa al’ummarsu kamar yadda yake da ita. Tarihin da Dakta Dauda ya kafa a ranar 15 ga watan Yunin 2019 wani abu ne da za a jima a na bitarsa, ana sanya mishi albarka tare da  jinjinawa ta musamman.

Me wannan bawan Allah ya yi haka da har ta sa ko ina cikin Jihar Zamfara albarka a ke sa mishi? Ba kawai talakawa ne ke sambarka da Dauda ba, hatta gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle sai da ya yi mishi jinjina ta musamman tare da yin kira ga sauran masu hannu da shuni na Jihar Zamfara da su yi koyi da kyawawan halayensa.

Gabadaya rahotannin jaridu sun nakalto cewa, gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed (Matawallen Maradun) ya jinjinawa Dakta Dauda Lawal Dare (Gamjin Gusau) a bisa namijin kokarinsa na samar da wasu muhimman ayyukan inganta ilmi a Jihar Zamfara.

Gwamna Bello Matawalle da kansa ya kaddamar da ayyukan gine-gine da titin Mota da Dakta Dauda Lawal ya aiwatar a Makarantun Jinya da Unguwar Zoma da ke Gusau, da Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, da kuma Kwalejin kiwon lafiya da kimiya da ke Tsafe.

A Makarantar koyon Jinya da Unguwar Zoma, Dakta Dauda Lawal ya gina masu manyan gidajen kwanan dalibai guda biyu domin amfanin dalibai Maza da Mata. Dakunan kwanan sun kunshi bangarori guda hudu a tsarin ginin sama da kasa.
Kowane bangaren yana da dakunan kwana Takwas.

Kowane daki kuma an sanya mai gadaje hurhudu masu daukar daliba biyu (wato dalibai Takwas kenan a kowane daki. Kuma an gina wurin wanka da bahaya a ko wane daki. Haka kuma kowace Mace Takwas suna da dakin dafuwar abinci tare da Kantar ajiyar kayan abinci.

Sannan kuma dakunan wurin kwanan dalibai Mata dari Biyu da Hamsin da Shidda ne.a bangaren Maza dalibai Dari da Ashirin da Takwas ne za su amfana da wurin kwanan. Kafin samarda wannan alheri daga Dr. Dauda Lawal wanda aka kammala tun a shekarar bara dalibai Hamsin (50) Maza da Mata ne kawai ke samun wurin kwana a Makarantar.

A kwalejin kiwon lafiya da kimiya ta Tsafe kuwa, Dakta lawal Dare ya gina azuzuwa Tara kowanne dauke da duk kan kujerun su da tebura da duk abubuwan da ake sanya ma azuzuwan karatu ya sa yashi.

A Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau kuwa, Titi ya yi masu mai tsawon kilomita biyu da rabi. Wannan ne dalilin da ya sa Gwamna Matawale ya jinjinawa Dakta Dauda Lawal. A yanzu irin wadannan mutane masu kishin al’umma Jihar Zamfara take bukata.

A cikin watan da ta gabata ne Dakta Dauda Lawal tare da wasu kamfanonin hadin gwiwa suka ziyarci Jihar Zamfara inda suka duba filin da za a fara ginin tashar jirgin sama na zamani. Irin wannan namijin kokari da Dakta Dauda ke yi wa Jihar Zamfara, da kokarin ganin ya taimakawa gwamnatin Jiha don ta yi nasara, abin a yaba ne, a kuma jinjinawa Gamjin Gusau. Lallai Zamfara ta yi sa’ar samun Da mai kishinta.

Barka da cika shekaru 54, Gamjin Gusau. Allah Ya karo shekaru masu albarka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!