Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Imo: Dan Giya Ya Kashe Matarsa Har Lahira

Published

on

Mazauna kauyen Umuoduku da ke garin Oboama Autonomous cikin karamar hukumar EzinihitteMbaise ta Jihar Imo, sun fada cikin rudani lokacin da wani mashayin giya mai suna  Richard Anochirionye, wanda a ke yi wa lakabi da  ‘Okpoka’ ya buge matarsa har lahira da katako.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, “sai da mutumin ya tabbatar da yaransa sun fita daga cikin gidan. Inda ya aiki diyarsa ta sayo masa wani abu, kafin ta dawo ya buge matar har lahira,” in ji wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a sakaye sunansa.

Majiyarmu ta kara da cewa, a cikin watan Yulin shekarar 2017, wannan mutumi mai suna Okpoka, ya sayo lita 25 na fetur inda ya kone gidan gadonsu kurmus, sakamakon yaransa sun sayar masa da baburansa ba tare da izinin sa ba. A cewar mazauna yankin Oboama, sun ce gidan nasu ya na da bangare biyu, daya bangaren ya na da daki biyar, yayin da daya bangaren ya na da daki uku, sannan gidan ya na kusa da filin wasa na karamar hukumar Ezinihitte Mbaise.

Wakilinmu ya ruwaito mana cewa, kafin mashayin ya kone gidan, sai da ya zagaye kauyen ya na sanar wa cewa, duk wani wanda ya ke iya fada wa yaransa magana, to ya fada mu su su dawo masa da baburansa guda biyu ko kuma ya daki matakin da sai an buga a jarida.

“Ya kuma tuntubi sarakunan da masu unguwar garin a kan lamarin, idan yaransa ba su dawo masa da baburansa wanda ya ke kasuwanci da su, zai dauki mummunar mataki wanda ba za su taba mantawa da shi ba har zuwa karshen rayuwarsu,” in ji majiyarmu.

An bayyana cewa, lokacin da Okpoka ya saka wuta a gidan a shekarar 2017, ya yi gudun hijira a wannan gari. Bayan da yaran su ka kara gina wani gidan, sai ya dawo, inda a yanzu ya kashe matar da katako har lahira.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, lokacin da yarinyarsa ta dawo daga aiken da ya yi mata, sai ta ga gawar mahaifiyarta, inda nan take ta sanar wa mutanen kauyen tare da damke wanda a ke zargin, sannan a ka mika shi ga ‘yan sanda. Shi dai Okpoka tsohon dan acaba ne, inda daga baya ya zama mai yin giya, inda ya bayyana cewa, ya shiga cikin ukuba tun lokacin da a ka raba shi da baburansa.

A halin yanzu dai, an ijiye gawar matar a wani asibiti da ke makwabtaka da garin mai suna Ibeku cikin karamar hukumar Aboh-Mbaise ta jihar. Lokacin da wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Imo, Orlando Ikokwu, ya bayyana cewa zai tuntubi DPO na karamar hukumar Ezinihitte, domin ya samu cikakken bayani a kan lamarin, sannan zai tuntubi wakilinmu.

Amma har zuwa lokacin da a ke hada wannan rahoto, Mista Ikokwu bai sake tuntubar wakilinmu ba, inda bai dauki wayar da wakinlinmu ya buga masa, sannan kuma bai maido da sakon karta kwana ba da wakilinmu ya tura masa a waya ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: