Connect with us

RIGAR 'YANCI

KCCI Ta Karrama Ministocin Kano Biyu

Published

on

  • Cin Zarafin Manya A Radiyo Na Nuna Rashin Shugabancin Kano – Nanono
  • A Soke Mu, A Bar Buhari Ya Huta Haka – Magashi
  • Kada A Cika Ministocin Kano Da Yawan Shawarwari Ko Bukata – Sheikh Khalil

A  Ranar Asabar din da ta gabata ne, Kungiyar Masu Kishin Jihar Kano da Ci-gabanta, wato KCCI ta shirya wani gagarumin taron karrama Ministocin na Kano guda biyu, Ministan Aikin Gona da Albarkatun Kasa na Nijeriya, Alhaji Sabo Nanono da kuma sabon Ministan Tsaron Nijeriya, Alhaji (Janar) Bashir Salihi Magashi, tare da ba su shawarwari domin ci-gaban Kano ta kowane irin fanni karkashin Shugabancin Alhaji Bashir Tofa, Shugaban KCCI na Kano. Kazalika, dukkanin Ministocin sun tofa albarkacin bakinsu a wajen wannan muhimmin taro.

A nasa jawabin, Ministan Aikin Gona, Alhaji Sabo Nanono, ya yi matukar nuna takaicinsa bisa yawan habaice-habaice da zage-zage da ake yi a kafafen yada labarai na Kano, musamman ta fuskar muhimman mutane da ya hada da Mai girma Gwamnan Kano, Mai Martaba Sarki da manyamanyan Malama da ma sauran al’umma baki daya da sunan Siyasa. Ko shakka babu, wannan na nuna cewa, babu Shugabanci a Kano, sannan ya zama wajibi a yi kokarin kawo karshen wannan al’amari ta hanyar kawo kawo gyara a fadin Jihar baki daya.
Haka zalika, ya ci gaba da bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya na da damar taimakawa a kan dukkanin abin da ya shafi al’umma. Don haka, duk wani wanda ya ce ko ke ikrarin cewa, Gwamnatin Tarayya ba za ta iya taimakawa  a kan abin day a shafi ci-gaban al’umma ba, karya yake yi, in ji Ministan.

Shi ma a nasa jawabin, Ministan Tsaron Nijeriya, Janar Bashir Salihi Magashi, ya bayyana cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi wa Jihar Kano komai a halin yanzu, sakamakon Ministoci guda biyu da ya ba su. Don haka, yanzu lokaci ya yi da ya kamata a kyale Shugaban Kasan ya huta, musamman ta fuskar shan suka da kuma kushe a wannan Jihar ta Kano, duk abin da aka gani ba dai dai ba a Kano, laifinmu ne ba na Shugaba Buhari ba.

Har ila yau, Magashi ya kara da cewa, tasa kofar a bude take wajen karbar shawarwari daga daidaikon mutane ko kuma rukunin jama’a, duk da ya san cewa, ba zai taba iya biya wa mutanen Kano baki dayansu bukatarsu ba, duk kuwa da ganin yadda ake nuna musu soyayya da kauna. Sannan ya bukaci al’ummar Jihar Kanon baki daya, da su taya su da addu’a don ganin sun samu damar sauke nauyin day a rataya a kawunansu.

Har wa yau, shi ma Sheik Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Kasa, reshen Jihar Kano, ya yi jan hankali tare da yin kira cewa, ka da a damu wadannan sabbin Ministoci da shawarwari barkatai ko yawan neman bukata ta kashin kai, domin kuwa kowane mutum yana da nasa ra’ayin da kuma masu ba shi shawarwari.

Sabo da haka, idan aka yi dace da masu ba shi shawarwari na gari, to kuwa za a ga aiki na gari, idan kuma aka yi rashin dace da samun akasin haka, akasin hakan za a gani. Daga nan ne kuma, sai ya yaba wa Kungiyar KCCI bisa shirya wannan taron karramawa ga wadannan sabbin Ministoci guda biyu da aka samu a wannan Jiha ta Kano, wato Alhaji Sabo Nanono da kuma Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya.

Har ila yau, Shugaban Kungiyar na KCCI (Kano Concerned Citizens Initiatibe), Alhaji Bashir Usman Tofa, ya bayyana dalilai masu tarin yawa a kan shirya wannan walima da addu’o’i da kuma godiya ga Allah Madaukakin Sarki, da ya azurta Jihar Kano da wannan gagarumar dama.

Kadan daga cikin dalilan su ne, tabbatar wa da wadannan sabbin Shugabanni cewa, Kano da mutanen cikinta na tare da su, sannan kuma su na sanya idanu a kansu da kuma sauraron irin dimbin alhairin da za su kawo ma ta na cigaba, in ji Tofa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: