Connect with us

RIGAR 'YANCI

Leah Sharibu Na Nan Da Ranta – Shugaban Kasa

Published

on

A ranar Asabar ce, fadar Shugaban kasa ta baiwa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa yarinyar nan, Leah Sharibu, ta makarantar Sakandaren ‘yan mata da ke Dapchi, wacce ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace a watan Fabrairu, 2018, tana nan da ranta.

Fadar ta kuma ce ba ta saurara ba a kan kokarin da take yi na ganin ta ‘yanto ta domin ta komo a cikin iyalanta a kowane lokaci daga yanzun.

Babban mai taimakawa Shugaban kasa a kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa, gwamnatin Buhari ba za ta sarara ba har sai ta ga ta ‘yanto Leah Sharibu.

“A maimakin mu sarara, gwamnatin tana ci gaba ne da bin hanyoyin da suka kamata wadanda ake sa ran za su haifar da da mai ido na ganin wadanda suke rike da ita sun sako ta.” Shehu yana fadin hakan ne a bayan tsoron da wasu ke nunawa kan lafiyarta.

Ya ce, yawancin abin da ake yadawa a kafafen yada labarai a kanta duk karya ne. A cewar shi, “Har yanzun kafofin sadarwa da wadanda suka kama ta a bude suke, domin tabbatar da an sako Leah Sharibu.

“Sabanin rahotannin karya, tana nan da ranta, muna da tabbacin hakkan daga hukumomin tsaronmu, gwamnati kuma tana yin aiki tukuru domin ganin an sako ta, har ma da sauran tsararrun su komo zuwa ga iyalansu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!