Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Neja: Makiyayi Ya Gurfana A Kotu Bisa Kashe Manomi

Published

on

A ranar Juma’a ce, wani makiyayi mai suna Mohammed Bello, ya gurfana a gaban wata kotu da ke garin Minna, bisa laifin kashe wani manomi, inda zai cigaba da zama a gidan yari har sai an samu shawarwari daga ma’aikatar shari’a ta jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, alkali mai shari’a Mariam Kingas ta yi watsi da duk wata hujja da wanda a ke tuhuma ya bayar. Kings ta bai wa ‘yan sanda umurnin mika fayal din karar ga ma’aikatar shari’a ta jihar.

Ta dage sauraron wannan kara har sai ranar 26 ga watan Satumba. Tun da farko dai, lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara Sufeta Aliyu Yakubu, ya bayyana cewa, ana tuhumar Bello da laifuka guda uku wadanda su ka hada da laifin shiga gonar mutum ba tare da izini ba, fasadi da kuma laifin kisan kai, wanda sun saba wa sashe na 348, 327 da 222 na dokar fanal kot.

Yakubu ya bayyana cewa, an samu nasarar damke wanda a ke tuhuma ne a kauyen Rubochi da ke cikin karamar hukumar Lapai, a ranar 2 ga watan Agusta.

Ya kara da cewa, wanda a ke tuhuma ya tura dabbobinsa zuwa cikin gonar wani mutum mai suna Haruna Mohammed, inda su ka cinye ma sa amfanin gonarsa.

A cewarsa, lokacin da mutumin ya yi masa gargadi, sai Bello ya cire addarsa ya sari Mohammed, inda jini ya yi ta zuwa daga baya ya ce, ga garinku nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: