Connect with us

RA'AYINMU

Samun Tsaiko Kan Gabatar Da Sabon Tsarin Albashi

Published

on

Fiye da wata uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan dokar mafi karancin albashi na ma’aikatan kasar nan, amma har yanzu ma’aikatan ba su fara dandana wannan karin ba. Idan za mu iya tunawa, an bayyana sabon karancin albasjin ne a ranar 18 ga watan Afrilun shekarar 2019, bayan da a ka shafe kusan shekaru uku ana tattaunawa tsakaanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadugo da kuma kamfanoni masu zaman kansu. Kungiyar kwadugo na Nijeriya (NLC) da kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) su su ka jagoranci ma’aikatan, yayin da a bangaran gwamnati kuma jami’ai daga gwamnatin tarayya da na jiha su ka jagoranci tattaunawar.

A ranar 14 ga watan Mayu ne, gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamiti a karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan kasar nan, Misis Winifred Oyo-Ita, wanda za su tattauna a kan dai-daita mafi karancin albashin a dukkan kasa baki daya. Da ya ke kaddamar da kwamitin, sakataran gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha, wanda shi ne shugaban wannan kwamitin ya bayyana cewa, an bai wa wannan kwamiti mako hudu da su kammala aikinsu, wanda za su fara gudanar da aiki a ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2019.

Makwanni hudun sun shude amma kwamitin bai bayyana wani rahoto ba. An dai samu rashin jituwa a tsakanin mambobin wannan kwamiti a kan kari ga ma’aikata, sakamakon dai-daita tsarin sabon karancin albashin. Wanda ya ke da tsarin aiwatarwa. Tun da farko dai, gwamnatin tarayya ta nemi ta kara wa ma’aikata kudi na naira 10,000 ga dukkan ma’aikatan tun daga mai daraja ta daya har zuwa mai mataki na 17 a ranar 11 ga watan Satumba. Duk da haka dai, daga baya gwamnatin ta nace a kan za ta kyara wa ma’aikata albashi kashi 9.5 tun daga kan 07-14, sai kuma sauran kashi biyar din daga 15-17.

A bangaranta kuma, kungiyar kwadugo ta nace kan kashi 30 daga 07-14, yayin da kashi 25 daga 15-17. Wannan rashin jituwa shi ya sa a ka dakatar da wannan kwamitin har sai mama ta gani.     A ra’ayinmu mu na ganin cewa, ya kamata gwamnati ta duba irin wahalhalu da ma’aikata su ke ciki. Ita gwamnati ta na ga cewa, idan a ka kara wa kashi 30 na ma’aikata albashin da su ke bukata, manyen ma’aikatan za su sami karin kudi na naira 100,000, saboda an kara wa kananan ma’aikata mafi karancin albashi na naira 30,000.

A bangaran kungiyar kwadugo kuma, su na ga a kan karin da su ke tattaunawa da gwamnati na karawa ma’aikata albashi tun daga mataki na bakwai har zuwa na takwas za su samu karin naira 5,000 kasa da naira 16,000 abinda kungiyar kwadugo ta ke bukata.

Ya na da matukar muhimmanci mu bayyana cewa, tattanawa na sabon tsarin mafi karanci albashi ya yi tsanani, kuma ya na kawo tsaiko wajen rattabawa dokar hannu, sannan ya sa an samu karin farashin kayayyakinabinci, haya da kuma sauran kayayyaki na yau da kullum.

A ra’ayinmu tsaikon da a ka samu na fara gudanar da sabon tsarin mafi karancin albashi, ya haddasa matsaloli ga ma’aikata wanda su ke ganin tsarin zai fidda su daga talaucin da su ke ciki. Ya na da muhimmanci mu san da cewa, sabon tsarin mafi karancin albashi ya fara aiki a hukumance tun ranar 18 ga watan Afrilun shekarar 2019, lokacin da shugaban kasa ya rattaba hannu a kan dokar. Wannan ya na nuna cewa, ita gwamnati ta kara wa ma’aikata bashi.

Duk inda tattaunawa ta yi tsawo wajen aiwatar da tsarin kara albashin, to sai an samu karin manyen basussuka a bangaran gwamnati. Akwai bukatar a aiwatar da tsarin cikin gaggawa, saboda ya na kawo tsaiko ga masana’antu. Ma’aikata na bukatar fara neman a biya su basussukan da su ke bi, ga kuma wasu na kara karuwa. Ya na kawo matsaloli masu yawa ta harkokin gwamnati da kuma rushe tattalin arziki gaba daya.

Mu na fatan dukkan bangarorin guda biyu da ke tattaunawa su kasance an samu masalaha ta yadda ma’aikatan za su fara jin dadin sabon tsarin biyan mafi karancin albashin. A wannan jarida, mu na bayar da shawar da a aiwatai da tsarin mafi karancin albashi, saboda kar masu gidaje da kuma sauran ‘yan kasuwa su yi awon gaba da duk abinda ma’aikaci ya samu
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: