Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Shida Sun Mutu, 24 Sun Jikkata A Hatsarin Hanyar Legas Zuwa Ibadan

Published

on

A wani hatsarin mota wanda ya afku ranar Juma’a a Jihar Ogun, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida, yayin da mutum 24 su ka samu mummunar rauni.

Hukumar kiyaye hadararruka ta Jihar Ogun, ta bayyana cewa, hatsarin ya faru ne a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan kusa da yankin Isara da ke garin Ogun.

A cewar hukumar kiyaye hadararruka ta Jihar Ogun, hatsarin ya rutsa da motocin bas na haya guda biyu wadanda su ka yi karo da juna. Hatsarin ta rutsa da mutanen guda 30, wadanda su ka hada da maza guda 19 da mata guda tara, sai kuma kananan yara guda biyu na miji da mace.

An bayyana cewa, hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida, wadanda su ka hada da maza uku mata uku.

A cikin bayanin da jami’in ilmantar da jama’a na hukumar kiyaye hadararruka ta Jihar Ogun, Florence Okpe, ya rattabawa hannu, ya bayyana cewa, wata farar motar bas kirar Toyota mai lamba kamar haka ABC 932 DJ, ta yi karo da wata farar motar bas kirar Mazda mai lamba kamar haka FST 820 DD.

Okpe ya ce, “hatsarin ya faru ne sakamakon mummunar gudu da kuma tukin ganganci, lokacin da motar bas kirar Mazda wanda ta taso daga garin Legas,

inda ta bar hannunta sannan ta bugi motar bas kirar Toyota wanda ta taso tun daga garin Abuja.” An bayyana cewa, an garzaya da wadanda su ka samu raunika asibiti na kusa da wurin da lamarin ya afku, yayin da a ka kai gawarwakin da su ka mutu zuwa dakin ijiye gawarwaki a asibiti.

“An kwantar da mutum 11 wadanda hatsarin ya rutsa da su a asibitin Bictoriy Hospital Ogere, sannan a ka kwantar da mutum shida a asibitin koyarwa na jami’ar Olabisi Onabanjo da ke Sagamu.

An kwantar da mutum bakwai a asibitin Idera da ke garin Sagamu, domin yin jinya. “Gawarwakin fasinjoji guda shida wadanda su ka mutu an ijiye su a dakin ijiye gawarwakui da ke asibitin koyarwa na  Olabisi Onabanjo cikin garin Sagamu da kuma asibitin Ipara.

“Kwamandar hukumar kiyaye hadararruka ta Jihar Ogun, Clement Oladele, ya yi wa iyalan mamatan ta’aziyya tare da yin addu’a Allah ya baiwa wadanda su ka samu raunika sauki.

“Ya bayyana wa mutane cewa, za a iya tuntubar hukumar a yankin Ogere ko kuma a Ogunmakin domin a samu cikakken bayani a kan hatsarin.

Sannan za a iya tuntubar hukumomin lafiya domin karin bayani a kan hatsarin,” in ji Okpe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!