Connect with us

WASANNI

’Yan Mowa Da ’Yan Bora A Rukunin Kofin Zakarun Turai!

Published

on

A ranar Alhamis hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai ta fitar da jadawalin rukunin kungiyoyi da kuma yadda za’a fara buga gasar ta cin kofin zakarun turai ta wannan shekarar a birnin Monaco na kasar Faransa.

Mai rike da kofin Zakarun Turai Liverpool tana rukunin da ya kunshi kungiyoyin Napoli da Salszburg da kuma Genk a gasar Champions League ta bana sai kuma Manchester City tana rukuni da ya hada da Shakhtar Donetsk da Dinamo Zagreb da kuma Atalanta.

Tottenham wadda ta yi rashin nasara a hannun Liverpool a wasan karshe an hada ta da Bayern Munich da Olympiakos da kuma Red Star Belgrade ita kuwa Chelsea ta na rukuni daya ne da Ajax da Balencia da kuma Lille.

Paris St-Germain da Real Madrid su na rukunin farko, ita kuwa Barcelona da Borussia Dortmund da kuma Inter Milan za su fafata ne a rukuni na shida kamar yadda  aka fitar da jadawalin a ranar Alhamis din.

Masu hasashe dai tuni su ka bayyana cewa kungiyoyi irinsu Liverpool da Juventus da Manchester City da kuma Real Madrid su ne a ke saran zasu iya lashe gasar ta bana duk da cewa akwai irinsu Inter Milan da Bayern Munchen da kuma Chelsea.

Ga yadda aka raba jadawalin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League ta ban:

Rukunin farko: Paris St-Germain da Real Madrid da Club Bruges da kuma Galatasaray

Rukuni na biyu: Bayern Munich da Tottenham da Olympiakos da kuma Red Star Belgrade

Rukuni na uku: Manchester City da Shakhtar Donetsk da Dinamo Zagreb da kuma Atalanta

Rukuni na hudu: Juventus da Atletico Madrid da Bayer Leberkusen da kuma Lokomotib Moscow

Rukuni na biyar: Liverpool da Napoli da Salzburg da kuma Genk

Rukuni na shida: Barcelona da Borussia Dortmund da Inter Milan da kuma Slabia Prague

Rukuni na bakwai: Zenit St Petersburg da Benfica da Lyon da kuma RB Leipzig

Rukuni na takwas: Chelsea da Ajax da Balencia da kuma Lille

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fito a cikin rukuni mai wahala rukunin daya hada kungiyoyin Borussia Dortmund da Inter Milan da kuma kungiyar kwallon kafa ta Slabia Prague ta kasar Bulgeriya kuma masana sun bayyana cewa rukunin ya na daya daga cikin rukunu mafi wahala a gasar ta bana.

Sai dai wasu suna ganin Manchester City, wadda itace zakarar gasar firimiya ta shekarar data gabata zata fito daga cikin rukuni cikin sauki bayan da aka hada tad a kungiyoyin Shakhtar Donesk ta kasar Turtkiyya sai kuma Dinamo Zegren ta Crotia da kuma kungiyar kwallon kafa ta Atlanta wadda ta fito daga kasar Italiya.

Duk da haka wasu masu koyarwar da kuma ‘yan wasa za su yi farin ciki da yadda aka fitar da jadawalin yayinda kuma wasu basuji dadin yadda rabon ya kasance ba musamman yadda suka fito acikin rukuni mai wahala.

Wasu daga cikin kungiyoyin da za’ace rabon yayi musu daidai su ne kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, wanda acikin shekaru uku da akayi ana buga gasar duk shekara sai Manchester City da Shakhtar sun hadu sai dai a shekarar da ta gabata Manchester City ta yi ragaraga da Shakhtar din daci 9-0 har gida. Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a wannan karon za’a iya cewa ta samu rukuni mai sauki bayan ta fito acikin rukunin daya hada da kungiyoyin Napoli da Selsburg da kuma kungiyar kwallon kafa ta Genk.

A kakar wasan data gabata dai an hadu acikin rukuni tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Napoli inda Napoli ta lallasa zakarun na turai daci 2-0 a wasan da suka fafata a kasar Italiya. Shima dan wasa Cristiano Ronaldo za’a iya cewa ya samu damar lashe wannan kofin a kungiyar ta Juventus bayan da har yanzu kungiyar ta kasar Italiya take neman hanyar da zata lashe kofin a karo na uku saboda rabonta da kofin na zakarun turai tun a shekara ta 1996.

Sababbin ‘yan wasan kungiyar da suka hada da Matthijs De Ligt da Aaron Ramsey da Adrein Rabbiot da kuma ragowar ‘yan wasan kungiyar suna da kwarewar da zasu sanya kungiyar ta samu nasarar lashe wannan gasa wadda za’a fara a tsakiyar wannan watan.

Akwai Matsala A Barcelona Sai dai za’a iya cewa a wannan kakar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona bata samu damar da take samu ba duk shekara bayan data tsinci kanta acikin rukunin daya hada da kungiyoyin Inter Milan, wadda ta kashe kudi a wannan kakar wajen sayan ‘yan wasa irinsu Lukaku da kuma kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund da kuma Slabia Prague Itama kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, zata kwashin kashinta a hannu a wannan kakar bayan data fito acikin rukunin daya hada da kungiyoyin Ajax da Balencia ta kasar Sipaniya sai kuma Lille ta Faransa.

Chelsea dai bata sayi sabon dan wasa ba a wannan kakar sakamakon dakatarwar da hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa tayi mata na hanata sayan ‘yan wasa sai sayarwa ma da tayi tad an wasan Edin Hazard wanda ya koma Real Madrid.

Acikin rukunin Chelsea zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Ajax Amsterdam, wadda ta buga wasan kusa dama karshe a gasar a kakar wasan data gabata kuma ta doke kungiyoyin Real Madrid da Juventus duka a gasar ta bara.

Har ila yau Chelsea zata fuskanci kalubale daga kungiyoyin Valencia da Lille wadanda dukkansu kungiyoyi ne wadanda suke bawa manyan kungiyoyi wahala kuma suna daya daga cikin wadanda suke iya fitowa daga cikin rukuni.

Tottenham, wadda ta buga wasan karshe da Liverpool a kakar data gabata zata fafata da kungiyoyin Bayern Munchen da Olympiakos da kuma kungiyar kwallon kafa ta Red Star Belgrade sai dai ana ganin Tottenhan din da Bayern Munchen sune zasu iya fitowa daga cikin rukunin duk da cewa Tottenham din bata kokari kamar yadda akayi zaton zatayi.

Bayern Munchen, wadda itama ake ganin zatayi abin arziki a wannan kakar bayan daukar aron dan wasa Coutinho daga Barcelona da kuma kwallayen da dan wasa Robert Lewandowki yakeyi yasa ta zama daya daga cikin kungiyoyin da zasu iya abin azo a gani a wanann kakar ta bana.

Real Madrid, wadda tafi kowacce kungiya yawan lashe gasar a tarihi tana cikin rukunin daya hadada kungiyoyin Paris Saint German da Club Brugge da kuma Galatasaray ta  kasar Turkiyya wadda dan wasan Najeriya Victor Moses yake bugawa wasa.

Sannan kuma mai koyarwa Zinadine Zidane, wanda ya kafa tarihin lashe kofin sau uku a jere a kungiuat ya dawo zai sake jan ragamar kungiyar bugu da kari akwai manyan ‘yan wasa irinsu Edin Hazard da kuma Luca Jobic da kungiyar ta sayo daga Frankfurt sai Ferland Mendy da Rogrygo da kuma Elder Militao.

Ita ma kungiyar kwallon kafa ta PSG ana ganin babu tabbas ko zata tabuka abin kirki a bana musamman halin da kungiyar ta shiga na rikicin Neymar da kuma rashin kwarewar wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar a kofin zakarun turai da kuma mai koyar da kungiyar, Sai dai kungiyar zata iya bawa manyan kungiyoyi mamaki duba da irin ‘yan wasan da kungiyar take dasu duk da cewa masu hasashe a gasar rukuni rukuni ta kasar Faransa sun bayyana cewa karfin kungiyar ya fara raguwa ba kamar shekarun baya ba da su ke iya doke manyan kungiyoyi.

Za a fara wasannin cikin rukuni ranar Talata 17 ga watan Satumbar shekarar nana, yayin da ake sa ran karkare gasar bana ranar 30 ga watan Mayun shekara ta 2020 a babban birnin kasar Turkiyya wato Istanbul.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: