Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ana Kara Yi Wa Kasuwar Hada-hadar Kudin Sin Gyaran Fuska

Published

on

Kwanan baya hukumar raya hada-hadar kudin kasar Sin ta tsayar da kuduri cewa, za a kara yiwa kasuwar hada-hadar kudi a kasar Sin zurfafa gyaran, ta yadda za a bunkasa ci gaban tattalin arziki mai inganci a kasar.
Tun bayan da kasuwar hada-hadar kudin kasar Sin ta fara samun ci gaba a shekarar 1990, aka rika yi mata gyaran fuska a matakai daban daban, a shekarar 2004, gwamnatin kasar Sin ta taba tsara wani shiri a fannoni tara ta yadda kasuwar za ta ci gaba yadda ya kamata, ya zuwa shekarar 2014 kuwa, kasar Sin ta gabatar da muradun ci gaban hada-hadar kudi wadanda ke kumshe da kasuwar hannun jari da kasuwar bashi da kuma kasuwar da za ta yi hasashen farashin hannun jari, a halin da ake ciki yanzu, gwamnatin kasar Sin tana gudanar da wani sabon zagaye na gyaran fuska kan kasuwar hada-hadar kudi domin dakile hadarin da yanayin rashin tabbas na hada-hadar kudin kasa da kasa zai haifar.
A yayin taron hukumar raya hada-hadar kudin kasar Sin, an yi nuni da cewa, za a kara raya kasuwar hada-hadar kudi a kasar yayin da ake yi mata gyare-gyare ta hanyar yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, saboda kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha zai taimaka matuka wajen raya kasuwar hada-hadar kudin kasar Sin.
An kafa kasuwar sayar da hannayen jarin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a ranar 13 ga watan Yunin bana a nan kasar Sin, kawo yanzu kamfanoni sama da 150 sun gabatar da bukatunsu na sayar da hannayen jarin kirkire-kirkirensu a cibiyar hada-hadar kudin birnin Shanghai, yanzu haka ana gudanar da aikin cikin lumana, ana sa ran cewa, kasuwar sayar da hannayen jarin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha za ta taka rawa ga ci gaban kasuwar hada-hadar kudin kasar Sin.
Yanzu matsalar da kasuwar hada-hadar kudin kasar Sin ke fuskanta ita ce, adadin hukumomin zuba jari ba su da yawa, kan wannan, hukumar hada-hadar kudin kasar Sin ta tsai da cewa, za ta ci gaba da yin kokari domin samar da sharuda masu inganci ga hukumomin zuba jari ta yadda za su kara zuba jari a kasuwar hannayen jarin kasar.
Abu mai faranta rai shi ne, manyan kamfanonin hada-hadar kudin kasa da kasa sun sake nuna amincewa ga hannayen jarin kudin Sin RMB, misali kamfanin Frank Russell ya daga kason RMB da ya saya daga kaso 5 bisa dari zuwa kaso 15 bisa dari, kamfanin MSCI shi ma ya daga kasonsa daga kaso 10 bisa dari zuwa kaso 15 bisa dari, matakan da manyan kamfanonin hada-hadar kudin kasa da kasa suka dauka, za su kara inganta bunkasuwar kasuwar hada-hadar kudin kasar Sin.
Hakika makasudin zurfafa gyaran fuska kan kasuwar hada-hadar kudi shi ne domin samar da hidima ga bangaren samar da kayayyaki, a don haka hukumar raya hada-hadar kudin kasar Sin ta jaddada cewa, zai yi kokari domin tabbatar da cewa, kasuwar hada-hadar kudi ta ingiza ci gaban tattalin arzki mai inganci a kasar.
(Mai Fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: