Connect with us

TATTAUNAWA

Dauda Lawal Ba Shi Da Tsara Wurin Taimakon Al’umma – Ali Alinco

Published

on

Babban dan kasuwar nan mai sana’ar sayar da motoci a Jihar Zamfara, Alhaji Ali Garba Alinco wanda ke da ‘Alinco Motors’ ya bayyana cewa, irin taimakon da Dakta Dauda Lawal Dare ke yi wa al’umma a fadin jihar Zamfara ba shi da tsara.

Alhaji Ali Alinco ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke zantawa da wakilin LEADERSHIP A Yau a ofishinsa da ke Gusau Babban birnin Jihar Zamfara.

Hirar ya yi ta ne domin fadin irin nagarta da kyawawan halayen Dauda Lawal Dare, wanda ya a jiya ya cika shekara 54 a duniya.

Dan kasuwan ya bayani sosai kan irin halin kyauta da Dakta Dauda yake da ita. Inda ya ce, da hannunsa Dakta Dauda ya sanyashi ya raba kyautan motoci kanana da manyan sama da 300, wanda har yanzu a na ci gaba da cin gajiyar wannan tallafi.

“Da ya ke sana’a ta ce sayar da motoci, wannan ya sa nake shaidar irin tallafin da Dakta Dauda ya yi wa mutane, wurin bayar da kyautan motoci sama da 300. Ni da kaina a ke sawa na bayar. Don haka ni shaida ne a kai,” in ji shi.

Da ya koma a kan  batun tallafin da Dakta Dauda ya bayar a fannin Ilimi kuwa, wadanda kaitsaye sun shafi rayuwar talakawa ne, Alhaji Alinco ya bayyana cewa, Dakta Dauda ne kadai wanda a duk fadin jihar Zamfara ya yi kwalta a tagwayen hanyoyin da ke cikin Jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Gusau (Federal Unibersity, Gusau).

Alinco ya ce; “A Makarantar koyon Jinya da Unguwar Zoma, Dakta Dauda Lawal ya gina masu manyan gidajen kwanan dalibai guda biyu domin amfanin dalibai Maza da Mata. Dakunan kwanan sun kunshi bangarori guda hudu a tsarin ginin sama da kasa. Kowanne sashe yana da dakunan kwana Takwas. Kowanne daki kuma an sanya mai gado hurhudu masu daukar dalibai biyu (wato dalibai Takwas kenan a kowane daki. Haka kuma ya samar da wurin wanka da bahaya a kowane daki da dai sauransu.

“Sannan kuma dakunan wurin kwanan dalibai Mata dari Biyu da Hamsin da Shidda ne. A bangaren Maza dalibai Dari da Ashirin da Takwas ne za su amfana da wurin kwanan. Kafin samar da wannan alheri daga Dr. Dauda Lawal wanda aka kammala tun a shekarar da ta gabata, dalibai Hamsin (50) Maza da Mata ne kawai ke samun wurin kwana a Makarantar. Haka nan ma a kwalejin kiwon lafiya da kimiya ta Tsafe kuwa, Dakta lawal Dare ya gina azuzuwa Tara kowanne dauke da duk kan kujerun su da tebura da duk abubuwan da ake sanya ma azuzuwan karatu ya sa yashi.

“Wannan ba kawai a iya Zamfara aikin tallafawa ilimin da Dauda ke yi ya tsaya ba. Ya gina dakunan kwanan dalibai a Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, da kuma wasu dakunan a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU)” Inji shi

Alhaji Alincon ya kuma kara da cewa, Dakta Dauda yana tallafawa makarantun addini da haka kuma ya taimaka wurin ginawa tare da sabunta masallatai a fadin jihar ta Zamfara. Ayyukan alherin nasa sun hada har da gyaran da kuma gyaran Makabartu.

Alinco ya ce: “Kuma yanzu haka duk da Allah bai bashi Gwamnan Jihar Zamfara ba ,amma ya hada kai da mai girma Gwamna Dakta Bello Muhammad Matawallen Maradun wajen kawo wa jihar Zamfara ci gaba ta kowanne sashe. Kuma a kan haka ya zamo dan lelen gwamna Matawale. Don yanzu haka shi ne ke jagorantar gina filin jirgin sama na Kago da ake kan ginawa a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

“Dakta Dauda Lawal ya shahara wajen harkar kasuwanci a cikin gida Nijeriya da ma a kasashen waje. Wanda ya sa kasar nan ke matukar alfahari da shi. Kuma yana daga cikin dabi’arsa shi ne mutunta mutane, da sakin fuska. Wannan ne ya sanya a al’umar Jihar Zamfara suka ga ya dace su mika goron gayyatarsu na ya fito takarar gwamnan Jihar Zamfara a karkashin inuwar jam’iyyar APC, kuma ya amsa kiran al’ummar ya fito takarar fidda gwani, duk da abin ya zo da tarnaki amma zaben ya ki yiwuwa.”

A fagen siyasa kuwa, Alhaji Ali Alinco ya ce, Dakta Dauda Lawal jarumi ne wanda ba shi da tsoro, jajirtacce ne, wanda a kodayaushe burinsa shi ne ya ga an kwatarwa mai hakki hakkinsa.

“Tsarin tafiyar siyasarsa ya sa a duk fadin Jihar Zamfara, mutanensa ne kadai ke tsaftatacciyar siyasa, don ya hana matasa bangar siyasa. Kuma duk masu zama a ofishin kamfen dinsa ya yi masu albashi da kuma basu abinci a kowace rana, wannan ya sanya ya yi zarra ga sauran abokan takararsu na jam’iyyar APC.

“Wannan ne ya sanya jama’a ke ci gaba da sha’awar shiga tawagarsa don ganin da kowa ya yi cewa, a tsaftace yake siyasa, ba tare da hauragiya ko banga ba. Kuma yanzu haka bayan kammala zabe, duk ‘yan takarar sun watsar da mutanensu, amma shi kuwa Dakta Dauda Lawal yana tare da ‘yan siyasarsa, kuma hatta lokutan shagulgulan sallah, mutanen tawagar Dakta Dauda Lawal su ne suka fi kowa darawa. Kai ka ce, su ke da gwamnatin jihar, saboda irin yadda yake tallafa musu.”

Daga karshe Alhaji Alinco ya ce: “A kan wadannan dalilai ne muke kara taya Dakta Dauda Lawal Dare murnan cika shekaru hamsin da hudu masu albarka. Kuma mu ke kira ga masu hannu da shuni da ‘yan siyasa da su yi koyi da kyawawan halaye da saukakakkiyar  rayuwa irin ta Dakta Dauda Lawal”.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!