Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Ekiti: Wasu Mahara Sun Halaka Wani Dan Acaba

Published

on

Mazauna yankin Aba da ke babbar barnin Ado Ekiti sun fada cikin tashin hankali, lokacin da a ka samu labarin cewa, wasu mutane wanda ba a san ko suwane ne ba  sun taba wa wani matashi mai suna Sunday Olorunleke wuka har lahira. An bayyana cewa, shi dai mamacin dan acaba ne, an kashe shi ne a gidansa da ke yankin Aba cikin jahar.

Majiyarmu ta ruwaito mana cewa, mutumin tare da yaransa guda biyu su na cikin gida lokacin da lamarin ya afku. Majiyar ta kara da cewa, matar mamacin tare da sauran yaransa sun yi tafiya tun ranar Laraba, inda su ka dawo a ranar Asabar da safe su ka isar da gawar marigayin sharbe cikin jini a dakinsa. Majiyar ta tabbatar da wannan kisa, inda ta bayyana cewa ta na zargin wannan lamari ya furu ne tsakanin daren Juma’a da kuma ranar Asabar. Ta kara da cewa, mamacin ya gana da makwabcinsa a ranar Alhamis da safe.

“Matar mamacin ta kira wasu daga cikin makwabatansu sa’ilin da ba ta samu wayar mijinta ba, inda su ka shaida mata cewa ya na cikin koshion lafiya domin sun ganshi a wannan rana ta Alhamis. “Mun girgiza kwarai lokacin da matar mamacin ta dawo daga tafiya a ranar Asabar da safe, inda ta tarar da kofa rufe, nan take ta nemi taimakon mutane wajen balle kofar, lokacin da a ka balle kofar, sai a ka sami gawar mamacin kwance cikin jini.”

Da ya ke zantawa da manema labarai ta wayar salula, kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Ekiti, Caleb Ikechukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa, ana gudanar da bincike domin damke wadanda su ka aikata wannan mummunar aikin. Ya kuma bukaci mutane da su kwantar da hankulansu, sannan su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda su ka saba. Kakakin rundunar ya shawarci mazauna yankin a kan su sanar wa ‘yan sanda duk wata zirga-zirga wanda ba su yarda da ita ba a yankunansu, domin daukar matakin gaggawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!