Connect with us

MAKALAR YAU

Minti 30 Tare Da Injiniya Rabi’u Kwankwaso

Published

on

A karshen makon nan na samu ziyartar tsohon gwamnan Kano, Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, kususan don yi ma sa jaje kan batan dan uwa abokin gwagwarmaya, Abubakar Hanifa, wanda a ka fi sani da Dadiyata. Hakika duk mutumin da ya ke yin warkamaji a kafafen sadarwar zamani, ya san irin kokarin da Dadiyata ya ke yi wajen tallata manufofin da jagoransa a siyansance. Misali ni, duk da mu na saba wa da shi a lokuta daban-daban har ma ta kai mu ga zazzafar takaddama, na shiga tashin hankalin matuka da gaske da batan wannan dan ta’aliki.

Yau kusan kwana 30 kenan da batan Dadiyata, wanda a ka ce wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun je har kofar gidansa, su ka yi awon gaba da shi. Hakika wannan labarin ya tayar wa da mutane hankali matuka da gaske, inda a ka rika kiran jami’an tsaro da su tsananta bincike, domin gano inda Abu Hanifa ya shiga.

A kafafen sadarwa zamani tuni tuni su ka kaddamara da #PrayForDadiyata. wanda dubunnan mutane ke yekuwa kan lallai hukumomin tsaro su yi mai yiwu, domin kubuto da shi, amma har yanzu shiru ka ke ji.

Babban abinda ya ja hankalina bai wuce yadda wasu ke maganganu maras dadi na cewar ‘yan siyasa ba su damuwa da mutanensu a lokacin da wani ibtila’i ya fada mu su ba. Sai dai a sanin da na yi Kwankwaso sama da shekaru 10, ina da yakinin shi din ba haka ya ke ba, kuma bisa abinda idona ya gane min, lallai Kwankwason bai canja ba, ya na rike mutanensa a zuciya domin kulawa da su daidai bakin gwargwado, haka zalika Abu Hanifa Dadiyata ya na cikin ransa.

Mun tattaunawa batutuwa da yawa, musamman kan batan Dadiyata da kuma irin kokarin da a ke yi na ganin Allah ya kubuto da shi daga wannan halin da ya ke ciki. Wannan ta sa na ga dacewar yi mana waiwaye, wanda masu iya magana su ka ce adon tafiya, kan irin gudunmawar da Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba wa al’umma, musamman Kanawa da kuma irin sakayyar da ya kamata a yi ma sa.

Kullum idan mu ka hadu da Kwankwaso, na kan ce ma sa ba gadojin da ya gina a Kano ne ya sa maza, mata, samari da kananan yara ke nuna ma sa kauna ba, illa iyaka irin kokarin da ya yi wajen wayar da kan al’umma ta hanyar ba su ilmi da wata rana za a yi alfahari da su.

Kusan zan iya cewa kai yara ko kuma dalibai kasashen waje domin yin karatu ya na daya daga cikin wasu ayyuka da gwamnatoci su ke yi tun daga gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin jihohi wanda hakan wani tsari ne na kawo cigaba a cikin al’umma.

Jihar Kano tana daya daga cikin jihohin da su ke kurbar romon dimokradiyya musamman idan a ka yi magana ta daukar ‘yan asalin jihar domin zuwa kasashen waje karatu daga digiri na farko da na biyu har da na uku.

A lokacin gwamnatin Kwankwaso, bayan ya dawo mulkin Kano a karo na biyu daga shekara ta 2011 zuwa 2015, Kwankwaso ya tura dubunnan dalibai daga jihar Kano inda su ka je su ka yi karatu a fannoni da dama na ilimi a kasashe daban-daban na duniya kuma wasu daga cikinsu sun dawo Najeriya yayin da wasu kuma su ka cigaba da zama a kasashen da su ka yi karatun sakamakon damarmakin da su ka samo na zama a kasashen.

Wasu daga cikin daliban sun kammala karatuttukansu sun dawo Najeriya su na cigaba da harkokinsu yayin da wasu su ka zama malaman makaranta wasu kuma su ka dogara da kansu wasu kuma su ka kama aiki da hukumomin da ba na gwamnati ba.

Sai dai kamar kowacce gwamnati an samu matsaloli bayan tafiyar gwamnatin ta Kwankwaso, musamman wajen cigaba da biya wa daliban da a ka tura kudin makaranta  bayan da gwamnatin da ta gaji gwamnatinsa ta bayyana cewa, an yi coge sannan kuma akwai kurakurai a kan maganar tura wadannan yara.

Har yanzu akwai daliban da su ke kasashen waje kuma ba a kammala biya mu su kudin makarantar ba sakamakon sabani da aka samu tsakanin Kwankwaso da gwamnatin da ta ke ci, sannan kuma abubuwa da dama na siyasa sun shiga cikin lamarin daliban da har yanzu su ke faman rokon gwamantin Kano a kan biya mu su kudaden nasu domin su dawo gida.

Kwanakin baya ne tsohon gwamnan na Kano, Injiya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ya kammala shirye-shiryensa na kai wasu daga cikin dalibai kusan 370 ’yan asalin jihar Kano, wadanda su ka fita da mataki mai daraja ta farko (wato First Class) a makarantun da su ka gama domin turasu kasashen waje cigaba da digiri na biyu wanda hakan ya biyo bayan kammala tantance daliban tun farko.

Kwankwaso ya kafa gidauniyar tallafawa wadannan dalibai domin tara kudin da za a biya mu su kudin makaranta kuma sakamakon taron kafa wannan gidauniya an tara miliyoyin kudin da za a yi amfani da su ta hannun manya manyan ’yan siyasar Kwankwasiyya da kuma manya-mayan ’yan kasuwa na jihar nan da ma jihohin da su ke cikin kasar nan.

Yayin da abubuwa su ka tabarbare a kasar nan musamman rashin aikin yi da ya yiwa kasar nan katutu wannan yunkuri da Kwankwaso ya yi zai taimakawa wadannan yara wajen dogaro da kansu ta hanyar yin amfani da abinda suka karanta ba tare da dogaro da gwamnati ba.

Har ila yau wasu daga cikin daliban za su iya samun aiki  a inda su ka je karatun kamar yadda kashi na farko su ka yi a shekarun baya kuma za su kasance sun zama ma’aikata a wadannan kasashe hakan ya na nufin an samu aikin yi a tsakanin wadannan yara sannan kuma an samu raguwar cinkoson marasa aikin yi a jihar.

Idan kuma mu ka kalli abin ta fuskar ilimi zuwan wadannan dalibai kasashen waje zai taimaka wa makarantun kasar nan ta hanyar samun kwararrun malaman da za su dawo domin taimaka wa makarantun da suke kasar nan ba kawai jihar Kano ba.

Har ila yau samun masu ilimi a cikin kasa zai taimaka wajen rage aikata muna nan laifuffuka saboda yawancin masu aikata laifi akwai karancin ilimi da kuma rashin aikin yi a tattare da su, sannan kuma zai taimaka wa al’ummar jihar Kano wajen samun al’umma mai cikakken tunani mai kyau da kuma fito da hanyoyin cigaban jama’a.

Haka kuma idan mu ka kalli abin ta bangaren siyasa za mu ga wannan yunkuri da Kwankwaso ya yi wani sabon lissafi ne na siyasa wanda ya shigo da shi ta hanyar tallafa wa matasa da ilimi wadanda kuma matasan nan su ne kashin bayan kowacce al’umma kuma duk inda a ka ce matasa su na son abu ko kuma wani dan siyasa tabbas wannan abin ko dan siyasar zai yi karko.

Ya na daya daga cikin abubuwan da Kwankwaso da ’yan Kwankwasiyya su ke alfahari da shi kuma dan takarar gwamnan jihar Kano, Abba K Yusuf ya yi yakin neman zabe da shi, wato kai yara karatu kasashen waje kuma matasa da dama su na bin tafiyar Kwankwaso ne saboda wannan dalili.

Kafin babban zaben shekara ta 2019 da aka gudanar a watannin baya kungiyar Kwankwasiyya ta na da kungiyoyi da dama a karkashinta wanda kuma daya daga cikin wadannan kungiyoyi akwai kungiyar dalibai wadanda Kwankwaso ya tura kasashen waje karatu kuma sun bada gudaunmawa sosai a yakin neman zaben Abba Kabir Yusuf wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar PDP.

Babu wani abu da za ka ba wa matasa a wannan lokaci wanda ya wuce ilimi kuma duk wanda ka ba wa ilimi bazai taba mantawa da kai ba a rayuwarsa saboda ta hanyar ilimi duk wani wanda ya zama wani abu a duniya za ka iya zama kamarsa.

A halin da a ke ciki Kwankwaso ya na daya daga cikin manyan ‘yan siyasa a kasar nan sannan kuma a arewacin kasar nan idan a na maganar dan siyasa wanda zai iya tara mutane masu zabe tabbas Kwankwaso ba shi da na biyu.

Idan mu ka duba za mu ga wadanda su ka samu damar zuwa karatu a lokacin da Kwankwaso ya na gwamanan jihar Kano yanzu dayawa daga cikinsu sun zama wasu mutane domin wasu sun zama malaman makarantun gaba da sakandire wasu kuma sun zama manyan ma’aikata a kamfanunuwa daban-daban ciki har da wadanda su ka zama matukan jirgin sama da likitoci da wadanda yanzu su na zaune kasashen waje suna aiki ko kuma su na kasuwanci.

Ban da jihar Kano, Kwankwaso dan siyasa ne wanda ya ke da dubunnan magoya baya a ragowar jihohin da su ke arewacin kasar nan musamman yadda ya ke tallafawa harkokin ilimi da kuma yadda ya kawata jihar Kano da gine-gine na gadojin sama dana kasa da kuma bude makarantun gaba da sakandire dana koyon sana’a, sannan kuma uwa uba shi ne gwamna na farko kuma na karshe a jihar Kano daya kirkiro jami’u guda biyu da su ka hada da jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke garin Wudil da kuma Jami’ar Northwest Unibersity da ke cikin birnin Kano.

Kwankwaso ya zama jagora kuma jigo a siyasa musamman a arewacin Najeriya kuma ya na kafa wani tushe wanda nan gaba ture shi zai yi wahala ta hanyar taimaka wa matasa su yi ilimi, wanda kuma nan gaba matasan su ne za su kasance shugabannin wannan kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!