Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mutun Uku Sun Mutu A Hatsarin Mota Kan Hanyar Numan-Yola

Published

on

A kalla mutane uku sun rasa rayukansu, yayin da mutane da dama su ka jikka a wani hatsarin mota wanda ya faru a kusa da garin Yola babbar birnin Jihar Adamawa. Hatsarin wanda ya afku a Yola karshen kan hanyar Numan zuwa Yola, lamarin ya rutsa da wasu motoci guda biyu na sufurin motocin Jihar Adamawa.

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a cikin wannan hatsari, wanda a halin yanzu ya ke jinya a wata asibiti ta musamman da ke garin Jimeta, ya bayyana wa ‘yan uwansa wadanda su ke jiyarsa cewa, motar da su ke ciki ne ta bugi wata mota da ke zuwa, inda nan take mutum biyu su ka mutu, daya daga ciki ya fada cikin kogin da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.

Wani daga cikin dan uwan wanda ya tsallake rijiya da baya mai suna Mista Joseph Adanu, ya bayya wa wakilinmu a ranar Juma’a cewa, direban motar nasu ya samu mummunar rauni, hatsarin dai ya faru ne ranar Laraba, ya yi sa’a da ya tsallake rijiya da baya. Ya kara da cewa, ba a san musabbabin da ya sa direban motar ya rikice ba har ya doki daya motar ma zuwa. Mista Adanu ya ce, kamar yadda ya sami labara daga wurin dan uwansa cewa, akwai motoci da yawa a gaban motarsu bayan da direban ya wuce motar da ke gabansa, babu ta yadda za a yi direban ya kauce wa wannan hatsari.

“Kawuna ya dawo daga kasar waje kenan, sai ya zo garin Yola domin ya ga likita a kan ya duba lafiyarsa, bai san abinda ya faru da fasinjojin dayar motar ba, amma dai ya bayyana cewa motar ta yi mummunar lotsewa,” in ji Adanu.

Kwamandar hukumar kiyaye hadararruka ta Jihar Adamawa, Husseini Muhammed ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ta wayar salula a ranar Juma’a da yamma, sai dai bai bayar da yawan adadin wadanda hatsarin ya rutsa da su ba. Ya kara da cewa, wani mutum ne ya kawo rahoton lamarin bayan hatsarin ya faru, lokacin da mutumin ya kawo rahoton lamarin ya yi latti, domin kuwa sa’ilin da jami’anmu su ka isa wurin da lamarin ya afku, mutanen yankin sun kammala bayar da duk wata agajin ga wadanda lamarin ya shafa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!