Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Neja: Barawo Ya Balle Kofar Masallaci Ya Sace Kayan Lasifika

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Neja, ta samu nasarar cafke wani saurayi mai suna Usman Adamu dan shekara 34, dan asalin yankin Fadikpe da ke Minna, bisa zargin sa da balle kofar masallacin Kwarkwata da ke karamar hukumar Bosso ta jihar tare da sace kayayyakin abun magana. Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Muhammad Abubakar shi ya bayyana hakan ranar Alhamis a garin Minna. A cewar Abubakar, an samu wanda a ke zargin kuma har tawagar ‘yan sanda sun samu nasarar damke shi bisa bayanai sirri da su ka samu. Ya kara da cewa, tun da dadewa wanda a ke zargin ya na cikin sunayen ‘yan fashin da makami wadanda ‘yan sanda su ke nema ruwa ajallo, inda ya balle kofar masallaci sannan ya sace kayayyakin abun magana. Kakakin rundunar ‘yan sandar ya tabbatar cewa, an samu nasarar kwato kayayyakin abun maganar daga hannun wanda a ke zargi.

Da ya ke magana da manema labarai a shalkwatan rundunar ‘yan sanda, Adamu ya amsa cewa ya na cikin ‘yan fashi da makami tun a shekara biyu da su ka gabata. “Muna yawan sace kayayyakin mutune duk lokacin da mu ka samu wata dama. Ina fasa gidajen mutane musamma ma lokacin da su ka tafi aiki ko kuma lokacin da su ke yin barci. Ina da karfen da zai iya bude duk wata kofa da nake son budewa,” in ji shi.

Ya bayyana dalilin da ya sa ya saci kayayyakin abun magana daga masallaci, Adamu ya ce, “na saci abun maganan ne saboda in saida don in samu kudin kulawa da kaina.”

Za a gurfanar da wanda a ke zargin a gaban kuliya idan a ka kammala cikakken bincike a kan lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!