Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Suleja: Mutum Uku Sun Rasa Rayukansu Lokacin Da Tankar Mai Ta Fashe

Published

on

An tabbatar da mutuwar mutum uku, yayin da mutane da dama su ka jikkata sa’ilin da wata tanka cike ta man fetun ta yi bindiga a garin Suleja cikin Jihar Neja. Babura guda 19 sun kone kurmus a wannan lamari.  Lamarin ya afku ne a ranar Juma’a da dare a mahadar hanya da ke yankin Dikko kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna. Nan take wani mutum ya kone kurmus, yayin da mutum biyu su ka mutu a asibiti. Har zuwa yanza dai babu wanda ya san musabbabin wannan fashewar, amma dai hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Neja ta na gudanar da bincike a kan lamarin. An ijiye gawarwakin mamatan a dakin ijiye gawarwaki da ke asibitin Umaru Musa cikin yankin Sabon Wuse, yayin da wadanda su ka jikkata kuma su na yin jinya a wannan asibitin.

Daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, Ahmed Inga, ya tabbatar da wannan lamari. Ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10.30 na daren Juma’a. Ya ce, har yanzu ba a san yawan adadin wadanda su ka jikkata ba. “Mun samu rahoton lamarin a ofishinmu da ke garin Suleja cewa, tankar mai ta fashi kuma lamarin ya shafi mutane da dama. “Sai dai a yanzu haka ba za mu iya bayyana yawan wadanda su ka rasa rayukansu ba, za mu gudanar da bincike, sai dai daga rahoton da mu ka samu daga ofishinmu na garin Suleja ya nuna mana cewa, mutum daya ya rasa ransa a wannan lamari. “Mutane da dama sun samu raunika, sannan ababan hawa da dama sun kone kurmus.”

Inga ya cigaba da cewa, hukumar kashe gobara ta tarayya da kuma ta jiha sun samu nasarar kashe wannan gobara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!