Connect with us

WASANNI

Chelsea Ta Bayar Da Rahman Aro Kungiyar Mallorca

Published

on

Mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Baba Rahman ya koma kungiyar Real Mallorca, domin buga mata wasannin aro, bayan da ya saka hannu kan yarjejeniyar zama a Chelsea na shekaru biyar.

Rahman wanda ya koma Chelsea daga kungiyar kwallon kafa ta Augsburg a kakar wasan shekara ta 2015, zai ci gaba da zama dan kungiyar wadda Frank Lampard yake koyarwa har zuwa karshen kakar wasa ta 2022.

Kamar yadda Chelsea ta sanar a shafinta na Intanet ta ce dan kwallon zai buga wa kungiyar kwallon kafa ta Real Mallorca wasannin aro har zuwa karshen kakar bana bayan kungiyoyin biyu sun kulla yarjejeniya a ranar Litinin din data gabata.

“Muna yiwa dan wasanmu Baba Rahman farin cikin samun kungiyar da zai cigaba da bugawa wasa a kakar wasa ta gaba muna fatan zai buga kwallo yadda yakamata domin ganin ya sake gogewa yadda zai zama babban dan kwallo” in ji Chelsea a shafinta na Sadarwa

Rahman mai shekara 25 dan kwallon tawagar Ghana ya yi wasannin aro a kungiyoyin Schalke 04 ta kasar Jamus da Reims ta Faransa sai yanzu daya koma Mallorca wadda ta koma buga gasar La Liga a bana, bayan da ta yi nasara a wasannin cike gurbin da ta yi.

Dan wasan ya fara buga wa Chelsea wasa a karawar da ta doke Maccabi Tel Abib a gasar cin kofin zakarun turai na  Champions League a watan Satumbar shekara ta 2015, jumulla ya buga mata wasanni 23 tun bayan komawarsa kungiyar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: