Connect with us

LABARAI

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri Na Adamawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Published

on

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya tsallake rijiya da baya a wani harin da ‘yan binga suka kai a Lokoja stadium dake jihar Kogi, lokacin da jam’iyyar PDP ke gaf da kammala zaben fidda gwani da asubahin ranar Laraba.

Rahotanni daga Lokoja stadium inda lamarin ya auku, sun tabbatar da cewa ‘yan awanni kafin kammala kirga kuri’a da sanar da wanda ya yi nasara, kawai sai ga ‘yan bindiga sun shigo filin wasan da jam’iyyar ke gudanar da zaben.

“mun kammala kada kuri’a, muna kan tantance kuri’un, kawai muka ji ‘yan bindiga sun iso wajajen qarfe xaya da minti arba’in da biyar na safiyar laraba (1:45am), munajin harbe-harbe ta vangarori daban daban” inji ganau.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa a kwatunan zaven takwas daga cikin goma an rigada an kammala qirgasu da tantancesu kafin zuwan ‘yan bindigar filin gudanar da zaven.

A nan take dai ‘yan takara, masu kaxa quri’u kowa ya yi ta ransa domin neman tsira, kawo lokacin haxa wannan rahoton ba a kai ga tantance mutanen da suka jikkata ko rasa rayuka ba.

Dama dai gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, yana filin zaven ne a matsayin shugaban kwamitin gudanar da zaven, da shima ya tsallake rijiya ta baya daga harin ‘yan bindigar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: