Connect with us

Da dimi-diminsa

Gwamnan Bauchi Ya Janye Sunan Sani Damban A Cikin Kwamishinoninsa

Published

on

Kwana guda da fara tantance Kwamishinonin da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya aike wa majalisar dokokin jihar Bauchi domin tantancewa da amincewa da su, kwatsam sai majalisar ta riski wasika daga wajen gwamnan wanda ke bukatar ta amince masa janye sunan mutum guda daga cikin jerin wadanda ya aiko tun a farko.

Gwamna Bala ya cire sunan Dakta Sai Muhammad daga karamar hukumar Dambam a cikin jerin sunayen kwamishinonin da ya zaba gami da sauya shi da wani, inda majalisar kuwa ta amince masa da sauya sunan.

Wakilinmu ya shaida mana cewar a ranar Litinin 2 ga watan Satumba ne gwamnan ya aike da bukatar janye sunan mutum guda daga cikin wadanda ya nemi su zama masa kwamishononi a zangonsa ta farko.

Sai dai babu cikakken bayani kan dalilin gwamna na daukar wannan matakin.
Da yake yi wa ‘yan jarida karin haske kan wannan matakin, Musa Wakili Nakwanda, mambar majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Bogoro kana mai magana da yawun majalisar, ya shaida cewar gwamna yana da cikakken ikon turo sunan wanda yake so da janyewa.

A cewar shi; “Gwamnan shi ke da ikon zabar wadanda zai aiko majalisa domin tantancesu, don haka yana da cikakken ikon janye sunan wanda yake son ya janye daga cikin jerin sunansu kwamishononinsa,” A cewar shi.

Wakilinmu ya shaida mana cewar a jiya Talata majalisar ta dauka domin fara tantance Kwamishononin inda ta amince da sunayen mutum goma daga cikin kwamishinonin jihar.

Musa Wakili ya jero sunayen kwamishononin goma da majalisar ta tantance gami da amincewa da su ranar farko, inda ya bayar da sunansu da kamar haka: Farfesa Adamu Ahmad daga qarama hukumar Ningi; Dakta Aliyu Tilde qaramar hukumar Toro; Abdulkadir Muhd Chika Soro, Alkaleri; Umar Abubakar Sade, Darazo; Jidauna Tula Mbami, Bogoro; Hajiya Hajara Itas/Gadau; Dakta Aminu Hassan Gamawa; Turaki Muhammad Manga, Misau; Abdulrazak Nuhu Zaki, Warji; sai kuma Ahmade Aliyu Jalam daga qaramar hukumar Damban, dukkaninsu majalisar ta tantancesu haxi da amincewa da sub a tare da bata wani lokaci ba.

Wakilinmu a majalisar dokokin jihar ta Bauchi, ya shaida mana cewar wasu daga cikin wadanda aka tantance sun fuskanci tambayoyi zafafa daga majalisar jihar, inda wasu kuma tambayoyi masu sauki ne suka riske su, saidai babu guda daga cikin goman da suka tantance wadanda suka ki amince da shi.

Kamar yadda majalisar ta tsara, a yau Laraba ma za ta karasa tantance sauran kwamishinonin da gwamnan yake son su zama masa mukarrabai.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: