Connect with us

MAKALAR YAU

Hare-haren ‘Yan Bindiga: Daga Yau Za A Daina Kashe-kashe A Jihar Katsina

Published

on

Abubuwa ba su dadin ji da gani suna ta kara bayyana a jihar Katsina dangane da iftila’in da ya fadawa wannan jiha mai dadadan tarihin zaman lafiya a tarayyar Najeriya wanda yanzu haka magana ta yi nisa sai dai karashewa cikin yardar Allah.

Wannan masifa da ta afkawa ji har Katsina sakamakon makwabtaka da take yi da wasu jahohi da suka hada da jihar Kaduna da kuma Zamfara, ba karamin baida al’amura baya ta yi ba a wannan jiha musamman abubuwan da suka shafi zaman lafiya da tattalin arziki da Noma da Ilimi da duk wani abu da yake da alaka da more rayuwa.

Tunda daga shekarar 2015 lokacin da gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya samu nasarar lashe zabe, jim kadan bayan samun wannan nasara gwamnatinsa ta ci karo da burbushin wannan matsala ta barayin shanu da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma ‘yan fashin da Makami.

Bisa da la’akari da hagen nesa irin na Malam Aminu Bello Masari bai dauki wannan matsala da wasa ba, bai dauke ta a matsayin wani abu wai shi siyasa ba, tun a wancan lokacin ya yi iyakar kokarinsa a matsayinsa na Gwamna.

Sai dai ganin yadda wannan matsala ke cigaba da ruruwa kamar wutar daji, hakan ya kara data hankalin jama’a da kuma su shuwagabannin tare da shirya taruruka na gaggawa domin lalubu hanyar da za a warware wannan iftila’I da ya afkawa jihar Katsina mai tarihin zaman lafiya.

Ko shakka babu wannan bala’I wasu ke amfana da shi, wasu kuma suna azzabtuwa da faruwarsa, ko ba dai menene zamu duba kokarin gwamnatin jihar Katsina da kuma gwamnatin tarayya mu ga me suka yi wajan ganin an samu mafita jini ya daina zuba.

Abu na farko da gwamna Aminu Bello Masari ya fara yi shi ne amincewa ayi sasanshi da yin afuwa ga mutanen da ke aikata wannan mummunan laifi, babar manufa anan shi ne, duk abinda wani zai ce ya dade bai ce ba, idan dai har za a samu nasara a daina kashe jama’a da kwashe dukiyoyinsu ba gaira ba dalili.

Anyi kokarin matuka wajan ganin wannan shiri ya yi nasara, jama’a da dama sun sa ido su ga yadda zata kaya, amma dai masu fadin alheri game da wannan shirin sun fi masu fadin akasin haka, mafiyawan jama’a suna sukar abun ne saboda rashin kauna da jituwa da wanda aka ba jagorancin tafiyar da wannan lamari.

Wannan dalili yasa wasu suka rika fatan cewa kadda Allah yasa wannan shirin ya yi nasara, duk da haka an samu nasara a wancan lokaci, wanda haka tasa har wasu gwamnoni suka yi kokarin ganin cewa suma sun kwaikwaiyi gwamna Aminu Bello Masari.

Sannu a hankali wannan shiri ya gamu da baban cikas satar mutane domin neman kudin fansa da satar shanu da kuma fashi da makami suka koma babar sana’a a jihar Katsina musamman wasu yankuna da suke da makwabtaka da jihar Zamfara da kuma Kaduna.

Sakamakon tarbabarewa wannan lamari sai da ta kai gwamna Masari da kansa yana fadin cewa gaskiyar magana ana cikin halin rashin tabbas a jihar Katsina akan sha’anin tsaro wanda haka ya kara farkar da gwamnatin tarayya wanda alhakin haka ya rataya a wuyanta ta yi na wani hubbasa a sakamakon bayyana wannan matsala da gwamna Masari ya yi.

A gefe guda kuma an cigaba da yin taruruka da tattaunawa da jama’a musamman masana akan harkar tsaro domin dai kawai kwaliya ta biya kudin sabulu game da sha’anin tsaro a wannan jiha ta Katsina.

Duk lokacin da wani abu ya faru da ya shafi kai hare-haren wuce gona da iri ba tare da bata lokaci ba gwamna Masari zai yi kokarin zuwa inda wannan lamari ya faru domin jajantawa wadanda wannan iftila’I ya afkawa, tare da ba su hakuri da yi masu alkawarin cigaba da yin iyakar ganinsa wajan ganin wannan lamari ya zo karshe.

Halin dantako da gwamna Masari yake nunawa jama’a ya kara sanya jama’a suka kara bashi dama domin ya cigaba da wannan kokari na shi, har a kai ga nasara, amma da yake wannan kaddararan abu ne daga Allah sai da ya koma wani abu daban.

A lukotan baya, jama’ar da wannan bala’I ya fadawa, sun rika dauko gawawakin jama’ar da aka kashe zuwa fadar mai martaba Sarkin Katsina ,Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da kuma shin kan shi gwamna jihar Katsina domin ya kara ganewa idanunsa wannan masifa.

Wannan lamari sai da ya haifar da zubar da  hawayan gwamna Aminu Bello Masari a gaban bainar jama’a, saboda tausayi da yakana da kuma dattako irin da shugaban mai jin jama’rasa a jikinsa.

A dalilin haka, gwamna Aminu Bello Masari ya cigaba da kai komo a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kara lalubu hanyar magance wannan  matsala, sai dai hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Duk abubuwan da na fada a sama suna a matsayin matashiya ne dangane da abubuwa da suka faru ko suke faruw a jihar Katsina da ya shafi  hare-haren ‘yan bindiga da masu satar shanu wanda ya ta’azara a wannan lokaci ya hana komi tafiya yadda ya kamata.

To, amma sabon tunani da kara nuna cewa wannan lamari ya shafi shugaba ne kai tsaye indai da gaske shugaban ne, gwamna Aminu Bello Masari ya shirya tsaf domin tunkarar wannan bala’I da kansa, don ganin abinda ya turuwa buzu nadi, kila ma dadi ne ya turewa buzu nadi Allah Masani.

Bayan harin wuce gona da irin da ‘yan bindiga suka kai a garin Wurma da ke karamar hukumar Kurfi kwanan nan, inda suka kwashe mutane da dama gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin Sakatarn gwamnatin jihar Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ta kira wani taron gaggawa da wakilan wadannan ‘yan bindiga domin ayi ta ta kare.

Duk wanda ya je inda aka yi wannan taro sannan ya ji abinda gwamna Masari ya bayyana game da halin da jihar Katsina ta shiga yasan cewa tura ta kai bango, wannan lamari ya isa haka,  “enough is enough” inji shi, haka kuwa ba wai yana nufin a baki kadai ba, a wannan karon mai gayya mai aiki ne da kansa zai jagorancin wannan al’amari domin samun nasara da yardar Allah.

Tun kafin a kammala taron gwamna Masari ya fada cewa abin kirki ne ke da wahalar yi, amma sheganta kowa ya iya ta, ga mai hankali wannan ba karamar magana ba ce, amma wasu sun dauki abin da wasa, a ya yin da wasu ke ganin cewa an zo wajan domin yanzu ido ya koma akan gwamna Masari na ganin yadda wannan abu zai zama tarihi.

A yau laraba da yarda Allah gwamna Masari tare da rakiyar jama’an tsaro na kowane bangare da manyan jami’an gwamnatinsa da mu kan mu ‘yan jarida masu yada labarai za mu shiga cikin daji domin ganawa ido-da-ido da wadannan ‘yan ta’ada domin jin dalilin da yasa suka hana jihar Katsina zama lafiya.

Wannan yinkuri abu ne na Allah san barka, abu ne da yarda Allah zai taimaka wajan kawo karshen kashe-kashe da satar mutane da fashi da Makami da sauran muyagun laifufuka Insha’Allahu

Saboda haka kowa yanzu a jihar Katsina yana da kwakwawar fatan cewa da yardar Allah an kawo karshen wannan al’amari da ya dade tana tafiya da rayukan jama’a.

Daga cikin abubuwa da jama’a su ka shirya wajan taimakwa gwamna Masari domin samun nasara shi ne, a gobe Alhamis an shirya taron addu’a na musamman da niyyar Allah ya kowa karshen wannan bala’I ya tona asirin masu hannu a ciki ya kawo zaman lafiya a jihar Katsina da arewacin Najeriya da kuma Najeriyar bakidaya.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: