Connect with us

WASANNI

Kano Pillars Ta Kara Wa Kociyanta Kwantiragi

Published

on

Duk da cewa kungiyar ta gaza kaiwa zagaye na gaba a gasar cin kofin zakarun nahiyar Africa bayan da tayi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta Ashanti Kotoko a watan daya gabata da kwallaye 4-3 gida da waje.

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta karawa kociyanta, Ibrahim Musa sabon kwantiragi wanda zai zauna a kungiyar har karshen kakar wasa ta gaba wadda ake shirin fara wa a karshen wannan watan daya kama.

Kamar yadda kungiyar ta sanar a shafinta na sadarwa wato Twitter, ta bayyana cewa mai koyarwa Ibrahim Musa zai cigaba da zama mai koyarwa yayinda kuma tsohon dan wasan kungiyar, Ahmad Garba Yaro yaro a matsayin mataimaki sai kuma Friday Christopher a matsayin mataimakinsu.

Shima mai koyar da masu tsaron ragar kungiyar Muzammil Aliyu, zai cigaba da kasancewa a matsayinsa yayinda Kabiru Baleria shima acikin sanarwar zai cigaba da kasancewa a matsayin manajan kungiyar ta jihar Kano.

A kakar wasan data gabata tsofaffin zakarun na gasar fiirmiya ta Najeriya, Kano Pillars, sune suka karkare gasar a mataki na biyu bayan da kungiyar Enyima Internatuonal ta jihar Abia ta zama zakara a gasar ta bara.

Har ila yau, a kakar data gabata Kano Pillars ta lashe gasar cin kofin kalubale na kasa wato Aito Cup, bayan data doke kungiyar Niger Tenardors a wasan karshen da suka fafata a Kaduna kuma nasarar itace nasara ta farko da kungiyar ta samu ta lashe kofin na kalubale kusan shekaru 30 kenan.

Sai dai bayan tabbatar da masu horar da kungiyar shugaban gudanarwar kungiyar ya bayyana cewa zasu sayi sababbin ‘yan wasan da zasu taimakawa kungiyar wajen tunkarar kakar wasan da za’a fara nan bada dadewa ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: