Connect with us

RAHOTANNI

Kwallon Kafa Ya Zama Babbar Sana’a A Duniya – Abdullahi Deko

Published

on

Wani matashi mai gudanar da harkokin wasannin kwallon kafa a karamar hukumar  Malumfashi a cikin jahar Katsina mai suna Abdullahi Kabir Deko ya bayyana cewar wasannin kwallon kafa a halin yanzu ya zama babbar sana’a ga matasan Nijeriya da na duniya bakidaya.

Abdullahi Kabir Deko ya fadi haka ne a filin wasannin kwallon kafa da ke cikin garin Malumfashi  ta jihar Katsina a lokacin da ya sanya gasar cin kofi tare da zunzurutun kudi har Naira 250,000 da ke gudana a halin yanzu.

Abdullahi Kabir Deko  ya cigaba da cewar, dalilan da su ka sanya ya sa wannan gasar ta cin kofi da zunzurutun kudi har Naira 250,000, shi ne domin ya rage wa matasa zaman kashe wando tare da gano tim din da ya fi ’yan wasa gwanaye da su ka zama zakaru a cikin tumatuman da su ke buga wasannin a halin yanzu, sannan kuma su ga tim din da zai samu nasarar lashe wanan kofin.

Sannan kuma  kudin Naira 250,000 za a kasa su ne ga ’yan wasan wadanda su ka fi samun maki na daya da na biyu da na uku. Sannan kuma su ma alkalai na wasan masu hura usur su ma za a duba wadanda su ka fi sanin dokokin wasannin su ma na daya da na biyu da na uku.

Sannan kuma a dawo kan masu tsaron gida su ma a samu na daya da na biyu  da na uku, domin kasafta mu su wadannan kudi a tsakaninsu.

A nasa jawabin a wajan gudanar da wadannan wasannin, Nasiru Ahamad, shugaban kungiyar alkalai na wasannin kwallon kafa na jahar Katsina, ya cigaba da cewa ne, lallai sun samu cigaba ta fannin wassani kwallan kafa a jihar Katsina.

Sai dai su na fama da matsalar rashin wadan da za su cigaba da horar da ’yan wasan kwallon kafar na jihar katsina tun daga daga kasa har zuwa sama.

Shi kuma tsohon kaftin na kulab din Gangarawa United da ke Malumfashi, Sani Rabiu, cewa ya yi, za su tsaya tsayin-daka domin ganin an kara samun cigaba ta fannin wasannin kwallon kafa a garin Malumfashi da kewayenta bakidaya tare da fatan alheri a wajan samun zaratan ’yan wasan kwallon kafa a cikin wadannan kulab-kulab da ke buga wasannin a halin yanzu.

A cigaba da nasa jawabin Abdulrazak Bishir, mai horas da ’yan wasan kulab din unguwar Gangarawa da ke Malumfashi, ya kara da cewa, ya na matukar farin ciki bisa ga yadda ya ga shuwagabannin wadannan kulab-kulab da ke garin Malumfahi sun hada kawunansu tsaf, domin gudanar da wannan gasar da Abdullahi Kabir [Deko]  ya sanya wa ’yan wasan na garin Malumfashi domin ya kara mu su ’yan wasan azama  a game da gudanar da irin wadannan wasannin kwallon kafa a Malumfashi da kewayenta bakidaya.

Sannan kuma kulab din da ya samu nasarar lashe wannan kofi ya kara samun daukaka, sannan kuma ’yan wasan da su ka dama dakaru a cikinsu su amfana da wadannan kudade da a ka sanya mu su.

Mamuda Lawal Malumfashi, wanda shi ne sakataren offishin yankin Malumfashi da Kafur da Kankara  a jihar ta Katsina a wajen gudanar da wasannin kwallon kafa na wannan yankin, ya cigaba da cewa ne zai yi iyakar bakin kokarinsa a wajen hada kawunan shuwagabanin kungiyoyin ’yan wasan wannan yankin na Malumfashi da Kafur da Kankara, domin su cigaba da gudanar da wadannan wasannin kwallon kafa a kokarin Abdullahi Kabir (Deko} na bunkasa wasanin kwallon kafa na wanan yanki.

Sannan ya isar da sakon godiyarsa ga gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da ya gyara mu su filin wasan kwallon kafa na garin Malalumfash, ya na mai fatan Allah ya yi ma sa jagoranci a wajen mulkin al’ummar jihar Katsina.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: