Connect with us

MANYAN LABARAI

Nijeriya Ta Janye Jakadanta Daga Afirka Ta Kudu

Published

on

Nijeriya ta janye jakadanta da ke Afirika ta Kudu, wato Amsada Kabir Bala, yayinda ta kuma fice daga taron tattalin arzikin duniya da aka fara gudanarwa a birnin Cape Town a wannan Laraba saboda hare-haren da ake kai wa ‘yan kasarta.

Gwamnatin Nijeriya ta kuma bukaci biyan diyya ga ‘yan Nijeriya da aka kashe, sannan aka kwashe dukiyoyinsu a hare-haren kyamar baki a Afrika ta Kudu.

Gwamnatin ta dauki matakin janye jakadanta ne a wani taro da ya samu halartar shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama a fadar gwamnatin kasar da ke birnin Abuja.

Tuni kasashen Congo da Rwandada Malawi su ma suka janye daga taron tattalin arziki na duniya da ke gudana a Afrika ta Kudun saboda wannan farmakin na kyamar baki a kasar.

A bangare guda, gwamnatin Nijeriya ta jibge jami’an tsaro kan kadarorin Afrika ta Kudu da ke fadin kasar nan, sakamakon yunkurin matasan kasar na kai wa kadarorin harin ramuwar gayya, yayinda aka rufe katafaren kantin nan na Shoprite da ofisoshin sadarwar MTN mallakar Afrika ta Kudu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!