Connect with us

LABARAI

Shugaban NIS Ya Tabbatar Da Amincin Sabon Fasfon Nijeriya A Ko Ina Cikin Duniya

Published

on

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS), Muhammad Babandede, ya sake jaddada wa al’umma cewa ingantaccen sabon fasfon da aka yi amintacce ne a duk kasashen duniya.
Babandede ya bayyana cewa an magance ‘yar matsalar da aka samu kwanan baya a wurin mahukuntan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, don haka ma ya ce yana amfani da wannan dama wajen gode wa Jakadar kasar a Nijeriya da kuma Jakadar Nijeriya a can kasar.
A sakamakon hakan, Babandede ya fitar da sanarwa ga manema labarai da ke cewa, ana karfafa gwiwar ‘Yan Nijeriya su mallaki lambar katin shaidar zama dan kasa da kuma tabbatar da cewa bayanansu da ke cikin shaidar sun yi dai-dai da na fasfonsu.
Sanarwar wacce jami’in hulda da jama’a na NIS, Sunday James ya rattaba wa hannu a madadin shugaban na NIS, ta yi bayanin cewa abin da ya sa aka hada bayanan katin shaidar zama dan kasa da na fasfon mai aiki na tsawon shekara 10, domin a tabbatar da bayanan shaidar mutum ne bai-daya, kuma hakan ita ce babbar alamar ingantaccen sabon fasfon wanda ake iya samu a shalkwatar hukumar da ke Abuja, sai kuma ofishinta na Ikoyi, kafin daga bisani a fadada bayarwa zuwa sauran ressan ofishoshin hukumar da suka kamata.

Shugaban NIS Muhammad Babandede yana mika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sabon fasfon da aka inganta a watannin bayaShugaban NIS, Muhammad Babandede yana mika wa Shugaban Kasa Buhari sabon fasfon da aka inganta a watannin baya, a tare da su Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne.

 

Wakazalika, sanarwar ta ce ana kara nanata wa jama’a cewa, ana ci gaba da bayar da tsoho da sabon fasfon kuma kowanne yana aiki.
Idan za a iya tunawa dai, a kwanan baya ne hukumar ta NIS ta bullo da sabon fasfon wanda aka inganta da abubuwa na zamani da kuma tsaro domin tabbatar da fasfon Nijeriya ya yi gogayya da na manyan kasashen duniya da suka ci gaba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: