Connect with us

KANNYWOOD

Shugabannin Kannywood Sun Koka Da Shugabancin Hukumar Tace Finafinan Kano

Published

on

 Dangane da ruruwar wuta da a ke samu tsakanin Hukumar Tace finafinan Hausa ta Jihar Kano da kuma wasu daga cikin ’ya’yan wannan masa’anta ta shirya finafinan Hausan, musamman ma wani abu da ya fi jan hankali shi ne, na guda daga cikin masu bayar da umarni, wato Sunusi Oscar, ya sa LEADERSHIP A YAU, ji ta bakin wasu daga cikin shugabannin wannan masana’anta da kuma shugaban Hukumar tace Finafinai na Jihar Kano.

Da farko dai, mun samu tattauna da Shugaban Kungiyar ’yan kasuwar Finafinan Hausa, Alhaji Sani Rainbow, don jin musabbabin cafke mai bayar da umarni, Sunusi Oscar, wanda Hukumar tace Finafinan Hausa ta Kano ta yi, inda ba tare da wani bata lokaci kuma ba, Alkali ya aike da shi gidan kaso.

Rainbow ya alakanta faruwar wannan al’amari kai tsaye a matsayin bambancin ra’ayin siyasa da sauran makamantansu, inda ya bayyana cewa, “mu ba lallai ne mu san dalilan da su ka sanya a ka kama Sunusi Oscar ba, wadanda su ka kama shi, su ne su ka san dalilan da ya sa su ka kama shi, amma dai mu abinda mu ke yin hasashe a kai shi ne, bambanci ra’ayi na siyasa da kuma wasu matsaloli da ke tsakaninsu ne su ka sa a ka kama shi. Dalilina a nan kuwa, idan har a kan wakar Hasashe ne a ka kama shi, to fa wannan waka ta yi akalla shekara uku da fitar da ita kafar sadarwa ta Youtub.

“Haka nan, wakar da a ka yi ta Rai-na-amana, ita kuma akalla ta yi watanni hudu zuwa biyar da fita. Don haka, sai yanzu ne za a ce an taso da wadannan abubuwa, za a dauki mataki a kai. Me ya sa tun lokacin da a ka yi su ba a yi komai a kai ba, sai yanzu? Saboda haka, mu a wurinmu wannan abu da ya faru, ba saboda wadancan dalilai ba ne, illa kawai wasu abubuwa da ke tsakaninsu, musamman na bangaren bambancin ra’ayin siyasa da kuma jam’iyya.”

Shugaban ya cigaba da cewa, wannan Hukuma ta tace Finafinai ta Jihar Kano, mafi yawancin abubuwan da ta ke yi, ta na yin su ne babu tsari, wadanda su ka saba wa doka. Ma’ana, irin abin da a ke kira da kama-karya. Saboda haka, ya kamata wannan Hukuma ta san cewa, yanzu an samu cigaba a fannonin sha’anin shari’a da doka, sannan tuni yanzu kan mutane ya waye.

“Amma abin haushi da takaici, wannan Hukuma, musamman karkashin jagorancin Isma’ila Na’abba Afakallahu, idan dai har ya kasance ka na yin shiri da shi, ka na durkusa ma sa, ka na kuma ba shi girma, to fa zai ba ka dama har a kan wadansu abubuwa wadanda su ka saba wa ita kanta dokar Hukumar, tun da wai kai dan cikin gida ne. Amma da zarar ka kasance a matsayin akasin haka, to fa ka kade a wajensa.

“Misalin da zan bayar a nan shi ne, akwai wani mai bayar da umarni (Producer) mai suna Naziru Danhajiya, shi ma Sunusi Oscar ne mai bayar da umarni a wani fim dinsa mai su Budurwar Zuciya, ya je Kano domin a tantance ma sa wannan fim, a kuma ba shi satifiket. Daga baya sai ya kira shi ya ke cewa da shi, wannan fim nasa akwai kashe-kashe a ciki. Don haka ba zai ba shi wannan satifiket ba.

“Har ila yau, da mu ka tsananta bincike, sai mu ka gano cewa, dalilin kadai shi ne, saboda Sunusi Oscar ne ya ba d a umarni a wannan fim, domin kuwa babu wani wuri da wata ko wani ya yi amfani da wuka ya caka wa wani a wannan fim da ya ce akwai kashe-kashe a cikinsa.

“Kazalika, Afakallahu ya na wuce gona da iri ko hurumi na bangaren da ya shallake hukumar da ya ke jagoranta, dalili kuwa, akwai ire-iren wadannan hukumomi a mataki na kasa, wanda duk wani wanda ke son yin fim, sai ya je ya samu satifiket a wannan mataki na kasa, sannan idan shi ba dan Jihar Kano ba ne, idan ya na da bukatar sayar da finafinansa a Kanon, wajibi ne ya je ya yi rajista da wannan hukuma ta tace Finafinai ta Jihar Kano, idan kuma ba shi da wannan bukata, ya na iya sakin finafinansa tare da ya nemi wani izini a Kano ba. Don haka kuma, ba shi da wani hurumi na bincike ko hana wani daukar wannan fim nasa ya kai Kano.

“Haka nan, abin da ya kamata ya yi a nan shi ne, ya shiga kasuwa ya kama duk wani wanda ya samu ya na sayar da wannan fim ko wanda ya dauko daga wani wuri ya kawo wannan kasuwa. “Akwai wani lokaci da na yi wani fim a Kaduna, duk kuwa da cewa ni ba dan Jihar Kano ba ne, kwatsam, sai ga shi an kawo min sammace cewa, wai na fitar da fim ba tare da Hukumarsa ta tantance wannan fim din ba. Daga nan ne na aike ma sa da cewa, ni fa ba dan Kano ba ne, ba ni da ofis a Kano, sannan babu wani hurumi da na ke da shi na hana wani daukar wannan fim ya kai Kano. Saboda haka ba ka da wani hurumi na kawo min wannan sammace,” a cewar Sani Rainbow.

Wakazalika, a cewar Shugaban, “Afakallahu na da wasu alkalai da ya ke hada baki da su, da zarar an kawo ka a na zargin ka da wani laifi, sai kawai su tura ka kurkuku, su ce sai an kawo shaidu don kawai a ci mutuncinka. Na’abba ya sha yi wa mutanenmu haka. A karshe kuma ta tabbata cewa, ba su da wani laifi, amma kafin sannan idan mun nemi a ba mu belinsu, sai a hana mu har sai an dangana da su gidan yari.

“Haka zalika, ya kamata Hukumar tace Finafinai ta Jihar Kano, ta san cewa, kowace Jiha cin gashin kanta ta ke yi, don haka don na yi fim dina a Kaduna, zan iya sakin sa a can, sannan ba ni da wani hurumi na hana wani ya dauko wannan fim ya kai shi duk Jihar da ya ke so ya kai, illa iyaka wanda duk ya dauki wannan fim ya kai inda ransa ya ke so, idan an tashi bincike ko tuhuma, shi za a nema ba wani daban ba. Amma saboda kama-karya haka kawai ka na zaune sai a turo ma ka da sammace, dalili kuwa, a tsari da ka’ida na doka, a duk inda kotu ta kira ka, to fa wajibi ne ka je. Sannan manufar kadai ita ce, a ci mutunka tun kafin a gane ka aikata laifin da a ke zargin ka da shi ko ba ka aikata ba, kamar yadda ya hada baki da alkalansa su ke yi.

“Ko wani shugaban tace kinafinai da a ka taba yi a Kano, Abubakar Rabo, duk da irin kama-karyar da ya yi, idan har bai kama ka da fim a cikin Kano ba, ba ya taba daukar sammace ya kaiwa wanda ke wajen Jihar ta Kano, sai Afakallahu, dalilinsa kuwa shi ne, shi dan wannan masana’anta ne, ya san duk wani wanda ke ciki da wajenta.

“Bari na sake bayar da dan wani misali, kamar shi Sunusi Oscar da a ka ce ya fitar da wasu wakoki ne wadanda a ke rawa a ciki masu alaka da badala, kamar yadda Oscar ya bayyana cewa, shi wannan fim ko waka ba nasa ba ne, illa kawai umarni da ya bayar, sannan kuma a Abuja a ka dauke shi, ba a Kano ba, sannan ya na kammala aikinsa, a ka biya shi ya kama gabansa. A nan ka ga idan har za a kama wanda ya ba da umarni, ba wanda ya shirya ba, ya kamata har wanda ya dauki bidiyon ka kamo.”

Shugaban ya kara da cewa, “akwai wani fim da shi wannan Shugaban Hukumar tace Finafinai ta Jihar Kano (Afakallahu), ya shirya shi da kansa, mai suna ‘Masu-Gudu-Su-Gudu’, a cikin wannan fim nasa, abin da a ka aikata ko shakka babu ya fi badala, don kuwa ayoyin Alkur’ani a ka dauka daga cikin Fatiha a ka karanta a wulakance, ba kamar yadda Allah (SWT) Ya saukar da ita ba, a ka yi isgilanci a ciki. Saboda haka, akwai shugaban amintattu na tace wadannan Finafinai na Jihar, Malam Bazallahi Sheik Nasiru Kabara, da ya ga irin yadda a ka aikata irin wannan aika-aika, sai ya ce idan mu ka bar wannan fim ya fita a haka, mun ci mutuncin Alkur’ani, don haka a je a gyara a bangaren Hukumar tace Finafinai na kasa, nan Musulmin da ke ciki su ka ce wannan ko kadan bai dace ba, a koma a gyara.

“Kazalika, da a ka dawo a ka fada ma sa, sai cewa ya yi, ai wai kwaikwayon Namadi Sambo a ka yi a yayin da ya ke karanta Fatiha. Wallahi haka ya saki wannan fim da wannan babbar barna a ciki. Don haka, da wanda ya bata ayar Alkur’ani ya yi ma ta wulakanci da kuma wanda ya yi raye-rayen badala, wanne ne a cikin su ya fi aikata barna? Har yanzu wannan fim na nan ya na yawo a cikin kasuwa tare da wannan mummunan barna a cikinsa. Kenan, wannan na nuna cewa, babu abin da ke tattare da Afakallahu, wanda ya wuce tsantsar son rai da kuma son zuciya. Shi ya sa ba mu boye ba mu ke cewa, ba wannan masana’anta ce a gabansa ba, illa son girma da kuma son a rika zuwa a na yi ma sa bambadanci.

“Bugu da kari, Youtub wata sabuwar hanya ce ta fitar da fim ko wakoki, a lokacin da a ka yi doka ta kasa da kuma wadda a ka yi a Hikumar tace finafinai ta Jihar Kano, babu inda a ka yi maganar Youtub. Sannan, babu inda a ka yi maganar Youtub a wata Jiha, a’a Youtub ya na nan a ko’ina a fadin duniya. Ma’ana, za ka iya yin wani abu naka da ko’ina ka ke a duniya ka dora a wannan zaure na Youtub. Haka nan, idan su na so su kawo maganar Youtub, to fa wajibi ne su koma su gyara dokokinsu, sanya a ciki cewa, ba ka da ikon sanya wani abu a Youtub, har sai sun tantance shi.

“Ko jiya na ga Darakta Janar na harkokin Finafinai da bidiyo na kasa, ya saki wani bidiyo a zauren sada zumunta cewa, ba su da wata doka wadda ta yi magana a kan Youtub, sannan magana ta doka kuma Majalisar Dokoki ce ke yi, ba Shugaban Hukumar tace Finafinai na Jihar Kano ba, don kuwa Youtub, ba kasuwar Jihar Kano ba ce, kasuwa ce ta duniya bakidaya.

“Babu shakka, akwai kishin-kishin na cigaba da kama mutanenmu, baya ga Sunusi Oscar da a ka kama a halin yanzu, dukkanin alamu na nuna cewa, ba za a yi ma na adalci ba. Kazalika, da Hukumar tace Finafinai da kuma mu, idan mu ka tsaya a gaban kotu, cewa a ka yi wannan kotu ta yi adalci, domin kuwa za ka iya kai gwamnati kara, gwamnati kuma za ta iya kai karar ka. Amma babban abin da ya daure ma na kai shi ne, wai sai ga shi Shugaban Hukumar tace Finafinai na Jihar Kano ya gana da alkalai guda uku, sannan ya dauka ya dora a zaurensa na sada zumunta, ya na nuna wa duniya. To, ka ga a nan ina maganar yin adalci?

“Saboda haka, za mu iya yarda da cewa, zai iya kama duk wani wanda ransa ke so, tun da ya riga ya hada kai da wadannan alkalai, wanda a ka’ida dacewa ya yi a ce, wadannan alkalai ba a bangarensa su ke ba, ba kuma a namu bangaren su ke ba, zaman kansu su ke yi. Har wa yau, kaf cikin jerin sunayen da a ka bayyana cewa, ya na so ya kama su, babu guda wanda ya ke yin shiri da shi ko su ke yin jam’iyya daya ko kuma ya ke zuwa ya tsuguna ya gaishe shi. Shi ya sa wannan zargi namu ya tabbata. Shi kansa Sunusi Oscar, mun kai wata guda mu na jin kishin-kishin cewa, za a kama shi, hakan kuma ta tabbata. Yanzu kuma, akwai yiwuwar kama Naziru Sarkin waka, Musbahu Ahmed, Alan Waka, Adam A. Zango da sauran makamantansu kamar yadda mu ke jin kishin-kishin, ko da laifi ko babu wani laifi. Bukatar dai ita ce, da zarar an kamo su, kafin a kai ga yin bincike, an aike da su kiri-kiri,” in ji Sani Rainbow.

“Yanzu haka, tuni shirye-shirye sun yi nisa, na daukar irin matakan da su ka dace, illa matsala guda da ta sanya mu a gaba, ita ce ta rashin yin zabubbuka na shugabannin da ke rike da wannan sana’a ta fim, kamar Kungiyar MOPPAN da kuma wadda na ke shugabanta, duk kusan lokutansu ya kare, yanzu haka mu na nan mu na kokarin yadda za a yi mu yi wadannan zabubbuka. Da zarar mun kammala kuma, za mu hada karfi da karfe don kokarin ceto wannan masana’anta daga kangin tattalin arziki da kuma yanayi irin na kama-karya da a ke yi ma na, sannan a kungiyance yanzu haka, mun dauki lauyoyi wadanda za su je su kare Sunusi Oscar a gaban Kotu,” a cewar Shugaban ’yan kasuwar da ke sayar da finafinan Hausa.

A hannu guda kuma, Sakataren MOPPAN reshen Jihar Kano, Alhaji Salisu Ofisa, shi ma ya tofa nasa albarkacin bakin dangane da wannan dambarwa ta kama mai bayar da umarni a Finafinan Hausa, Sunusi Oscar, wanda Hukumar tace Finafinai ta Jihar Kano, ta yi a makon da ya gabata.

Ya ce, “abin da ya faru dai shi ne, an kama Sunusi Oscar, a ka kai shi wajen ‘yan sanda. A wannan lokaci ya kira ni, ya sanar da ni abin da a ke ciki. Daga nan ne kuma kai tsaye a ka wuce da shi zuwa kotu da ke Rijiyar Zaki. Shi kuma wannan alkali ya aike da shi Kurkuku.

Har ila yau, a cewar Ofisa, “laifin da a ke zargin Oscar da shi guda biyu ne; na farko, akwai wata waka wadda a ka yi a wani fim wanda tuni a ka tantace fim din (mai suna Hasashe), ya kuma dauki (fiye da) tsawon shekaru uku da yin sa, amma tun a wannan lokaci, akwai wasu gurare da a ka nemi cewa, a dan yi wa kwaskwarima.

“Sannan magana ta gaskiya ba Sunusi ne mai wannan fim ba, kadai abinda ya yi shi ne bayar da umarni (Directing), amma ba mu san yaya a ka yi da mai fim din ba, ba mu kuma san yadda a ka yi da mai wakar ba.

“Haka nan, akwai wata waka ita ma wacce a ka nade ta a Abuja, wacce ita ma ba shi ne mai wannan fim ba, ba kuma shi ne mai wakar ba, kadai umarni ya bayar. Saboda haka, wadannan abubuwa guda biyu alkali ya tuhumi Oscar da su, ya kuma ba shi amsa da cewa, shi dan kwadago ne, amma hakan bai hana alkalin aika shi gidan kaso ba.

“Haka zalika, abu na gaba shi ne, maganar dora waka ko fim a Youtub; Hukumar tace Finafinai ta yi ikrarin cewa, duk wanda ya dora fim ko waka a Youtub ko Instagram za ta kama shi ta hukunta.

“Wannan shi ne irin mawuyacin halin da masana’antar shirya Finafinan Hausa ta shiga. Saboda haka, masu sana’a a wannan masana’anta ta fim din Hausa, sun fahimta, sun kuma gane cewa, wannan abinda a ka yi wa Sunusi Oscar, abu ne da ya ke da alaka da siyasa. Wannan shi ne abinda mu ka sani, kuma a kansa mu ke.

“Dalili kuwa, Hukumar tace Finafinan Jihar Kano ba ta da wani hurumi na tantance dukkanin Fim ko waka da a ka dora a kan Youtub, saboda duniya ce ba Kano ba. Don haka, tun da mafiya yawan ‘yan Kano su ne ke harkar Finafinan Hausa, idan su ka dora wani abu a Youtub, za a iya zuwa gidajensu cikin iyalansu a ci mu su zarafi, amma dan Kaduna babu ruwan Hukumar tace Finafinan Jihar Kano da shi. Abinda mu ka lura da shi yanzu shi ne, a na so a kara kashe masana’antar ne bakidaya ne.

“Saboda haka, ni a matsayina na Sakataren Kungiyar MOPPAN ta Kasa, Ina sake jaddada cewa, babu wata doka da ta bayar da damar kama ko hukunta wanda ya dora bidiyon waka ko Fim a Youtub, Instagram da kuma setilayet, amma ba mu san ko akwai wata doka da a ke son kirkiro da ita don a ci mutuncinmu ba. Kazalika, mu ma a namu bangaren na shugabanci za mu yi dukkanin abinda ya kamata bisa doka da tsari, don kawo karshen wannan wulakanci da a ke yi ma na, domin kwatar kanmu da kuma ita kanta sana’ar.

“Har wa yau, wallahi shugabancin Kannywood ba zai taba barin wannan wulakanci da a ke yi ma na ba, domin kuwa akwai dimbin al’umma da ke cin abinci a cikinta, sannan Youtub din nan wata kafa ce ta yin ciniki, kuma mutane na yin amfani da ita don sayar da finafinansu a duniya.”

“Wakazalika, a matsayina na shugaba, ba ni da tabbacin rade-radin da a ke yin a kama wasu daga cikin mutanen wannan masana’anta, amma dai abinda na sani shi ne, an riga an dora wani dan-ba, wanda zai tsorata masu yin wannan sana’a, su ce watakila abin da ya samu Oscar, zai iya samun Naziru Sarkin Waka ko Misbahu ko da sauran makamantansu, kamar yadda a ka lissafa. Sannan kafatanin al’ummar da ke cikin wannan masana’anta sun firgita kwarai da gaske da Hukumar tace Finafinai ta Jihar Kano tare da jin tsoron rusa tanadin da a ka yi wa Matasa su ke cin abinci a wannan Masana’anta.

“Sa’annan matsalar da a ka samu ta bambance-bambancen siyasa da a ka samu a zaben da ya wuce, a namu ganin kamar shi ne ya sa a ke kokarin rusa masana’antar bakidaya, don kuwa magana ta gaskiya, an yi siyasa mai zafin gaske wadda ta shigo cikin wannan masana’anta kai tsaye, wasu su ka yi nan, wasu kuma su ka yi can. Kazalika, ga kuma wake-wake da a ka rika faman yi daga bangare daban-daban, wanda da ma ya kamata a ce da bangaren gwamnati da na wanda ba na Gwamnati ba, su san cewa, da ma haka siyasa ta gada, kowa ya rungumi kaddara a dawo a sake dinkewa, a zama abu daya.

“Haka zalika, Hukumar tace Finafinai ya kamata ta lura da abubuwa guda biyu da ya sanya a ka kafa ta, na farko ta rika tantance abubuwan da mu ke fitarwa a cikin Jihar Kano, domin ka da ya ci karo da al’ada da kuma addininmu, sannan gwamnati ta kafa wannan Hukuma ta tace Finafinan Hausa, domin ta kara habaka harkokin wannan Fim. Amma abin haushi duk an sauka daga wannan layi, an shiga wani layi na daban. Ko shakka babu, wadannan su ne kashin bayan kafa wannan Hukuma tat ace Finafinan Hausa, duk kuma wani abu da wannan Hukuma za ta yi bayan wannan, sai dai kawai a yi domin a na son a cimma wata manufa ta siyasa ko kuma ta zamantakewa da a ke yi.

“Sannan ya kamata a lura da cewa, idan misali na yi Fim dina a Zamfara, Ina so kuma ya ci kasuwa a Kano, to fa wajibi ne na kawo Fim dina a tantance shi a Kano, amma idan na tabbatar da cewa, babu wani dalili da zai sa a kawo Fim dina Kano, a nan fa ba ni da wata alaka da Hukumar tace Finafinai ta Jihar Kano.

“A karshe, shawarar da na ke so na baiwa wannan Hukuma ta tace Finafinai ta Jihar Kano shi ne, su tsaya a doron tsarin dokokin da aka kafa wannan Hukuma a kai, haka nan ta tsaya a doron dokokin gidanta, duk abin day a saba da dokokin gidanta, su ajiye shi a gefe guda. Tun da na tashi nake yin aikin Gwamnati, abin da na sani shi ne, a kullum za ka rika kokarin kiyaye wannan dokar ta inda kake yin aikin, babu yadda za a yi lokaci guda ka tashi ka kirkiro wata doka daban wadda ta ci karo da wannan doka ta cikin gidan, kuma ka dage a kai cewa sai an aiwatar da ita.

“Kazalika, shawarata ga Gwamnati, idan ma ba san abin da ake yi ba, ya kamata tsakaninmu da wannan Hukuma ta tace Finafinan Hausa, su ja hankalinsu cewa, su tsaya a iya huruminsu, mu ma mu tsaya a namu hurumin na Shugabanci, idan a ka yi haka za a fi samun daidaito da fahimta da kuma cin moriyar juna a Jihar Kano. Sannan ya kamata a kalli barazanar da ke cikin wannan Masana’anta, musamman ta fuskar barazanar da wannan Hukuma ke yi wa wannan Masana’anta, wadda dimbin Matasa ke cin abinci a cikinta, ana yi musu barazana, ana so a lalata Masana’antar baki daya.

“Ya kamata kuma, a lura da cewa ita harkar Fim, ba kamar tabarma ba ce da za a ce an nade ta, an daina zama a kanta har abada, a’a, ta riga fa ta zo, sannan ya zama wajibi Gwamnati ta inganta ta, ta kuma kyautata ta, ta yi mata wani gata, musamman ganin irin halin da Matasa kan samu kansu na yin garkuwa da mutane da sauran laifuka iri daban-daban. domin kuwa, da zarar sun rasa wannan sana’a, abu na gaba da za su yi shi ne, kwakwalsu ta fara fada musu cewa, ku yi kaza, ku yi kaza.

“Wallahi, wallahi, wallahi, ni ne Sakataren MOPPAN, na yi wa yara rijista a wannan Masana’anta, sama da Milyan daya kuma kowanne ina da Fam dinsa, daga kan masu shirya Finafinai zuwa wadanda suke fitowa a ciki, da wadanda suke yin abinci da sauran su.

“Don haka, wannan ba karamin kuskure ba ne, Gwamnati ke son yi na ruguza wannan tsari, ko da kuwa babu riba a cikinsa, amma dai an killace Matasa a wani wuri daban na sana’a. A takaice, wannan ita ce shawarar da na ke so na ja hankali Gwamnati a kai.”

Wakilinmu ya kira shugaban hukumar tace finafinai na Kano, Isma’ila Afakallahu, amma bai dauki waya, kuma ya tura ma sa da sakon waya bai bada amsa ba har zuwa lokacin tattarawa da wallafa wannan rahoto. Amma idan mun samu martaninsa daga bisani, za mu kawo mu ku bangarensa da hujjojinsa bisa zarge-zargen da ake yiwa hukumar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: