Connect with us

KASUWANCI

Afrika Ta Kudu: Kantin Shoprite Ya Yi Tir Da Hari Kan ‘Yan Nijeriya

Published

on

Sakamakon hare-haren kwanan nan da ake kaiwa ‘yan Afrika, musamman ma ‘yan Nijeriya da suke da zama a kasar Afrika ta kudu, da kuma harin ramuwar gayyar da ya biyo baya a kan ‘yan kasar ta Afrika ta kudu da suke da zama a nan Nijeriya, kamfanin kantin nan mai suna, Shoprite Nigeria, ya yi suka da kakkausar murya a kan duk wata fitina ta nuna wariya da kuma tsokana a kan al’ummar sauran kasashe a duk inda suke cikin Duniyar nan.

Sanarwar da jagoran kantunan na Afrika ya fitar a ranar Laraba a Legas, tana cewa abin damuwa ne matuka da ganin yanda ake aukar da rigima a kan mutanan kasashen waje a kasar ta Afrika ta kudu, wanda hakan ya janyowa al’ummar kasar Afrika ta kudu da suke zama a Nijeriya tsangwama.

“A matsayinmu na babban kamfani wanda yake da asali da kuma tushensa a Afrika, ya kuma dauki dubannan ‘yan Afrika aiki, musamman ma kan yanda yake yin aiki tukuru a wajen ganin an sauke farashin kayayyakin bukatu a kasashe 14 da suke a wajen kasar ta Afrika ta kudu. Babu shakka mun fi kowa son ganin ana zaune da juna lafiya tare da hadin kai, a kan haka mun kosa mu ga an kawo karshen wannan tashin-tashinan a duk inda ake yenta a nahiyar ta Afrika.

“Shoprite Nigeria, yana yin roko ga al’umma baki-daya na kasar Afrika ta kudu da kuma Nijeriya da su kare mutuncin ‘yan adam da tsaron lafiyar duk wanda yake da zama a cikin kasashen na su.

“A shirye muke da mu ci gaba da huldarmu ta kasuwanci da duk abokanan kasuwancinmu, da kuma yin amfani da masu ruwa da tsaki wajen daukan tsauttsauran mataki a kan duk masu aikata laifuka da tsokanar ‘yan wasu kasashen da suke zaune a tsakaninsu. A kan hakan, muna nuna kakkausar sukarmu a kan duk masu son nuna wariya,” in ji sanarwar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: