Connect with us

WASANNI

Ban Yi Nadamar Zuwa Manchester United Ba – Sanchez

Published

on

Dan wasan gaba Aledis Sanchez ya ce ko kadan bai yi nadamar kulla kwantiragi da Manchester United ba, sai dai kawai bai samu cikakken lokacin buga wasa ba yadda ya kamata ba a zamansa a kungiyar ta Ingila.

Sanchez dan kasar Chile mai shekaru 30 wanda ya koma Inter Milan a matsayin aro cikin watan jiya bayan shafe watanni 19 a Old Trafford, shi ne dan wasa mafi daukar albashi a Manchester United inda ya ke karbar yuro dubu dari 4 kowanne mako amma kuma kwallaye 5 kacal ya iya zurawa a wasanni 45 da ya dokawa United din tun bayan sayo shi daga Arsenal cikin watan Janairun shekara ta 2018.

A cewar Sanchez dalilin da ya baro shi daga Arsenal zuwa Manchester United a wancan lokaci bai wuce ganin ya lashe kofuna a gasa daba-daban ba, amma sai ya rasa samun abin da ya yi tsammani.

Tun bayan da Arsenal da sayo Sanchez daga Barcelona kan yuro miliyan 30 a shekarar 2014, ya zura mata kwallaye 80 cikin wasanni 166 kafin sayar da shi a 2018 kuma ya kasance jigo a nasarar da kungiyar ta samu na lashe kofin kalubale na FA.

Sai dai sauya shekar dan wasan ana ganin ta haddasa masa koma baya, ko da dai yayi rawar gani a bangaren kasarsa yayin wasannin Copa America da suka gudana a Brazil inda ya zura kwwale hudu a gasar.

Duk da haka Sanches ya bayyana cewa yana fatan zai cigaba da kokari a sabuwar kungiyarsa kuma yana fatan watarana zai sake komawa Manchester United domin cigaba da buga mata wasa kamar yadda shima kociyan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer ya bayyana cewa har yanzu Sanchez zai iya taimakawa kungiyar tasa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: