Connect with us

KASUWANCI

Gombe: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 21 Bisa Fashi Da Damfara A Yanar Gizo

Published

on

‘Yan sanda a Jihar Gombe sun ce sun kama mutane 21 da suke tuhuma da aikata addaban mazauna garin Gombe.

Da take Magana da manema labarai a hedikwatar rundunar, Kakakin rundunar a Jihar, SP Obed Mary Malum, cewa ta yi wadanda ake tuhumar an kama su ne bayan samun wasu tabbatattun bayanan sirri a kansu.

Ta ce, wani mai suna, Gabriel Michael Alli, dan shekaru 18, da ake da zama a Abguwar PZ ta Gombe, an kama shi ne a ranar 30 ga watan Agusta, a bisa tuhumarsa da aikata damfara da zamba a yanar gizo.

Ana zarginsa da damfarar wata mai suna, Deborah Tanko, 40, wacce take da zama a waje guda da shi ta hanyar yin amfani da Kwamfuta ya dandatse asusun ajiyarta na banki inda ya wawashe mata naira 187,100.

SP Malum ta ce, shaidun da aka kama a tare da wanda ake tuhumar sun hada da wayar GSM, tsabar kudi naira 10,000, talalma sawu biyu, da tufafin da kudinsu ya kai naira 33,000 wadanda ya saya daga kudin da ya sata a asusun.

Kakakin ta ‘yan sanda ta kara da cewa, a ranar 21 ga watan na Agusta, jami’an ‘yan sanda na sashen masu yaki da ‘yan fashi da makami sun kama wani mai suna, Yusuf Adamu, 20, da ake wa lakabi da, Baban Lauje; Ibrahim Mohammed, 19, da ake wa lakabi da, Babangida; Abubakar Zubairu, 20, da ake wa lakabi da, Flabour; da Usman Shuaibu, 20, da ake wa lakabi da, Dan Bakuwa.

An kama su ne a bisa tuhumarsu da aikata laifin hada baki da aikata fashi da makami, karban kayan sata a cikin garin Gombe.

‘Yan sandan suka kuma ce, wadanda ake tuhuman sun amsa laifin aikata ayyukan fashi da makami masu yawa a cikin garin na Gombe.

Shaidun da aka samu a tare da su sun hada da karamar bindiga kirar gida, wayoyin hannu guda 22 kala daban-daban da suka kwata daga hannun mutane, kwamfutar Laptop guda hudu, na’urar DBD, wukake guda biyu, adduna guda biyu, wani karfe guda daya, takobi guda daya, gariyo guda biyu, da kuma tufafin Soja guda.

Malum ta ce wasu daga cikin wadanda ake tuhumar sun amsa aikata laifinsu ana kuma kan gudanar da bincike, ta kara da cewa nan ba da jimawa ne ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin a hukunta su.

Ta bukaci al’umma masoya son zaman lafiya da su ci gaba da baiwa rundunar ‘yan sandan hadin kai ta hanyar ba su bayanan sirri da za su taimaka wajen kawo karshen aikata miyagun laifuka a cikin Jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!