Connect with us

MAKALAR YAU

Kokarin Ciyar Da Kanmu

Published

on

Ba wata kasa a duniya da za ta sami cikakken ci gaba idan ba ta iya ciyar da kan ta ba. Kasashen da su ka ci gaba a duniya su na iya ciyar da kansu, abinda ya baiwa mutanensu damar mayar da hankulansu wajen sauran al’amura na ci gaba.

Duk kasar da ta fi karfin abinci, mutanenta za su kasance fafutukarsu ta yau da kullum ba ta karewa kawai a wajen neman abinci, za su sami sukuni  na bin wasu abubuwa na rayuwa. Bayan alaka da tattalin arziki kuma, wadatar abinci na da matukar tasiri wajen lafiyar al’umma, musamman mata masu ciki da yara yadda za su kaucewa cuce-cuce wadanda ke haifar da tauyewar jiki da basira ko kaiwa ga mutuwa.

Allah ya albarkaci Nigeria da filayen noma, albarkatun ruwa da yawan jama’a wanda idan da ana amfanarsu yadda ya kamata, ba maganar ciyar da kai ba, hatta ilahirin Afirka ta yamma sai mun iya ciyar da ita.

Daga gefen Sahara zuwa gabobin kogunan Kwara da na Binuwai, ka gangara zuwa dazukan kudancin Nigeria har ka kai gabar teku, kasar nan na samar da mahimman kayan abinci na ci da kasuwanci kama daga shinkafa, alkama, masara, rogo, cocoa, roba, katako da sauransu. Shekarun baya kasar Indonesia ta zo kasar nan ta karbi irin kwakwar manja domin shukawa da kokarin ganin sun fara noma ta yadda za su iya siyarwa kasashen duniya.

Zuwa shekarar 2012 sai ga shi Indonesia ta zama kasa ta farko a wajen samar da man ja a duniya, domin ita ke samar da kashi 35% na yawan man ja a duniya, kuma su na da filayen nomanta da su ka kai kimanin hekta miliyan 12. Tun a wajajen shekarar 1870 Nigeria ta kasance kasa ta farko a duniya wadda ke samar da mafi yawan man ja, amma a yanzu mu ne na biyar saboda rashin habaka noman yadda ya kamata.

Wajibi ne kasar nan ta mai da hankali a kan harkar noma idan mu na burin samun ci gaba, kuma abinda ya faru a shekaru ukun da su ka gabata, wato yadda gwamnatin Buhari farfado da noman shinkafa ya isa ya bude mana idanuwa wajen gane hakan kadai zai iya kawo mana gagarumin canji.

Domin mun karbe ja-gaba a noman shinkafa a Afirka daga hannu kasar Misra, sannan farashin ta ya sauka a cikin gida kuma ta wadatu a kasuwanni. An dade ba’a sami kakar da kayan abinci su ka yi sauki irin wannan lokaci sakamakon mai da hankali ga noma da aka yi a shekaru uku da su ka gabata.

Bayanin shugaba Buhari a satin da ya gabata na baiwa Babban bankin tarayya umarnin hana duk yan kasuwa da ke shigowa da abinci kasar nan canjin kudaden kasar waje, abu ne wanda za a iya yabawa matuka amma idan da a ce yanayin kasar mu ba haka ya ke ba, amma kasancewar tsarin da gwamnatin ke da shi a kasa a kan harkar noma a gurgunce ya ke, aiwatar da wannan tsari na hana canji kudin ba zai haifar wa kasar da talakawanta da mai ido ba. Idan gwamnati da gaske ta ke wajen bunkasa harkar noma, wajibi ta saka kudaden tallafi ga harkokin noma ga kanana, matsakaita da manyan manoma kafin a fito da irin wannan tsari. Kasashen da su ka ci gaba kamar Amurka wallahi su na iya shiga yakin kasuwanci da duk mutanen duniya domin kawai su kare tallafin noma da su ke baiwa manomansu (mun ga haka a baya), saboda sun hakkake cewar samar da abinci ga al’ummarsu da wanda za su siyarwa kasashen waje, ya fi komai mahimmanci wajen kare mutanensu fiye da duk wata harkar kasuwanci.

Dalilin da ya sa na ce tsarin tallafin wannan gwamnati ga harkar noma a gurgunce ya ke shine, karancin basuka da ake iya baiwa manoma da kuma rashin wata hukuma wadda za ta rika kula da samar da kayan noma da kasuwancinsu yadda manoma za su iya samun kwarin gwiwa wajen samun ingantattun iri da za su shuka sannan bayan girbi sun san inda za su kai kayan amafanin gonarsu a siya kai tsaye. A wannan kakar manoma na kuka da karancin farashi na amfanin gona da kuma cikar da kasuwanni su ka yi da amfani gona amma babu masu siye.

Idan da akwai waccan hukuma, ita za ta sayi amfani gona kai tsaye daga manoma abinda zai kawo daidaito na farashi a kasuwanni.

A kowanne sashe na kasar nan babu wata kwayar abinci da ake sarrafawa kuma a ke ci a kullum kamar alkama, domin ana sarrafata ta hanyoyi daban-daban. Misali a Kananan hukumomi biyu kacal a jihar Kano, ana cin burodi na kimanin Naira miliyan tamanin a kowacce rana, na nawa ku ke tsammani a ke ci a fadin jihar ko a fadin kasar?

Nigeria na da bukatar kimanin Tan miliyan shida na alkama a kowacce shekara amma abinda mu ke iya nomawa tan dubu goma ne kacal, wato kasa da kaso daya (0.6%) kenan. Cike wannan gibi na abinda mu ke bukata da wanda mu ke iya nomawa ba karamin aiki ba ne wanda za’a iya yi cikin shekaru kalilan. Dole sai gwamnati ta yi hobbasa wajen samar da kudaden tallafi tare da jami’o’in mu su yi bincike na iri da zai dace da kasar noman mu.

Abin takaici duk da maganar da wannan gwamnati ta ke yi wajen harkar noma sai ga shi basu saka sisin kwabo ba wajen tallafawa harkar noman alkama, amma ana kokarin hana yan kasuwa kudaden canji wajen shigo da ita. Idan a halin da ake ciki a ka ce yan kasuwa su sayi dala a kasuwannin bayan fage su siyo alkama, masifar da hakan zata jawo mai girma ce domin farashin alkama zai yi tashin gwauron zabin da ba’a taba gani ba, kuma kuma kayayyakin da a ke sarrafawa da alkamar za su gagari talaka.

A yanayin da kasar ta ke ciki yadda miliyoyi ke ta kara shiga talauchi gami da rashin tsaro da ke dada bazuwa, matukar a ka bari kasar ta tsunduma ciki rashin abinci, hakika hakan na iya kawowa dumokuradiyar kasar barazana. A shekarar 1987 Janar Babangida ya hana shigo da alkama kasar nan, kuma a lokacin muna iya noma tan dubu hamsin a shekara (ninki biyar na abinda muke nomawa a yanzu) kuma cikin dan lokaci kankane mu ka iya noma Tan dubu dari da hamsin zuwa dubu dari da tamanin a shekara (ninki uku) saboda akwai yanayi mai kyau a wancan lokaci.

Amma daga baya, kamar hadin baki, sai a ka kassara noman alkama kasar wanda har yanzu bai farfado ba. Idan shekaru talatin da suka wuce muna iya noma Tan dubu dari da tamanin shin ba abin kunya ba ne a ce a yanzu dubu goma kacal mu ke iya nomawa? Kuma ina dalilin da gwamnati ba ta iya yin hobbasa koda kamar na shinkafa ba ne wajen samar da basukan noman alkamar?

Hakika a bayyane ya ke cewa alkama itace wadda ta fi kowacce kwayar abinci daraja a doron duniya a yau, kuma ja-gaba a nomanta su ne manyan kasashen duniya mafiya karfin arziki wato kasashen China, USA da Russia. A Afirka, Nigeria ba ta cikin manyan kasashe goma da su ka fi yawan noman alkama, ta biyu a yawan noman itace kasar Morocco wadda ke noma kusan adadin da kasar Nigeria ke bukata a shekara na alkama, wato tan miliyan shida.

Mun fi Morocco yawan kasar noma da albarkar ruwa da yawan manoma. Kai hatta kasar Libya, wadda ke cikin yanayi na yaki kuma a cikin sahara, ta noma tan dubu dari biyu a shekarar 2014 (ninki ashirin na baindamu ke nomawa).

Wajibi ne gwamnatin Nigeria idan dai da gaske ta ke a maganar noma, ta farfado da noman alkama a kasar nan ta hanyar fito da tallafi ga manoman alkama, sannan ta sani cewa hana yan kasuwa a wannan gaba samun kudaden canji domin siyo alakama ba zai Haifa mana da mai ido ba a lokacin da muke iya noma tan dubu goma kacal.

Akwai kayan abinci wadanda ba ma hana kudaden canji wajen siyo su ba, ko da hana shigo da su a ka yi kacokan zai taimaki nomansu da kawo wa kasar alfanu, Misali; Idan ka dauki tumatirin gwangwani, gidaje kalilan ne su ka dogara da shi wajen girki saboda kusan ilahirin mutanen kasar nan sun fi amfani da danyen tumatir wajen girki.

Sannan ba ma shigo da danyen tumatiri daga waje don haka idan ka hana shigo da tumatirin gwangwani, hakan zai taimaka wajen ganin masu saka hannun jari sun kafa masana’antun sarrafa tumatirin gwangwani wanda zai samawa matasa ayyuka, ya kuma binkasa noman tumatiri a kasar tare da adana mana kudaden kasar waje da za’a yi amfani da su wajen siyo tumatirin gwangwanin.

Wannan shi ne tsari da zai bunkasa noma da samar da masana’antu a kasar. Amma alkama wajibi ne kafin a tsaurara shigo da ita sai an tabbatar an samarwa yan kasa hanya da ba za ta kara jefa su cikin talauci ba.

Duk abinda ba ma iya shukawa dole a bada dammar shigo da shi amma wanda mu ke iya shukawa, kamar shinkafa babu laifi idan an hana shigo da ita.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: