Connect with us

LABARAI

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe A Sakkwato Ta Yi Watsi Da Karar Dasuki

Published

on

Kotun sauraren kararrakin zaben ‘yan majalisa da na gwamna a jihar Sakkwato ta yi watsi da karar da Abdussamad Dasuki ya shigar gabanta yana mai kalubalantar zaben dan majalisa Alhaji Bala Kokani.

Kokani wanda ya lashe zaben a karkashin jam’iyyar APC ya buge Dasuki na PDP a yayin zaben 2019 da ya gudana. Dan majalisar dai da kotun ta sake tabbatar masa da cewa ya lashe zaben, yana wakiltar Kebbe/Tambuwal a Sakkwato.

Dasuki ta hannun lauyansa, Dr. Garba Tetengi, SAN, ya gabatar da shaidu shida dake nuna cewa akwai magudi a zaben, yiwa masu kada kuri’a barazana da kuma rikici tare da karya ka’idar zabe. Sai dai Lauyan Kokani, Mr. Solomon Alimasunya, da na APC, Nuhu Adamu sun gabatar da shaida guda da ta karyata dukkanin zarge-zargen da ake yiwa zaben a madadin wanda ake kara.

Da yake gabatar da hukunci a ranar Laraba a Sakkwato, Mai Shari’a, Yusuf Muhammad-Ubale ya ce mai shigar da karar ya gaza gabatar da hujja kwakkwara da ke tabbatar da zarge-zargensa.

Jim kadan da hukuncin kotun, Kokani ya yiwa Allah godiya bisa nasarar da ya samu, inda ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu su kuma ci gaba da goyon bayan APC da manufofinta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!