Connect with us

KASUWANCI

Makarantu 1,320 Za Su Ci Gajiyar Tallafin Bankin Duniya A Bauchi

Published

on

Makarantu guda dubu daya da dari uku da ashirin 1,320 da suke fadin kananan hukumomi biyar na jihar Bauchi ne suka samu nasarar cin gajiyar shirin kyautata makarantu na Bankin duniya ta shekarar 2019.

Da yake jawabi bayan gabatar da cek (Chekue) din dubu dari biyar-biyar ga kowace makarantar da ta samu cin gajiyar wannan tallafin, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya shaida cewar sake kudaden wani hanya ce ta kokarin shawo kan matsalolin da suke fuskantar karatun yara kanana a jihar.

Ya shaida cewar gwamnatinsa tunin ta ja damara domin tabbatar da kai makaratun firamare da na sakandari zuwa matakin da suka dace gami da shawo kan matsalolin da suke yi wa makarantun katutu, ta hanyar gine-gine, kwaskwarima wa makarantun, horo da kuma kara horar da malamai domin kyautata sha’anin ilimi a jihar.

A cewar shi, gwamnati mai ci ta maida hankalinta ne wajen shawo kan matsalolin ilimin yara a makarantun gwamnati gami da tabbatar da bayar da ilimi mai nagarta ga kowani mazaunin jihar.

Sanata Bala ya shawarci makarantun da suka ci gajiyar da su tabbatar da yin amfani da kudaden wurin inganta koyo da koyarwa domin kyautata ilimi a makarantu.

Gwamnan ya nemi masu ruwa da tsaki da su bayar da tasu gudunmawar wajen kyautata harkar ilimi, yana mai shaida cewar babu wata al’ummar da za ta ci gaba ba tare da ilimi mai nagarta ba.

A fanninsa, Ko’odinetan shirin a jihar ta Bauchi, Muhammad Datti Umar, ya jero sunayen kananan hukumomin da suka ci gajiyar tallafin da cewar sune, Zaki, Shira, Ganjuwa, Katagum Darazo da kuma Toro, ya ce shirin an tsara ne domin shawo kan matsalolin ilimin yara kanana ta fuskacin kwaskwarima, da kuma gyara makarantu hadi da sauran matsalolin da makaratun ke fuskanta.

Tun da farko, babban sakataren ma’aikatar ilimi na jihar, Alhaji Musa Wadata, ya shaida cewar wannan matakin zai taimaka sosai wa kananan hukumomin da suka ci gajiyarsa.

Ya shaida cewar gwamnatin jihar mai ci ta maida hankalinta wajen shawo kan matsalolin da suke fuskantar ilimi, domin shawo kan matsalolin ilimi a jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!