Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Magungunan Gargajiya Suka Bunkasa A Kasar Hausa

Published

on

Sakamakon irin damuwar da cuta ke yi wa dan Adam ne ko don son nuna buwaya da bajinta da daukaka ya sanya ita fafutukar nema ire-iren magunguna da za su taimaka masa yayi riga-kafi ko maganin ire-iren waɗannan cututtuka ko kuma don nuna fifiko a tsakanin tsarar dama na gaba da shi. A cikin al’ummar Hausawa wannan dalili ne ya haifar da samuwar wadannan nau’o’in mutane waɗanda suka kware wajen bayar da magungunar cututtuka  daban daban, ko kuma dan nuna buwaya da bajinta da kuma daukaka, waɗanda wasun su suka mayar da wannan al’amari a matsayin abinda suka gada iyaye da kakanni. A dalilin haka ne ya sa a ƙasar Hausa a ka raba masu bayar da maganin gargajiya zuwa kashi biyu; wato masu maganin gado da waɗanda ba su gada ba:

Masu maganin gado:

Wannan kashi na masu ba da maganin gargajiya su ne kamar yadda Bunza (2003) ya ce su ne waɗanda suka gaji bayar da magunguna daga wurin iyayensu, kamar yadda su ma iyayen suka gada a wajen na su iyayen. Ire-iren waɗannan mutane sun sami wannan hikimar ce daga wurin mahaifansu. Masu irin wannan magani sun hada da; masu sana’o’in gargajiya na Hausawa kamar:-

-Makera wadanda suke bayar da maganin wuta da kuma tsatsube-tsatsuben da suka danganci wannan sana’a kamar wasan wuta da makamantan su.

-Masunta suna bayar da maganin sarkewar kayar kifi da maganin sanyin jiki da iskokin ruwa da kuma tsatsube-tsatsuben da suka shafi wannan sana’a

-Manoma kuma suna ba da maganin ciwon baya da karfin hali da juriyar yin aiki da kuma tsatsube-tsatsuben noma.

-Mafarauta suna ba da maganin jini da sarkafewar nama ko kashi a makogwaro da kuma tsatsube-tsatsuben da suka da nasaba da  wannan sana’a

-Maharba suna bayar da maganin Iskoki da  kuma Mayu da fargaba da dafi da kauda bara da maganin bindiga.

-Masaka suna ba da  maganin zafi da na dan kanoma.

-Fatake suna bayar da maganin daurin daji da maganin ‘yan fashi da kuma barayi.

-Madora suna bayar da maganin karaya da gocewar kashi da targade da na amosanin gashi.

-Wanzamai suna ba da maganin Jini da na Mayu da na cututtuka da suka bambanta waɗanda kan shafi jikin Jarirai da na yara kanana da manyan maza da mata. Hakanan kuma suna ba da magunguna waɗanda suka danganci tsatsube-tsatsuben da surkulle dan nuna buwaya da daukaka da kuma cutar da  wasu.

-Akwai kuma wasu mutane waɗanda suka gaji bada maganin gargajiya waɗanda suka hada da ‘yar Mai ganye da Magori, sai kuma wasu waɗanda saboda wasu dalilai suka lakanci sanin maganin  wasu cututtuka, wadanda a wasu lokuta za’aji ana cewa maganinnau’in kaza , “ai sai gidan wane” ko kuma “zuri’ar wane ce za a iya samun hakan”.

Waɗanda ba ‘yan gado ba:

Bunza (2003) ya ce akwai wasu mutane waɗanda suke ba da maganin gargajiya, amma su ba su gaji wannan al’amarin daga wurin mahaifansu ba, ba su samu wannan hikimar ba a saboda wasu dalilai misali, a dalilin rashin lafiya, indai mutum ya san maganin irin rashin lafiyar da yake fama da ita ya yi amfani da shi kuma ya sami biyan bukata, da wannan lokacin sai ya rika ba da wannan magani. Ire-iren waɗannan mutanen sun hada da bokaye da Unguwarzomomi da sauransu.

Wasu kan iya samun maganin da za su rika bayarwa a dalilin samun lakanin daga wurin wani mutum wanda yake da shi. Ana samun irin wannan lakanin ne ta hanyar kyautata wa mai irinsa. Jin dadin abinda ya yi ma wanda ya yi masa wannan abin sakayya ta hanyar sanar da shi tushen maganin wata cuta. Wannan dalilin kan sa wanda aka ba lakanin ya rinka ba ma waɗanda suka fuskanci matsala ta irin wannan rashin lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!