Connect with us

TATTAUNAWA

Addu’ar Al’umma Ta Zama Allurar Kuzari Gareni Wajen Ba Da Maganin Gargajiya – Hassan

Published

on

Tsadar rayuwa da al’ummomin kasar nan ke fuskanta da yawan kudade da Asibitocin gwamnati da masu zaman kansu ke cajin majinyata a garin Jos fadar gwamnatin jihar Filato, ya tilasta wa magidanta da yawa komawa yin amfani da magungunan gargajiya wajen jnyar cututtukan da ke damunsu.

Da yake zantawa da wakilimmu da ke Jos Lawal Umar Tilde, daya daga cikin mutanen da suka je karbar maganin gargajiya don jinyar dan uwansa a daya daga cikin wadannan asibitocin ba da maganin gargajiya din wanda kuma ya nemi da a sakaya sunansa, ya zargi shugabanni ‘yan siyasan da talakokin kasar nan suka jumiri zafin rana da ruwan sama suka tsaya suka zabe su da fatan za su gudanar da ayukan da za su inganta rayuwarsu, amma suka zo suka yi biris da rayuwarsu. Ya ce yanzu  jinya ya fi karfin talaka a Asibitin gwamnati da na kudi ba tare da mutum ya tanadi akalla Naira dubu dari ba kafin ya y i tunanin zai je ko zai kai nasa.

Ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da da ‘yan siyasar kasar nan da al’umma suk zabe su da su yi wani abu don saukaka ke wahalhalu da kuncin rayuwa da talakan kasar nan suke fuskanta.

A sakamakon hakan, shi ma a tattaunawar da ya yi da wakilimmu daya daga cikin masu bada maganin gargajiya, Malam Hassan ya bayyana yadda yake gudanar da ayyukansa, da yake ya sami karin mutanen da suke zuwa gunsa su karbi magunguna, ga dai yadda hirar ta gudana.

Kasancewar yadda mutane suka amince da irin magungunan da kake basu ya sa na nemi saduwa da kai, sai dai da farko zan so ka bayyana wa masu karatu sunanka…

Sunana Malam Hassan mai bada maganin gargajiya, cikin garin Jos, shekaruna Hamsin da biyu.

Tunda kafara wannan sa’a, ta ba da magani yau shekara nawa  kuma ban sani ba ko kagaji wannan sana’a?

Na fara wannan sana’a, na bada magani wa mutanen da suke da lalurori na rashin lafiya tun a Alib 1983, kusan zan ce na gaji wannan sana’a, domin mahaifina makeri ne kuma yakan dan taimakawa mutane da wadansu magunguna idan basu da lafiya, daga nan na fara koyon taimakawa jama’a da magani idan wata damuwa ta rashin lafiya ta samesu kuma Alhamdulillahi yanzu mutane suna zuwa wajena daga kowane bangare na kasar nan su karbi magani a wurina. Kai yanzu haka ana lodin magunguna a cikin buhuna ana kai wadansu garuruwa don taimakawa marasa lafiya da suke da lalurori daban-daban, kowa na bashi magani za ka ji ya dawo yana godewa yana ce mini Malam Allah ya saka da alkhairi, irin wadannan addu’o’i, da ake mini da iyayena yake kara karfafa mini guiwa domin duk lokacin da na ji an yi wa iya’yena addau’a, nakan ji kamar an yi mini allura ne na kara kuzari.

Ko za ka fada wa masu karatu irin cututtukan da ka fi ba da magani a kai?

Nakan bada magani ne bisa irin ciwon da mutum ya zo da ita wanda kuma na ga ba zan iya ba nakan gaya wa mutum yaje wani gu.

Kasancewar yanzu jinya a Asibitocin Gwamnati da masu zaman kansu ya yi matukar tsada ko za ka iya bayyana abin da mara lafiya zai tanada kafin a bashi magani a nan?

Gaskiya ni ban kayyade kudin jinya ba a nan domin wannan aiki nawa aiki ne na jin kai, nafi son Allah ya bani sakamakon wannan aiki gobe kiyama idan ka kuntata wa mai jinya me ye ribanka? Nakan ce masu su bayar da duk abin da za su iya bayarwa domin ina da iyali nakan ciyar da su kuma ga ma’aikatana nakan biyasu kuma wadansu daidaikun mutane sukan zo na taimakamasu da abin da za su biya wadansu bukatunsu.

Ko kana da adadin mutanen da ka kayyade a ko wane yini domin ba su magani don kar a yi maka tururuwa mai yawa?

Alhamdulillahi ni ba zan iya gaya maka ko mutane nawa ne suke zuwa nan a wuni su karbi magani a wajena ba, domin ban da jerin mutanen da suke gani na kafin in basu magani akwai wadanda suke tsayawa a waje su karbi magani a wajen yarana, Allah ne kawai ya san ada’dinsu, ba mu kayyade ba.

To me za ka ce wa irin mutanen nan da suke cewa idan mutum bashi da lafiya bai kamata ya zo wajenku neman maganin ciwon da yake damunsa ba?

To ai ni lafahari nake yi tun da Likitoci daga jihohi daban-daban na kasar nan sukan zo wajena su karbi magani kuma sukan bugo mini waya idan sun kasa warkar da wani ciwo su kan gaya mini irin ciwon kuma su ce in taimaka masu da maganin kuma in aika a kai masu su ba maras lafiya ya sha ya warke. Ina da likitoci daga wadansu manyan Asibitoci kamar Asibiti koyarwa na jihar Filato (JUTH), da wadanda suke a wadansu jihohin arewacin kasar nan da abokantaka ya hada ni dasu a dalilin wannan aiki, domin idan mutum zai yi, ya yi domin Allah kar ya ce zai dubi duniya ko abin da zai samu.

Wane irin taimako kake bukata daga wajen gwamnati?

Ina bukatar gwamnati ta sanya masu bada maganin gargajeya a cikin tsarinta na kiwon lafiya da taimaka masu ta hanyar ba su tallafi wata-wata don karfafa masu guiwar gudanar da ayyukansu na taimakawa jama’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: